Mata Za Su Yi Wa Kwankwaso Tarba Duk Ranar Da Zai Zo

Hana tsohon Gwamnan jahar Kano jagoran kwankwasiyya Sanatan kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnatin Ganduje tayi zuwa ziyara Kano ya kara masa tasiri ne da karin karbuwa a kasarnan. Hajiya Zainab Audu Bako tk bayyana hakan.

Tsohuwar Kwamishiniyar al’amuran matan ta Kano, kuma daya daga cikin shugabannin mata ’yan kwankwasiyya ta ce mata sun shirya su tarbeshi a wannan rana, duba da irin kyautatawa da ya yiwa cigaban mata ta koya musu sana’oi da basu jari tareda basu ilimi kyauta da tura su makarantu dan samun ilimi a sassa daban-daban na ciki da wajen kasar nan, amma sai Gwamnatin Kano ta tauye masa hakkinsa dan kasa dan kano, kuma tsohon Gwamna, tsohon mai bada shawara ga shugaban kasa aka hanashi zuwa.

Ta ce Kwankwaso mutumne da yake da kishin al’umma mai jin maganar manya, dan haka nema da yaga irin mugun tanadinda akayi na baiwa matasa kayan maye da makamai dan su tana hankali, saboda kishin kar’a zubarda jinin mutun daya a kano da kuma kira da fadar shugaban kasa da sauran manya masu ruwa da tsaki a cikin al’umma da sukayi masa ya janye zuwansa zuwa wani lokaci.

Hajiya Zainab Audu Bako tayi nuni da cewa wannan dage ziyarar da mutane suka yi shirin zuwa tarba daga wurare daban daban na jahar nan, musamman mata da matasa dama wadanda bama ba yan jam’iyyarsu bane, sunci alwashin sake dawowa fiye da baya dan tarbar super sanata kwankwaso.

Hajiya Zainab ta ce wani abin takaici shine abinda Kwankwaso ya kawar na daba da shaye-shaye, amma yanzu an dawo dashi ana baiwa matasa makamai da kayan maye an hanasu sana’a da neman ilimi, wanda hakan ba karamar illa bace ga koma baya ga cigaban jahar Kano.

Ta ce Sanata Kwankwaso har yanzu yana kulada gina matasa ta tallafawa ci gabansu a fannoni da dama, ta basu jari da sauran abubuwa da zaisa su zama masu sanin kimar kansu da anfanawa al’umma.

Hajiya Zainab Audu Bako tayi kia ga iyaye maza da mata su kiyaye tarbiyar ya’yansu karsu yarda a yi anfani dasu ta basu makamai da kayan maye wajen bangar siyasa su dage wajen ganin sun nemi ilimi da dogaro da kai.

 

Exit mobile version