- Majalisa Za Ta Gudanar Da Bincike
- Dukkan Ɓangarori Ne Ke Ɗanɗanawa – MURIC
Mai bai wa Shugaban Kasa Bola Tinubu Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa, Sunday Dare, ya karyata zargin da Sanatan Amurka Ted Cruz, mai gabatar da shirye-shiryen talabijin Bill Maher, da mai sharhi kan harkokin siyasa Ban Jones suka yi cewa ana gudanar da “kisan kiyashi ga Kiristoci” a Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na D (wanda a da ake kira Twitter) a ranar Litinin, mai taken “Karyata Maganar Kisan Kiyashi da Sanata Ted Cruz, Bill Maher, Ban Jones da sauran su suka yada,” Dare ya bayyana wannan zargi a matsayin karya, abin yaudara, kuma mai iya haifar da rarrabuwar kai.
- Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025
- An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar
Ya zargi masu sharhin daga kasashen waje da “kirkirar zarge-zargen ban mamaki game da wani kisan kiyashi da ba a tabbatar da shi ba,” yana kira ga ’yan Nijeriya da al’ummar duniya su yi watsi da wannan yunkuri na “sanya wa kasar riga wadda ba ta dace da ita ba.”
Dare ya jaddada cewa Nijeriya kasa ce mai addinai da dama, wacce aka gina bisa juriya, zaman lafiya, da girmama juna tsakanin mabambantan addinai, al’ummomin da ya ce Tinubu ya shugabanta.
Dare ya ambaci maganar Shugaban Kasa inda ya jaddada cewa Nijeriya “kasa ce mai cikakken ‘yanci da girma, wadda aka gina bisa bangaskiya da juriyar jama’arta,” ya kara da cewa “Babu wani addini da ake zalunta, kuma babu wata al’umma da aka ware.”
Yana nuna misali da rayuwar Shugaban Kasa a matsayin shaida ta juriya da fahimtar addinai, Dare ya bayyana cewa Shugaba Tinubu, Musulmi ne da yake auren fasto mai bin addinin Kirista.
Ya kuma ruwaito Shugaban yana cewa, “Gaba da kiyayya ba su da gurbi a gare mu. Soyayya ce abin da muke wa’azanta, kuma dole mu rika son juna.”
Dare ya bayyana cewa labarin “kisan kiyashi ga Kiristoci” babban rudani ne da ya kau da kai daga ainihin matsalolin tsaro da Nijeriya ke fama da su, inda ya bayyana cewa kasar na yaki da ta’addanci da ‘yan fashi da ke yin barna don samun riba da tayar da hankali, ba saboda addini ba.
Ya ce, “Wadannan ‘yan ta’adda suna kai hari kan fararen hula ba tare da bambance coci-coci, masallatai, kasuwanni, makarantu ko kauyuka ba, suna kashe ’yan Nijeriya masu bin addinai da kabilu daban-daban.”
Ya yi gargadin cewa fassara wannan rikici a matsayin yakin addini yana kara karfafa ’yan ta’adda ne tare da raunana hadin kan kasa.
Ya yi kira ga Cruz, Maher da sauran su da su nemi sahihan bayanai kafin su yada karya da ke bata sunan Nijeriya tare da karfafa ’yan ta’adda.
Dare ya kammala da cewa, “Gaskiya abu daya ce mai sauki , Nijeriya ba ta fuskantar kisan kiyashi ga Kiristoci; tana yaki ne da ta’addanci da ke kai hari ga kowa da kowa. Duk wanda ya yi zargi, to ya gabatar da hujja.”
A wani bangaren kuma majalisar dattawa ta zartar da kudurin tattauna lamarin da zaran sun kama aiki gadan-gadan daga hutun da suka dawo ranar Talata da ta gabata. Wannan na zuwa ne bayan da Sanata Ali Ndume da Sanata Sani Musa da Sanata Aliyu Wamakko da kuma Sanata Ibrahim Bomai suka gabatar da kudurin neman haka ga zauren majalisar ranar Talata.
A cikin kudurin da suka gabatar, sanatocin sun nemi bangarorin gwamnati da suke da ruwa da tsaki a kan lamarin musamman ma’aikatar kasashen waje da hukumomin tsaro su tabbatar da bayar da kididdiga da bayanai da suka kamata don karyata wannan frofaganda na kafafen yada labarai na kasashen waje suke neman bata sunan Nijeriya a idon kasashen duniya.
Sanata Ndume ya nuna damuwarsa na yadda ake yada labaran kanzon kurege a kan halin tsaron da kasar nan ke fuskanta. Yana mai cewa, dukkan bangarorin al’umma ke dandana matsalar rikicin ba wai wasu addinai ko kabilu ba.
Wani mai wasan barkwanci na kasar Amurka ne dai mai suna Bill Maher, ya yi ikirarin cewa, an kashe fiye da Kiristoci 100,000 a kisan kare dandi da ake yi wa Kiristocin Nijeriya.
Haka kuma wasu kugiyoyin musulmai kamar MURIC ta bayyana cewa, ayyukan ‘yan ta’adda a Nijeriya a cikin shekararun ya shafi duk wani dan Nijeriya ta hanyoyi daban daban. Haka kuma an tabbatar da cewa, lamarin ya ci rayukan musulmai fiye da 32,000 a cikin shekara uku. Don haka dukkan bangarorin ‘yan Nijeriya ke dandanawa” ya kuma kamata a hada hannu gaba daya don kawo karshen ayyukkan ‘yan ta’adda” in ji kungiyar.