• English
  • Business News
Sunday, October 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masu Sarrafa Rogo Da Kwakwar Manja A Binuwe Na Fuskantar Tasku

by Abubakar Abba
3 years ago
in Noma Da Kiwo
0
Masu Sarrafa Rogo Da Kwakwar Manja A Binuwe Na Fuskantar Tasku
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mata masu sarrafa rogo da Kwakwar Manja zuwa sauran nau’ukan abinci a jihar Binuwe sun koka kan yadda suke sha bakar walaha wajen sarrafa amfanin ta hanyar yin amfani da Gawayi da Itace, inda suka ce, hakan ke sanyawa hayaki ya cika masu idanuwan.

Daya daga cikin su wata uwargida  mai suna  Onyeka Audu ta sanar da cewa, ba ta yin wata sana’ar wadda ta wuce ta sarrafa garin rogo da kwakwar manja zuwa sauran nau’ukan abinci, ida ta ce, ba mu da karfin da za mu yi amfani da wutar lantarki ko kuma kayan aiki na zamani don yin aikin a cikin sauki.

  • Peng Liyuan Ta Ziyarci Dakin Adana Kayan Tarihi Na Fasaha Na Birnin Ayutthaya Na Thailand
  • 2023: INEC Ta Nemi Masu Kada Kuri’a Da Su Duba Sunayensu Cikin Wadanda Ta Yi Wa Rajista

Ba wai Onyeka ba, haka sauran mata da ke yin wamnan sana’ar, suma suna fuskantar wannan kalubalen, musamman a karamar hukumar Okpokwu wadanda keda alummar da suma kai yawan 237,000

Suk da cewa, Nijeriya ta shiga cikin sahun tsarin muradin karni, musamman domin yin amfani da makamashi nan da shekarar 2030nan.

Bankin duniya a cikin watan Afirilun shekarar 2021 ya an dora kasar a kan sikilen kasashen da ke da alumma mai yawa, amma sai dai, abin takaici, kasar ta kasance ta na fama da raahin wadacacciyar wutar lantarki.

Labarai Masu Nasaba

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

Har ila yau, hukumar samar da wutar lantarki a karkara REA ta kiyasata cewa, akalla a cikin yawan alummar kasar nan miliyan 200 a cikin wannan adadin da   miliyan 100 ne ke samun wutar lantarki, inda hakan ke kara ta’azzarar haifar da yunwa a kasar.

A wani rahoton da hukumar ta fitar a shekarar 2017 tya sanar da cerwa, kashi  36 a cikin dari na alummar da ke zaune a cikin karkara a kasar nan ke samun wutar lantark, inda kuma kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 95 ke samun wutar ta lanrakin.

A wani rahoton  bincike da aka wallafa na NDHS a shekarar 2018 wanda kuma hukumar kidaya ta kasa ta aminta da shi, an bayana cewa, akasarin wadanda ba su da wutar ta lantarki, na zaune a cikin karkara.

Misali, al’umomin a  jihar Biniwe garin Ugbokolo an sada shi da babban layin wutar lantarki na kasa.

Har ila yau, a bisa wani bincike da aka gudanar, an gano cewa, mata da yara da ke taya iyayn su aikin na sarrafa Rogon da kuma Kwakawar ta Manja, sune suka fi shan wahala saboda hayakin da ake sarrafa wadanan amfanin biyu.

A bisa wani bincike da aka yi a yankunan Ihem, Okonobo, Odessassa, Mabe, Aikpla, Effoyo da kuma a karamar hukumar  Okpoga in Okpokwu L da ke a cikin jihar ta Binuwe, mata da maza sun fi yin sana’ar ta sarrafa Rogon da Kwakwar Manjan zuwa sauran nau’ukan abinci.

Wata mazauniya a yankin Ihem Kate Onche ta sanar da cewa, tana yin amfani da itace ne domin sarrafa rogon da kwakwar manjan, inda ta ce, tana sarrafa buhun garin mai cin kilo 50.

Ita ma wata mai sarrafa kwakwar manja a yankin  Aikpla Mary Adoga ta sanar da cewa, rashin wutar ta lantarkin, na janyo masu cikas, inda ta sanar da cewa, sai sun tara itace da yawa ne suke iya gudanar da aikin

Mary Adoga ta kara da cewa, idanuwan sun a yi masu zafi saboda hakin na itacen haka sukan fuskanci ciwon kai mora da saurans.u

A cewar Mary Adoga, “rashin wutar ta lantarkin, na janyo masu cikas, inda ta sanar da cewa, sai sun tara itace da yawa ne suke iya gudanar da aikin”.

Hakazalika, ita ma wata mai suna Paul Olomu ta bayyana cewa, idanuwanta sukan yi ciwo saboda hayakin na itacen da suka yin aikin sarrafa Garin ko kuma Kwakwar manjan

Bincike ya nuna cewa, masu aikin ‘yan kadan ne daga cikin su ke yin amfani da man Dizil don gudanar da aikin na sarrafa Rogon da kuma Kwakwar manjan, inda akasarin mata da suke yin wannan sana’ar, suka dogara kachokam a kan yin amfani da itace

A bisa wani bincike a watan Yulin shekarar 2022 da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta gudanar WHO a akan shakar gurbatacciyar iska ta bayyana cewa, kashi 32 a cikin dari na mutane na kamuwa da cututtuka, inda kuma mutane kashi 12 a cikin dari ke mutuwa saboda shakar gurbatacciyar iskar.

A cewar binciken, kashi 12 daga cikin dari na mutane na mutuawa ne saboda hayakin itace da na kalamzir da sauransu.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: KalubaleNomaRogo
ShareTweetSendShare
Previous Post

Tinubu Ya Amince Da Sa’adu Gulma A Matsayin Shugaban ‘Yan Arewa Na APC A Legas

Next Post

Yadda Mutuwar Abokai Biyu Ta Fallasa Lalacewar Asibitocin Jihar Neja

Related

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

2 days ago
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

2 days ago
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

1 week ago
Dalilin Gwamnatin Tarayya Da Hukumar FAO Na Zuba Dala Biliyan 3.14 A Fannin Noma
Noma Da Kiwo

Dalilin Gwamnatin Tarayya Da Hukumar FAO Na Zuba Dala Biliyan 3.14 A Fannin Noma

1 week ago
Gwamnatin Kogi Ta Yi Haɗin Gwuiwa Don Fara Fitar Da Amfanin Gona
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Kogi Ta Yi Haɗin Gwuiwa Don Fara Fitar Da Amfanin Gona

1 week ago
Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan 10.5 Sakamakon Rashin Cin Gajiyar Kashin Dabbobi
Noma Da Kiwo

Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan 10.5 Sakamakon Rashin Cin Gajiyar Kashin Dabbobi

2 weeks ago
Next Post
Yadda Mutuwar Abokai Biyu Ta Fallasa Lalacewar Asibitocin Jihar Neja

Yadda Mutuwar Abokai Biyu Ta Fallasa Lalacewar Asibitocin Jihar Neja

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun

October 5, 2025
Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku

Atiku Ya Zargi Tinubu Da Fifita Ziyarar Siyasa A Maimaikon Ta Waɗanda Rashin Tsaro Ya Shafa 

October 5, 2025
Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya 

Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya 

October 5, 2025
Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

October 5, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

Rundunar ‘Yansanda Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Haɗa-baki Kan Sace Mai Anguwa A Kano

October 5, 2025
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

Al’ummar Sokoto Sun Koka Kan Yadda Hare-haren Lakurawa Ke Kara Ta’azzara

October 5, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

October 4, 2025
Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

October 4, 2025
Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

October 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.