Daruruwan masu Zanga-zangar ganin an kawo karshen ‘yan sandan musamman na SARS sun yi dafifi a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, tun da misali karfe 1 na ranar yau masu zanga-zangar suka tare hanyar, inda suka haifar da muguwar conkuson ababen hawa.
Masu zanga-zangar sun sha alwashin ba zasu tashi a kan hanyar ba, don haka ma sun kunna wakoki ne kawai abun a manya lasifiku da suke ajiye a gefe da tsakiyar hanya. Wata kungiyar jin kai ta al’umma da ke Legas mai suna Gidauniyar Kokun ta baiwa masu zanga-zangar abinci.