• English
  • Business News
Sunday, October 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mata Ke Shugabantar Kashi 36 Na Bankunan Nijeriya

by Bello Hamza
2 years ago
in Tattalin Arziki
0
Bankunan Nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A shekarun baya, maza ne suka mamaye harkokin shugabancin bankunan Nijeriya amma a sannu a hankali a ‘yan shekarun nan mata na ci gaba da samun tagomashin zama shugabannin manyan bankuna a Nijeriya.

A halin yanzu akwai manyan bankuna 25 kuma yawan mata da ke shugabantar bankuna yana kara karuwa, a shekarar 2019 mace 1 ce ke shugabantar wani babban banki a Nijeriya amma a shekarar 2024 mata masu shugabantar bankuna sun kai 10 wanda ke nuna sun kai kashi 36 ke nan na yawan mata masu shugabantar bankuna a Nijeriya.

  • Goman Ƙarshe Na Watan Ramadan [Darajarsu Da Mutsayinsu] Na 2
  • CBN Ya Kara Adadin Kudin Ruwa Zuwa Kashi 24.75

Bayani ya nuna cewa, duk da wannan ci gaban da mata suka samu a bangaren harkokin banki suna ci gaba da fuskantar kalubale masu yawa. A kan haka ya kamata a taimaka wajen kara buda musu don su samu cika burinsu a bangaren harkar banki a kasar nan. Ga shugabanin banki mata da ke jagorantar manyan bankunan kasar nan a wannnan lokacin.

1. Miriam Olusanya, Shugabar Guaranty Trust Bank (GTBank)
Miriam Olusanya ta kafa tarihin zama mace ta farko na zama shugabar Guaranty Trust Bank, ta dare wannan mukamin ne a watan Yuni na shekarar 2021. Ta yi digirinta na farko ne a bangaren hahada magunguna (Pharmacy) daga Jami’ar Ibadan, daga nan ta yi digirinta na biyu a bangaren harkokin kasuwanci daga Jami’ar Liberpool ta kasar Birtaniya. Ta fara aiki a GTB ne a shekararJ 1998 inda ta ci gaba da samun karin girma har zuwa mastayin shugabar banking gaba daya.

2 Yemisi Edun, Shugabar First City Monument Bank (FCMB)
An nada Yemisi Edun shugabancin bankin ne a watan Yuli na shekarar 2021. Ta yi karatun ta gaba daya ne a kan bangaren harkokin banki ta kuma dade tana aiki a bangaren.
Edun ta jagoranci bankin zuwa matsayin bunkasar da ba a taba gani ba, har bankin ya zama cikin manya-manyan bankunan da ake ji dasu a Nijeriya. A tsarin jagorancinta ta fi bayar da muhimmanci a kan gamsar da abokan hulda, wannan ya sa bankin ya samu karin masu hulda, abin kuma da ya kara wa bankin riba mai yawa. Bayani ya nuna cewa, ana matukar mutuntata a cikin gammayar kungiyoyin bankuna na kasar nan.

Labarai Masu Nasaba

Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama

Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

3 Halima Buba, Shugabar SunTrust Bank
Halima Buba, kwararriyar ma’aikaciyar banki, ta zama shugabar Sun Trust Bank ne a watan Janairu na shekarar 2012, bayan ta shafe akalla shekara 22 tana aiki a bangaren bankunan Nijeriya, cikin bankuna da ta yi aiki a ciki sun hada da All States Trust Bank, Zenith Bank, Inland Bank Plc, Oceanic Bank Plc, da kuma Ecobank Nigeria Limited, tana kuma cikin daidaikun matan da suka samu irin wannan nasarar a kasar nan.

4 Ireti Samuel-Ogbu, Shugabar Citibank Nigeria
An nada Ireti Samuel-Ogbu shugabancin bankin ne a watan Satumba na shekarar 2020. Wannan ne karo na farko da bankin ya nada mace a matsayin shugaba, tun da aka kafa bankin shekara 36 da suka wuce.
Kafin ta zama shugabar bankin ta rike mukamin shugaba mai kula da yankin Turai, Gabas ta tsakiya da Afrika a ofishinsu da ke Landan.

5 Mrs. Nneka Onyeali-Ikpe, Shugabar Fidelity Bank
Mrs Onyeali-Ikpe ta kama aiki a matsayin shugabar banki ne a ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2021
Ta kuma kasance a kan gaba a jagororin da suka bayar da gudummawar bunkasa bankin a cikin shekara 6 da suka wuce. Tun da farko ta taba rike babbar darakta mai kula da yankin kudu maso yammacin Nijeriya da ke da hedikwata a Legas, ta kuma jagoranci bunkasa bankin har ta kai wannan matsayin.
A cikin shekaru 30 da ta yi tana aikin banki, ta samu nasarar zama shugabar bankin ta yi aiki a bankuna da dama da suka hada da Standard Chartered Bank Plc, Zenith Bank Plc, da kuma Citizens International Bank Limited.

6 Tomi Somefun, Shugabar Unity Bank
Tomi Somefun ta zama shugabar Unity Bank ne a watan Agusta na shekarar 2015.
Ta yi karatu a wurare da dama ciki har da Jami’a Obafemi Awolowo, Ile-Ife a Jihar Osun da Jami’ar Harbard Business School da kuma Jami’ar Columbia da ke Amurka.
Somefun ta fara aikin banki ne a kamfanin Peat Marwick and Co. daga na ta koma Arthur Andersen (KPMG) kafin aka nada ta shugabancin Unity Bank Plc.

7 Kafilat Araoye, Shugabar Lotus Bank
An nada Kafilat Araoye shugabancin Lotus bank ne tun a watan Mayu na shekarar 2021.
Ta karantar tarihi a Jami’ar Obafemi Awolowo ta garin Ile-Ife a shekarar (1985), ta yi digirinta na biyu a Jami’ar Legas a shekarar 1987 ta kuma yi karatu don kwarewa a harkokin bankin musulunci a wata makaranta da ke kasar Bahrain.
Ta kuma samu nasarar halartar kwasa-kwasai don kara kwarewa a ciki da wajen kasar nan.

8 Bukola Smith, Shugabar FSDH Merchant Bank
Bukola Smith ta yi karatu a bangaren harkokin sarrafa kudi a Jami’ar Manchester da ke Birtaniya.
Ta zama shugabar bankin ne a watan Afrilu na shekarar 2021. Bankin ya samu ci gaba mai muhimmanci a karkashin jagorancinta.

9 Yetunde Bolanle Oni, Shugabar Union Bank
A cikin watan Janairu na wannan shekarar aka nada Yetunde Bolanle Oni shugabancin Union Bank, ta samu horo a ciki da wajen kasar nan ciki har da Jami’ar Odford da ke Birtaniya. Tun da ta zama shugabar bankin an samu gaggarumin ci gaba ta kuma dora bankin a kan alkibla mai muhimmanci.

10 Dr. Adaora Umeoji, Shugabar Zenith Bank
Nadin Dr. Adaora Umeoji matsayin shugabar bankin Zenith zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Yuni na shekarar 2024, za ta kasane mace ta farko da za ta dana wannan mukamin.

Kafin nadata ta rike mukamin mataimakiyar shugabar bankin tun daga watan Oktoba na shekarar 2016. A shekaru 30 da ta yi a bangaren harkokin bankuna shekara 26 daga ciki ta yi sune a bankin Zenith.

Masu sharhin sun bayyana cewa, samun mata a shugabancin bankuna a kasar nan wata lama ce ta jajircewar mata da kuma rikon gaskiyarsu haka kuma wannan yana nuna irin gudummawar da suke bayarwa a bangaren bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Goman Ƙarshe Na Watan Ramadan [Darajarsu Da Mutsayinsu] Na 2

Next Post

Tsohon Shugaban NLC, Ali Ciroma, Ya Rasu

Related

Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama
Tattalin Arziki

Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama

2 days ago
Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho
Tattalin Arziki

Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

2 days ago
Majalisar Wakilai Za Ta Sasanta Dangote Da NUPENG
Tattalin Arziki

Majalisar Wakilai Za Ta Sasanta Dangote Da NUPENG

1 week ago
Yadda Sauye-Sauyen Da Aka Yi A Fannin Mai Da Iskar Gas Suka Samar Da Gagarumin Ci Gaba A Wannan Shekarar
Tattalin Arziki

Yadda Sauye-Sauyen Da Aka Yi A Fannin Mai Da Iskar Gas Suka Samar Da Gagarumin Ci Gaba A Wannan Shekarar

1 week ago
Manyan Motoci 2,000 A Kullum Ke Zirga-zirga A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Jihar Legas —Rahoto
Tattalin Arziki

Manyan Motoci 2,000 A Kullum Ke Zirga-zirga A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Jihar Legas —Rahoto

1 week ago
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina
Tattalin Arziki

NPA Ta Fara Aiki Da Sabon Tsarin ETO A Tashar Apapa

3 weeks ago
Next Post
NLC

Tsohon Shugaban NLC, Ali Ciroma, Ya Rasu

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun

October 5, 2025
Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku

Atiku Ya Zargi Tinubu Da Fifita Ziyarar Siyasa A Maimaikon Ta Waɗanda Rashin Tsaro Ya Shafa 

October 5, 2025
Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya 

Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya 

October 5, 2025
Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?

October 5, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

Rundunar ‘Yansanda Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Haɗa-baki Kan Sace Mai Anguwa A Kano

October 5, 2025
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

Al’ummar Sokoto Sun Koka Kan Yadda Hare-haren Lakurawa Ke Kara Ta’azzara

October 5, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

October 4, 2025
Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

October 4, 2025
Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

October 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.