Gwamnatin tarayya ta horas da masu kiwon kajin gidan gona da kuma masu noman Rogo, kimanin su 700 a fannin aikin noma daban-daban a Jihar Edo.
A karkashin horaswar, masu kiwon kajin gidan gona 200 da kuma masu Rogo 500 ne suka amfana da horon.
- Ministocin Da Ake Hasashen Za Su Tsallake Hisabin Tinubu
- Rodri Ba Zai Sake Buga Kwallo A Wannan Kakar Ba Sakamakon Rauni
Jami’i a ma’aikatar aikin noma ta tarayya da ke jihar, Samuel Owoicho; a jawabinsa a wajen bayar da horon ya sanar da cewa, an taimakawa wadanda suka amfana da horon ne, domin inganta sana’arsu da kuma kara karfafa tattalin arzikin jihar.
Horon, wanda aka gudanar da shi a garin Benin; babban birnin jihar, Owoicho ya sanar da cewa; horon ya nuna irin ci gaban da aka samar a jihar da kuma kasa baki-daya.
Haka zalika, ya bukaci a ci gaba da yin aiki kafada da kafada; domin tabbatar da dorewar fannin akin noman a wannan kasa baki-daya, musamman domin tabbatar da ganin cewa Jihar Edo ta ci gaba da kasancewa kan gaba a wannan fanni na aikin noma.
Owoicho ya kara da cewa, shirin bayar da horon; ya yi daidai da manufar ma’aikatar aikin noma ta tarayya na bunkasa fannin aikin noman tare da samar da wadataccen abinci da kuma inganta rayuwar kanannan manoma.
Jami’in ya ci gaba da cewa, shirin ya kuma nuna irin kokarin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Ministan Ma’aikatar Akin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari ke ci gaba da yi na bunkasa fannin da samar da wadataccen abinci a daukacin fadin kasar.
Haka zalika, ya kuma bayyana cewa; shirin zai kara samar da ilimi da kwarewa da kuma samar da karin kudaden shiga ga wadanda suka amfana da horon.
A cewar tasa, an samar da shirin tare da yin hadaka da sashen da ke kula da ayyukan malaman gona na ma’aikatar da kuma kamfanin ‘SANCT’ da ke cikin kasar.
Owoicho ya ce, babu shakka hadakar za ta taimaka wajen habaka fannin aikin noma tare da karfafafa fannin, musamman domin samar da wadataccen abinci da rage talauci da kuma kara habaka tattalin arzikin kasa baki-daya.
Haka zalika, ya kuma bukaci wadanda suka amfana da horon da su rungumi yin aiki ta hanyar yin noma da dabarun aikin noma na zamani da kuma yin aiki da ilimin zamani.
Sannan, ya kuma kwadaitar da su cewa, su ilimantar da sauran manoman da ba su samu damar amfana da wannan horo ba, su kuma shiga cikin kungiyoyin manoma domin samun tallafin aikin noma daga wurin gwamnati.
Shi kuwa a nasa jawabin a wajen bayar da horon, babban sakatare a ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci ta Jihar Edo, Peter Osagie; yaba wa gwamnatin ya yi kan horas da wadanda suka amfana da shirin.
Osagie ya kuma yi nuni da cewa, horon zai taimaka wajen ci gaba da habaka fannin aikin noma na jihar da kuma a kasa baki- daya, inda ya kara da cewa; wannan horon zai bai wa jihar karin damar zuba jari a fannin aikin noma na jihar.
Kazalika, ya bayar da tabbacin cewa; ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci ta jihar, ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen taimaka wa manoman jihar.