• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matasa A Guji Bangar Siyasa, ‘Yan Siyasa Ba Za Su Ba Ku Komai Ba Sai Ƙwaya – Matasan Arewa A Kudu

by yahuzajere
3 years ago
Matasa

Kasancewar matasa ƙashin bayan al’umma wanda kuma suka fi fuskantar haɗarin amfani da su wajen cimma muradun miyagun ‘yan siyasa, Gamayyar Matasan Arewa a Kudu da ke Legas, ta yi kira da babbar murya ga ɗaukacin matasan Nijeriya da kar su bari ɓata-garin ‘yan siyasa su riƙa amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa musamman a halin yanzu da aka shiga kakar siyasa.
Gamayyar ta yi kiran ne ta hannun shugabanta, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci a wani ɓangare na yunƙurin da take yi wajen wayar wa da ‘yan ƙasa kai a game da abubuwan da za su kawo musu ci gaba a rayuwarsu.

  • Yadda Ango Ya Yi Shahada Wajen Kare Amaryarsa Daga ‘Yan Bindiga

A cewar gamayyar, “muna sake tunatarwa ga dukkan matasan Nijeriya da su guji yin bangar siyasa domin rayuwarsu tana cikin haɗari, ɓata-garin ‘yan siyasar ƙasarmu ba za su tsinana musu komai ba illa su yi ɗibga musu kayan maye saboda gusar da hankulansu, domin sun san cewa idan matasan suna cikin hayyacinsu ba za su iya saka su miyagun abubuwa ba a ƙoƙarinsu na cimma burinsu na son zuciya.”

Ƙungiyar ta ce irin yadda ake amfani da ƙazaman kuɗaɗe wajen tsayar da ‘yan takara a jam’iyyu manuniya ce kan irin lalacewar da tsarin siyasar ƙasar nan ya yi.

“Kun ga dai yadda ake sayen daliget, wannan shi ne ya nuna wa duniya cewa tsarin zaɓenmu ya gurɓace. ‘Yan siyasar sun mayar da sha’anin takara na ko-a-mutu-ko-a-yi-rai, sannan duk abubuwan da suke faruwa a arewa na kisan jama’a da sace-sacen dukiyoyinsu da cin zarafin iyalai akwai alamun wasu da ke kan mulki a madafun ikon gwamnati suna da hannu a ciki, haka nan wasu masu neman tsayawa takara, shi ya sa wasu ko ana-ha-maza-ha-mata za su ce dole su ci zaɓe domin rufe asirin miyagun ayyukansu.

“Kowa ya san arewa tana da arzikin ma’adanai masu daraja, shi ya sa da ake son sacewa sai aka kitsa mana kashe-kashe da sace-sace, kuma abin takaici ba mu da shugabanni nagari da za hana. Shi ya sa a kullum yankin komawa baya yake yi, muna sake kira ga jami’an tsaro da su guji harka da ‘yan siyasa domin amana ce suka ɗauka ta kare al’umma ba wasu tsirarun miyagun mutane ba kawai kuma za su yi wa Allah bayani saboda tsakani da talakawan arewa na cikin mawuyacin hali.” In ji shugaban gamayyar.

LABARAI MASU NASABA

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

Ƙungiyar ta ce abubuwan da ake yi na rashin kishin ƙasa daga shugabanni ya ƙara sabbaba yunwa, matsalar tsaro da sauran ƙuncin rayuwa, ga kuma abin kunya harkar ilimi ta zama wasa da cin zarafin malaman jami’o’i.

“Yara matasa ‘yan label 400 (ajin ƙarshe) an ɓata musu karatunsu, wasu suna lokacin jarabawa aka rufe jami’o’i, ya kamata shuganinmu nagari su sake jajircewa kuma su ji tsoron Allah su ci gaba da faɗa wa juna gaskiya domin akwai ranar hisabi, abun dubawa a nan a yankin Yarabawa irin waɗannan halayen babu su, haka a yankin Inyamurai, duk inda ka bi mu ‘yan arewa ake kashewa, kuma hakan na ta faruwa tun daga kisan kisan gillar da aka yi wa manyan magabatanmu irin su Sardauna da Tafawa ɓalewa, don haka ya kamata wannan ya zama izina ga duk mai kishin ƙasa.” In ji Galadanci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
Manyan Labarai

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal
Labarai

Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

November 8, 2025
Next Post
Buhari Ya Sake Shillawa Kasar Ghana Don Halartar Taron ECOWAS

Buhari Ya Sake Shillawa Kasar Ghana Don Halartar Taron ECOWAS

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025
Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025
Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

November 8, 2025
Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

November 8, 2025
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Yadda Ake Miyar Margi

Yadda Ake Miyar Margi

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

November 8, 2025
Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

November 8, 2025
Maganin Nankarwa (4)

Maganin Nankarwa (4)

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.