Shi dai kasuwanci in ji masansa sun ce ”yaki ne” kamar yadda sojoji suke yaki yadda manufarsu ita ce su kori abokan gaba su kama gurare ya zama su ne suke da ikon wurin.
Shi ma dan kasuwa kusan haka yake, amma shi dan kasuwa duk burinsa a yakinsa shi ne ya kama mai saye.
Akwai wata halayya ta ‘yan kasuwa wacce a duk lokacin da za ku yi magana akan yaya kasuwa zai ce maka ”to! mun gode Allah” amma fa shi ya fadi hakan ne don kar kasan me yake samu.
Musamman a yi rashin sa’a rokonsa za ka yi ba zai ta ba nuna maka ai yana cikin jin dadi ba kullum sai dai ya nuna maka ai kasuwa ba labari ana dai yi ne kawai don kar a zauna haka.
Shin dan uwa baka san wannan karyar baya take mai da kai ba?
Ga wata tambaya shin laifi ne ka gaya wa mutum gaskiya cewa yau kasuwa ta yi kyau ko da wannan mutumin rokonka zai yi?
Matakai Shida Ga ‘Yan Kasuwa Don Cin Nasara
Bunkasar tattalin arzikin kasa ya dogara ne kacokan ta tallafa wa kananan sanao’i da kasuwanci a kasa, ta haka ne ya zama dole gwamnati ta taimaka wa kasuwanci musamman ta bangaren samar da bankuna domin samar da jari ga ‘yan kasa don yin kananan sanao’i.
Don bankunan da muke da su a kasar nan a yanzu ba kananan ‘yan kasuwa suke taimakawa ba, suna taimakawa manyan ‘yan kasuwa ne kawai.
Saboda haka dan karamin dan kasuwa wadannan matakai guda bakwai da zan gaya ma in dai ka karanta kuma ka yi aiki da su da shawarwari hakika na baka tabbacin samun ci gaba a lokaci kankani.
Saboda haka ka ga kenan kai zuwa da ‘yan wasu shekaru masu zuwa ka san inda ka sa gaba. Kasashen da ake ganin sun ci gaba ta fannin tattalin arziki sun ci gaba ne saboda yadda gwamnatocinsu suka jajirce wajen taimaka wa ‘yan kasuwa musamman kanana.
Mai karatu wadannan matakai da zan fada maka ba ni ne na kirkirosu ba, a a! nima na samo su ne daga masana kasuwanci da kuma hulda da na yi da ‘yan kasuwa a kasashen da suka ci gaba a hirarrakin da na yi da su na fahimce su.
Da fatan idan an karanta a yi kokarin yin amfani da abin da su.