Assalamu Alaikum, Editan Jaridar LEADERSHIP Hausa mai Albarka, da fatan alkairi ga dukkanin ma’aikatanku.
Hakika ya kamata gwamnatin jiharmu ta Jigawa ta dauki matakin gaggawa domin magance matsalar yawan samun kifewar kwale-kwale a sassan jihar duba da yadda wannan matsala take afkuwa a kai a kai a sassan wannan jiha tamu wanda hakan ke jawo asarar rayukan al’umma da dama, domin ya faru a garin Kalgwai ta Karamar Hukumar Auyo da garin Nahuche na Karamar Hukumar Taura da ma wani gari a Karamar Hukumar Buji duk a cikin dan karamin lokaci.
- Fina-finai Masu Dogon Zango Koma Baya Ne Ga Masana’antar Kannywood – Tanimu Akawu
- Amfani Da Kayan Marmarin Da Aka Jima Da Yankawa Na Haifar Da Matsala – Likita
Wannan matsala tana faruwa ce ta dalilin yin amfani da kwale-kwale marasa inganci, rashin yin amfani da rigar taimakon linkaya ma’ana (life jacket) da kuma zarin lodi da ake yi wa wadanan kwale-kwale, don haka ya kamata gwamnati ta dauki matakin magance wannan matsala.
Domin idan har gwamnati ta dauki matakin samar da gadoji, kananan kwale-kwale masu inji masu inganci da ma rigar taimakon linkaya ma’ana (life jacket) a wadanan gurare, hakika za a samu saukin wannan matsala, domin yawanci wadanan tafiye-tafiye da al’ummar wadanan yankuna suke yi a cikin kwale-kwalen suna yi domin zuwa gonakansu ko kuma kasuwanni wanda dukka dole ne sai an yi su domin hanyoyi ne na gudanar da rayuwar yau da kullum ta al’umma.
Akwai fa yankuna da dama da ke fama da irin wannan matsala ko a Karamar Hukumar Miga akwai mahayin kogi da ke yankin mazabar Sansani da ke fama da irin wannan matsala a duk lokacin damina.
Tabbas wannan matsala ta kifewar kwale-kwale matsala ce da ta jima tana faruwa a sassan kananan hukumomi na jiharmu ta Jigawa, duba da yadda wannan matsala take faruwa duk shekara ya kamata gwamnati ta yi dukkanin abin da ya dace domin magance matsalar, tunda babban aikin gwamnati shi ne kare rayukan al’umma da dukiyarsu.
Hakika wadanan yankuna da ake fuskantar wannan matsala ta kifewar kwale-kwale suna da matukar tasiri da muhimmanci a tattalin arzikin jiharmu domin yankuna ne da ake noman rani da damina ga kuma sana’ar kamun kifi ko su da kuma kiwon dabobi, don haka sun cancanci a ba su kulawa domin kare rayukan al’umma da dama habaka tattalin arzikin jiharmu.
Tabbas ya kamata gwamnati ta yi kokarin hada hannu da jami’an tsaro wajen kula da irin wadanan yankuna da ake tafiye-tafiye a cikin ruwa, domin rage lodin jama’a da kaya da ake yi wa wadanan kwale-kwale da ya yi yawa.
Daga karshe nake addu’ar Allah ya yi riko da hannayen Gwamna Malam Umar Namadi Danmodi wajen magance wannan matsala dama gudanar da mulkin jiharmu ta Jigawa don alfarmar Annabin Rahama (S.A.W).