Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya ce gwamnonin jam’iyyar APC sun gamsu da zabar Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar.
A ranar Lahadin da ta gabata ne Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya bayyana Shettima, tsohon gwamnan Borno, a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 mai zuwa.
- Na Matsu Mulkina Ya Kare Na Sauka – Buhari
- Bayan Biyan Kudin Fansa: ‘Yan Bindiga Sun Sako ‘Yar Fasto A Adamawa
Da yake magana a ranar Litinin bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, a jihar Katsina, Bagudu ya ce tikitin Tinubu-Shettima shi ne “mafi kyawun hadi” na takarar shugaban kasa.
Bagudu ya ce “Kashim Shettima na daya daga cikin mafi kyawun ‘yan Nijeriya kuma mun yi imanin cewa zai kawo kima mai yawa ga takarar shugaban kasa.”
Ta tabbata ke nan Musulmi biyu ne za su yi takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya a zaben 2023.
Tuni dai wasu suka shiga yabawa zabin na Tinubu wasu kuma suka shiga bayyana akasin hakan.