Matakan Da Ake Bi Wajen Fara Noman Attarugu

Attarugu

Daga Abubakar Abba,

Noman Attarugu na daya daga cikin fannin da ke samarwa da manoman da ke yinsa kudi. Ana amfani da shi a dukkan fadin duniya a cikin abinci.

Ya zuwa yanzu, Nijeriya ce ke kan gaba wajen nomansa a nahiyar Afirka, inda kasar Ghana da China ke  kan gaba wajen nomansa a duniya.

An tabbatar da cewa, nomansa ya fi yin kyau a Arewacin Nijeriya, kuma a yankin ne aka fi noma shi da yawa.

Ana kuma iya nomansa a ko’ina a yankunan Nijeriya, inda an kuma an yi hasashen cewa, Attarugu ya fito ne daga yankin  Amurka ta tsakiya.

Abin da ya sa ya kamata a rungumi nomansa:

Bukatarsa na kara karuwa,musamman ganin yadda ake yawan safararasa daga Arewacin Nijeriya zuwa Kudancin kasar.

Nau’ukan Attarugun  Da Aka Fi Sani:

Akwai nau’ukansa da dama, amma an fi sanin nau’in Atarodo wanda kuma shi ne aka fi sani a Nijeriya.

Sai kuma nau’in da ake kira ‘Sweet Pepper’, shi ne wanda manoma suka fi shukawa a yanzu saboda yana da saukin samar da kudi ga mai nomansa, haka ya fi tsada a kasuwanni.

Akasari ana yin amfani da shi wajen bayar da kala a cikin abincin da aka dafa,musamman kamar a cikin Shinkfa dafa-duka.

Gyaran  Gonar Nomansa:

Bayan an samu gona, sai a gyara ta, a yi mata kamar gado-gado don shuka shi ana kuma son a sanya wa kasar noman maganin feshi sai kuma a zuba takin gargajiya,musamman na Kajin gidan gona,ko na shanu.

Tsiran shuka ya kamata ya kasance mita daya mai tsayo, ana kuma bayar da shawara a yi amfani da ingantaccen Iri mai saurin girma domin an riga an gyara shi, yadda zai yaki duk wata cuta.

Yana daukar watannin kafin ya girma a girbe shi ana kuma son a samar da gurin da za a fara rainonsa idan kuma babu wajen da za a raine shi, ana iya shuka shi a cikin roba ko a cikin Buhun siminti mai budaden baki.

Canza Masa Matsuguni:

Ya danganda da irin girmansa, ana kuma son a samar da sararin da ya kai  inci 12 zuwa 18, inda kuma gadon da za a shuka shi, ya kasance inci 10.

Ana zuba wa komin da aka yafa shi ruwa har zuwa kwanuka biyu ko uku kafin a canza masa matsugunin an fi son a canza masa matsugunin da yamma.

Dole komin da aka yafa shi ya kasance daura da inda aka rene shi don kare Irin da aka yafa daga mutuwa.

Ana canza masa matsuguni zuwa gona daga sati 8  zuwa 10 bayan an yafa shi a gurin reno.

Lokacin Fara Nonansa:

Akasarin Irinsa yana kai wa kimanin kwana bakwai, inda yake kai wa yanayi daga70 zuwa 80, ko da yake, ya danganta da nau’insa da aka yafa.

Yi Masa Ban Ruwa:

Yana bukatar a ba shi ruwa sosai, domin yana da shan ruwa kafin ya nuna kuma ya kamata a yi ban ruwan yadda ya dace.

Yadda Ake Zuba Taki:

Ana son a zuba masa taki mai yawa lokacin da ya fara girma sosai kafin a fara dibansa, inda hakan zai sa ya yi saurin girma ana kuma iya yin amfani da takin NPK.

Cire Ciyawa:

Ana son a cire masa Ciyawa sau biyu kafin a tuge shi, ka da kuma a bar ciyawar a gonar domin tana da cututtuka da kwari don gudaun kar ta harbe shi.

 

Ana sa masa matokarai:

Yana da kyau a sa masa matokarai bayan an shuka shi ya fara girma,ganin cewa nauyinsa na kara karuwa, idan yana kara girma.

Ana samun Riba A Nomansa:

Ana samun riba  mai yawa a fannin nomansa, domin inka shuka daya, zaka samu daruruwansa kuma zaka iya gorbe shi a har zuwa watanni uku, inda kuma Kwandonsa daya,a ana sayar wa sama da naira 5,000.

Lokacin Fara Dibansa:

Ana girbe shi kafin ya gama nuna, domin ko an girbe shi, yana ci gaba da kara nuna.

Barkono mai zafi yana kai kimanin kwanuka 150 kafin ya nuna, ya danganta da nau’in da aka shuka.

Exit mobile version