Kungiyar masu sana’ar burodi ta kasa (PBAN), sun kammala Shirye-shiryen tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki hudu daga ranar Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022.
Kungiyar ta dauki matakin ne domin nuna takaicinta kan yadda farashin kayayyakin burodi a kasar ke tashin gwaron zabo, inda tace gidajen burodin ba za su iya cigaba da sana’ar ba.
Gas da man fetur da sauran kayayyakin sarrafa fulawar ya hauhawar da farashin Burodi zuwa Kashi 17.71 cikin 100 a watan Mayu.
Shugaban kungiyar, Emmanuel Onuorah da jami’in hulda da jama’a na masana’antar, Babalola Thomas, sun kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta daina karbar harajin 15 cikin 100 na alkamar da ake shigowa da ita Kasar nan.
Bugu da kari, sun bukaci hukumar ta NAFDAC da ta sake rage kudin hukuncin wanda aka kama bai sabunta shaidar kamfaninsa ba daga N154,000.
PBAN ta kuma yi kira ga gwamnati da ta bai wa ‘yan kungiyar damar samun tallafi da lamuni mai sauki da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke ba wa masana’antu Kanana da matsakaita (MSMEs).