Connect with us

TATTAUNAWA

Matsalar Mulkin Nijeriya: Rashin Amfani Da Harshen Hausa (2)

Published

on

Manyan }kasashen duniya da ake kira ‘Asian Tigers’ da sauran }asashe da suka ci gaba a duniya suna amfani har harshensu na gida ne a kowanne ~angare na cigaba.

Har al’umomi da ke da }ananan harsuna kamar Danish, ko Dutch ko Finish, suna amfani ne da harsunansu na gida. Don babu wata }asa da ta ta~a ci gaba da harshen Turawan mulkin mallaka.

Binciken wani masani mai suna Prah (1993), na nuna }asashen Afirka da suka ci baya har yanzu ba yabo ba fallasa, sun dauwama a wannan }angi ne saboda sun bautar da kansu ta hanyar ci gaba da amfani da harshen Nasara.

Ya }ara da cewa a Afirka harsunan turawa sun zame rigunan ado ga idon gari ko ‘yan boko, shi ya sa sai gi~in ya zama wagege tsakaninsu da talakawansu.

{asashen da suka ci gaba su ne }asashen da suka kula da harshensu, suka rene shi, suka yi masa goyo mai kyau, suka bun}asa shi, ya yi daidai da bu}atunsu na zamantakewa, da tattalin arziki, da siyasa, da }ere-}ere na kimiyya da fasaha. Likitanci da Injiniyanci duk cikin harshensu suke yi, amma mu a Nijeriya muna wa]annan abubuwa ne cikin ba}on harshe na Nasara.

Marigayi Farfesa Bashir Ikara a shekarar 1991, ya yi bayan cewa shugabannin }asashen Afirka sun yi wani taron {ungiyar ha]a kan Afirka (O.A.U.) a Addis Ababa daga ranar 28 zuwa 30 na watan Yulin shekarar 1986, sun cimma matsayar cewa:

  1. a) Babu wata ci gaba da za a samu cikin hanzari in ba ana amfani da harshenmu na Afirka ba.
  2. b) Afirka na bu}atar tin}aho da alfahari da harshenta muddin tana son a martabata a duniya.
  3. c) Har zuwa lokacin babu wata }asar Afirka da ta yun}ura domin ]ora harshenta bisa turbar da ta dace da aikin gona, da zamantakewa da ta tattalin arzikinta.
  4. d) Babu yadda za a yi duk wani gangami ya yi nasara in ba a yi shi cikin harshen Afirka ba.

Kada mu manta a Afirka gaba daya manyan harsuna uku ake da su. Harshen Hausa, da harshen Larabci da harshen Swahili.

Har ila yau Bashir Ikara ya yi bayanin cewa sun halarci tarurruka a }asashen duniya, inda suke ta ganin wakilan }asashen duniya ke tinti~ar juna cikin harshensu su yi ~ad-da-bami, idan sun koma taro, su yi harshen da ake yi a wajen.

Ikara ya ce yana ]aya daga cikin irin wa]annan wakilai zuwa }asar Ethopia. Sarkin Ethopia marigayi Haile Salassie ya iya harshen Ingilishi kamar bature, amma ya yi magana da harshensa na gida wato Amharic. Ministansa na harkokin waje ne ya fassara abinda ya fa]i da harshen Ingilishi. Haka nan marigayi Jomo Kenyatta ya yi nasa jawabin a harshens na gida wato Swahili, shi ma ministansa na kula da harkokin waje ya fassara wa jama’a da ke wajen taron cikin Ingilishi. Sai Farfesa Bashir Ikara da sauran na kusa da shi suka bai wa shugaban }asar Nijeriya Janar Yakubu Gowon shawarar shi ma ya mayar da jawabi da Hausa. Yakubu Gowon ya yarda shi ma ya ranga]a Hausa ana ta kallonsa. Bayan an kammala taron sai shugaba Kenyatta ya shaida wa Bashir Ikara cikin harshen Ingilishi cewa:

“anyone who cannot speak his language is in mental slabery”

Wato duk wanda bai iya magana da harshensa ba, hankalinsa na cikin }angin bauta.

Farfesa Ikara ya ce abin takaici a yau shi ne sarakunanmu da su ne ya kamata su kare harshenmu da sauran al’adunmu, idan suka yi ba}i ‘yan }asashen waje a fadarsu, sai su ta}ar}are suna buga Ingilishi domin nuna wa duniya su sun waye.

Kundin tsarin ilimi na Nijeriya na shekarar 2004, cewa ya yi kowanne yaro a shekarunsa uku na farko na karatunsa na firamare, a fara koya masa karatu da harshensa na gida ba da Ingilishi ba. Akwai wani bincike da Guibi da Hamisu suka gudanar a shekarar 2011 akan ko makarantun firamare da ke jihar Kaduna suna aiki da wancan tsarin ilimin. Binciken na nuna cewa ba a aiki da tsarin. Su kansu iyaye ke cire ‘ya’yansu daga makaranta idan sun ji ana koyar da yara da Hausa ba da Ingilishi ba. Su a wajensu Ingilishi ne ilimi ba Hausa ba.

A ilimance, kyakkyawar turbar iya mulkar mutum cikin jin da]i, ita ce amfani da harshensa na haihuwa, harshen da yake tafiyar da lamuransa na yau da kullum. Daga tashi barci zuwa kwanciya, da tunanisa, da falsafarsa har da mafarkinsa.

Hatta taron da ya gudana na sauraron ra’ayoyin jama’a a ranar 10 ga watan Nuwamba, na shekarar 2012, da ‘Yan Majalisun dokoki na tarayya suka shirya a maza~unsu guda 360, ni marubucin wannan takarda, aka ]auko domin taimaka wa fassara abubuwan da ake so a yi muhauwara akansu, a taron maza~ar Tudun Wadan Kaduna, da ya gudana. Da ke nuna cewa Ingilishin kundin tsarin mulkin Nijeriya, yawancin ‘yan Nijeriya, indai ba lauyoyi ba, gaskiya ba sa fahimtar ina aka dosa.

Ina mafita?

Mafitar kenan, komai ~angaren mulki ya koma Hausa. In har sauran ~angarorin }asarnan ba su yarda ba, to can Gabashin }asarnan, komai ya koma da harshen Igbo, Yammaci komai ya koma da Yarbanci, mu kuma Arewa a koma Hausa. Ba abinda ba za mu iya yi a harsunanmu ba. Likitanci, da Injiniyanci, da lauyanci, da jaridanci duk ba abinda ba za mu iya shi da Hausa ba.

In har aka koma sha’anin mulki cikin harshenmu, ko shakka babu matsalar da ta yi wa }asarnan dabaibayi, za ta kau, ba sai an ~ushe da kiran wani taro na }asa ba.

 

 
Advertisement

labarai