A kwanan baya ne, Hukumar Kula da Gidajen Gayran Hali ta Kasa ta fitar da wani rahoton da ke nuna cewa, akalla masu zama a gidan Jarun guda 8,246 a daukacin fadin kasar nan ke fuskantar matsalar Ciwon Kwakwalwa.
Mataimakin Kwantirola Janar na Hukumar da ke kula da lafiiyar ayyukan bangaren kiwon lafiya Dakta Glory Essien ne ya bayyana haka, a yayin wani sauraron bayanai kan binciken da ake yi wa Hukumar na zarge-zargen cin hanci da rashawa da yin amfani da karfin iko ba baisa ka’ida ba da ganawa masu zaman gidan kaso azaba da kuma sauran nau’ukan cin zarafi.
A cewarsa, duk da irin daukin kudi da ake samar wa domin magance matsalar, amma lamarin na ciwon kwakwalar a gidan yari na ci gaba da karuwa, hakan na neman ya gagari Kundila.
Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya wato WHO, ta jannyo wasu daga cikin jerin nau’ukan ciwon Kwakwalwa da suka hadda da, jirkewar dabi’ar wadanda suka samu matsalar da shiga cikin yanayin damauwa da kangin talauci da fuskantar tashe-tashen hankula da sauransu.
Koda yake dai, a Nijeriya babu wasu cikakkun alkamun da ake da su, na masu fama da larurar, amma wasu kwararrun a fannin kiwon lafiya a kasar, sun kiyasata cewa, ‘yan Nijeriya akalla miliyan 40 ne, ke fuskantar matsalar.
Wannan ya nuna yadda a halin yanzu irin yanayin da masu zaman a gidajen Yarin ke ci gaba da zama a gidajen, musamman saboda rashin kulawa da su yadda ya kamata.
Sai dai, Dakta Essien ya dora laifin kan rashin samu ‘yanci ga masu zaman gidan Jarun din.
Gidajen Yarin kasar guda 246 yau shekaru 100 ke nan da gina su, wadanda akasarinsu, duk sun tsufa, inda kuma dakunan da ‘yan jarun din ke kwana, ba su da wani sararin da masu zaman jarun din za su iya wani watayawa.
A cewar Essien, jimlar masu zama a gidan jarun ciki har da wadanda aka ajiye da suke jiran Shari’a, sun kai 81,122, wanda a ka’ida kamata ya yi su kai 50,153.
Kazalika, daga cikin wannan adadin, jimlar masu zaman jarun a a daukacin gidajen Yarin da ke kasar nan guda 3,688 a yanzu suke jiran a yanke masu hukuncin kisa.
Wannan yawan na masu zaman jarun din, ya kai kashi 136.7, wanda haka ke nuna karancin kudi na tafiyar da gidajen da kuma rashin kayan aiki.
A kwanan baya mun wallafa wani rahoton a wannan shafin kan irin yadda ake nuna rashin adalaci da tauye wa masu zaman jarun ‘yancinsu.
Muna sane da irin yadda ake fuskantar jinkiri wajen yanke wa wadanda ake zargi hukunci, musamman na yanke hukuncin kisa, inda wadannan matsaloli, suke kara haddasa karuwar cunkso a gidajen yarin kasa.
A ra’ayin wannan Jaridar, wannan jinkirin na yanke hukuncin, da kuma irn yanayin da gidajen Yarin hakan na kara haddasa wa masu zaman jarun din matsalar hauka.
Akasarin su da suke jiran hukunci, tuni, sun fitar da rai daga samun ‘yanci, saboda ci gaba da tsare su, da ake yi.
Dokar kasar ta bai wa duk wani da aka kama da aikata wani laifi, damar daukar Lauya, domin samun beli, amma saoda son rai, da nuna karfi, ba su samun hakan.
Akasarin wadanda ake tsare da su a gidajen Yarin, sun yi ikirarin cewa, sai sun bai wa ‘yansanda cin hanci, sannan suke ke gabatar da su a gaban kuliya ko kuma a wasu lokutan, su sake su.
Damuwar mu, saboda irin lalacewar da gidajen Yarin kasa ke ciki, kusan zai yi matukar wuya, a iya gyarasu, duk da cewa dokar kasar, ta bayar da damar a gyarasu.
Bugu da kari, dokar shekarar 2019 da ta kafa gidan Yarin kasar, ta bayar da damar a mayar da su zuwa na zamani, yadda za su yi daidai da na duniya, wanda kuma dokar, ta jaddda kula da ‘yancin masu zaman jarun
Ra’ayinmu a nan shi ne, akwai matukar bukatar a magance cunkson da ake da shi, a daukacin gidajen Yarin kasar da kuma yadda ake tauye hakkin masu zama a gidajen, wanda ya zama wajbi a dauki matakan magance wadannan matsalolin, ta hanyar samar da sauye-sauye da dabaru, masu dogon zango.
Samar da ingantattun kayan aiki a gidajen zai taimaka wajen rage cunkoson da gidajen ke ci gaba da fuskanta, wanda za a iya samun hakan ne kawai, idan Gwamnatin ta kara yawan kudaden da ake ware wa gidajen domin su tafi daidai da irin na kasashen duniya.
Kazalika, samar da sauye-sauye a bangaren shari’a da kuma kafa kotunan tafi da gidanka na yanke ‘yan kananan laifuka, hakan zai taimaka wajen yanke hukunci a kan lokaci, musamman domin a dakile yawan samun cunkoso a gidajen.
Kare ‘yancin masu zaman gidan na da matukar mahimmanci kuma ya kamata a samar da wasu kungiyoyi masu zaman kansu da za su rinka zuwa gidajen domin sanya a ido kan irin yanayin da gidajen suke ciki da kuma gudanar da bincike, kan batun cin zarafin masu zaman jarun.
Ya kuma kamata a rinka shirya wa ma’aikatan gidajen horo musamman kan yadda za su rinka bin ka’idar kiyaye hakkokin masu zaman gidajen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp