Nijeriya ta sake samun kanta a cikin halin tashin hankali, tsoro da alhini, a yayin da rahotanni suke nuna cewa, ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da daruruwan dalibai ‘yan makaranta a wasu jihohin kasar nan, wannan shi ya dawo da hannun agogo baya a kokarin da gwamnatoci a dukkan matakai suke yi na samar da tsaro a kasar nan.
A kwanakin baya ne ‘yan ta’adda suka sace dalibai 280 da Malaman su daga makarantar LEA da ke garin Kuriga, karamar Hukumar Birnin gwari ta Jihar Kaduna.
- Ɗiawara Ya Fice Daga Tawagar Faransa Bayan An Hana ‘Yan Wasa Yin Azumi
- Sin Za Ta Inganta Zamanintarwa Bisa Bunkasuwa Mai Inganci Don Ba Da Karin Karfi Ga Ci Gaban Duniya
Haka kuma wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari a yankin Buda da ke karamar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna inda suka yi nasarar sace mutum 61.
Duk a ‘yan kwanakin nan, sai gashi kuma ‘yan ta’addar Boko Haram sun yi awon gaba da mata 200 a yankin Gamboru-Ngala da ke karamar hukumar Dikwa ta Jihar Borno.
Rahotannin sun nuna cewa, matan da aka sace na daga cikin ‘yan gudun hijira ne da ayyukan ‘ta’addanci ya raba su da muhallansu a yankin Arewa maso gabas, an kuma sace su ne a yayin da suka shiga daji don neman itacen dafa abinci.
Har ila yau mun samu rahoton kashe mutum 50 ciki har da iyalai 7 a harin da ‘yan ta’addan suka kai yankin Gbagir da ke karamar hukumar Ukum ta Jihar Benuwai.
A daidai lokacin da ‘yan ta’addar ke cin karensu babu babbaka sai kuma gashi sun kai hari a kauyen Gidan Bakuso da ke karamar hukumar Gada can Jihar Sakkwato, inda can ma suka yi awon gaba da almajirai ‘yan makarantar tsangaya 15 wasu kuma da dama ba a samu labara inda suke ba har zuwa yanzu.
A ra’ayin wannan jarida, wadannan ayyuykan ta’addanci ba abin da ya kamata a kawar da kai ba ne; wadannan sun kasance wasu sabbin babi a cikin ayyukan ta’addanci da ya addabi sassan Nijeriya a cikin ‘yan shekarun nan.
Nijeriya ta dade tana dandana kudarta a hannun ‘yan ta’addr da suke harkokinsu ba tare da wani tsoro ba a sassan Nijeriya.
Wadannan ayyukan garkuwa da mutane da suka sake kunnu kai sun matukar tayar da hankulan al’umma, wadanda suka dade suna sauraron alkawurran masu tafi da kasa na cewa, lallai za a samar masu da tsaro amma kuma har yanzu babu ranar tabbatar da cika wannan alkawarin.
A ra’ayinmu, lokaci ya yi da za a sauya salon da ake amfani da shi a yaki da ta’addanci a Nijeriya. Duk da cewa, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaji wasu daga cikin matsalolin tsaron da ake fuskanta, matsalar da take barazana da kokarin jawo masu zuba jari daga cikin Nijeriya da kuma kasashen waje.
A ra’ayinmu, duk irin abubuwan da Shugaba Tinubu ya shirya gabatarwa na ci gaban kasa, batun samar da tsaro shi ya kamata ya zama a kan sahun gaba don da shi ne tattalin arziki zai karu, musamman ma la’akarin yadda ya tafiyar da tsaro da zaman lafiyar al’ummar kasa, musamman ganin yadda ake kashe mutane da tare da kakkautawa ba.
Matsayar shugaban kasa na kin biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda wannan ma abin a yaba ne. Hakan ya yi daidai da yadda ake tafiyar da irin wannan matsalar a sauran sassan duniya, yana kuma aikawa da sako mai karfi ga su ‘yan ta’addar da ‘yan bindiga na cewa, gwamnati a shirye take da ta murkushe su.
Amma kuma dole gwamnati ta fito da tsari na musamman kan yadda za ta karya alkadarin ‘yan ta’addar ba tare da bata lokaci ba.
Tattaunawa da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan bindiga ba zai haifar da da mai ido ba, irin tattaunawar tana kara karfafa kungiyoyin ne kawai da kuma nuna tamkar gwamnati bata da yadda za ta yi.
Muna kara jaddada cewa, bai kamata Nijeriya ta nuna gazawa ba a fafatawarta da ‘yan ta’addar da suka gallaza wa al’umma ba tare da tausaya masu ba. Lokacin da duk wata tattuanawa ta wuce, abin da ake bukata a halin yanzu shi ne fafatawa da gungun masu aikata laifi.
Domin samun wannan nasarar, dole ne Shugaba Tinubu ya karfafa jami’an tsaronmu ta hanyar samar masu da dukkan kayan aiki na zamani daidai da irin wadanda ake amfani da su a kasashe duniya wadanda suka ci gaba.Hakanan kuma a kwai bukatar a karfafa hanyoyin samar da bayanan sirri domin dakile ayyukan ‘yan ta’adda a daidai lokacin da suke shiryawa.
Hakanan kuma ya kamata a yi maganin ainihin  su matsaloli da dalilan da suke taimakawa wajen bunkasar harkokin ta’addanci a Nijeriya wadanda suka hada da talauci, rashin aikin yi ga matasanmu da kuma yadda ake nunawa wasu al’umma wariya a harkokinsu na yau da kullum na kasa.
Ya kamata a samar da ingantaccen tsarin yaki da ta’addanci wanda ya hada da samar da ayyukan bunkasa rayuwar al’umma da suka hada da samar da aikin yi ga matasa, bunkasa bangaren ilimi, kiwon lafiya, da kuma sauraron koke-koken al’umma.