Connect with us

LABARAI

Matasa Ke Da Kaso 85 Na Mahaukatan Nijeriya

Published

on

Dakta Aliyu Abubakar na asibitin jam’iar Ahmadu Bello Zariya, ya bayyana cewa, matasa ne kashi 85 na mahaukatan da ake da su a kasar nan gaba daya.

Dakta Abubakar ya yi wannan tsokacin ne a mukalar da ya gabatar a wani taron da kungiyar ‘Bizara Youth Debelopment Association’ ta karamar hukumar Zariya dake cikin jhar Kaduna. Mukalar mai taken “Drug Abuse in Nigeria: Causes, Effects and Solutions.”

Ya bayyana cewa, “wani bincike da aka gudanar a kwanan nan nan ya nuna cewa, kashi 85 na mahaukatan dake a cikin fadin Nijeriya matasa ne dake da shekaru 18 zuwa 38.

“Babban dalilin haukan da ake fama da shi a wanan lokaci shi ne yawan shaye shaye da matasan ke yi, don kuwa a halin yanzu matasan kan shaki kashin kadangare da sanya hancisu a cikn masai don su shaki tiririn masan sukan kuma sha kara ashana da kuma kashin doki sukan kuma hada kashin kadangare da sauransu don dai su samu su yi maye ko su bugu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: