‘Yan uwa musulmi masu karatu assalamu warahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Har yanzu dai muna nan a kan karatunmu na Hijirah.
Alhamdu lillah, mun ji dai karatu a kan ranar haihuwar Manzon Allah (SAW) da ranar Manzanci da irin muhimmancinsu, amma duk da haka Sahabbai (RA) ba su daidaita tarihin shekara da su ba, sai tarihin Hijra saboda sanin muhimmancin yin hakan.
- Gidauniyar Dangote Da Gwamnatin Kano Za Su Yi Yaki Da Cutar Tamowa
- Ma’aikatan Gwamnati Sun Fi ‘Yan Siyasa Cin Hanci Da Rashawa – Kwamitin Majalisar Dattawa
A yau kuma za mu mayar da hankali ne a kan rana babba, ita ce ranar Yakin badar. Allah yana ce mata ‘ranar rarrabewa’, ranar da aka rabe karya da gaskiya, ranar da Jama’ar Allah suka zama daban, na Shaidan ma suka zama daban, ranar da rundunonin mutane guda biyu suka hadu, rundunar Allah da rundunar Shaidan.
Rundunar Allah shugabansu Annabi Muhammadu (SAW). Rundunar Shaidan shugabansu Abu Jahli.
A wannan rana ce Allah ya halatta kare kai, duk yakokin da Manzon Allah (SAW) ya yi kamar yadda Shehu Ibrahim Inyass (RA) ya fada, ba ya yisu ne don ya tilasta wa kafirai su karbi Musulunci ba.
Manzon Allah (SAW) ya fi so mutum ya karbi Musulunci da kyakkyawar zuciya, da ‘yancinsa, da jin cewa yana son Musuluncin a ransa. Kowa yana da hankali, don haka kowa ya ga abu mai kyau ya sani, haka in ya ga abu mara kyau in dai ba kuma shaidan ya shiga cikin lamarin ba.
Idan ma mutum kokwanto yake a kan abu, ka iya ba shi shawara da kalamai masu dadi, ba zancen fada, ba zancen yaki. Allah Ta’ala ya ce “ba dole a cikin addinin nan”.
Ranar Badar rana ce ta rarrabewa, dama kafirai sun yi ta cutar da Manzon Allah (SAW) ba ya ramawa.
Ranar Badar Mala’iku ma sun yi yaki domin nuna gaskiyar Musulunci kurukuru a gani. Duk wani yaki na rabe gaskiya da karya har duniya ta nade zai zamo daga albarkar Yakin Badar ne, domin da ba a ci nasarar Yakin Badar ba da komai ya kare, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya nunar lokacin da ya ce, “Allah in har ka bari aka halaka wadannan mutanen (Sahabbai) ba za a kara bauta maka a kan kasa ba”.
Kuma Manzon Allah (SAW) ya nuna wa duniya irin alherin da ke cikin Musulunci, illa kawai dai wanda ya so ya yi imani, wanda ya ki kuma shi ya so.
Yakin Badar ba yaki ne na neman mamaya ba, Manzon Allah (SAW) ya toshe shisshigi ne da ‘yantar da Bayin Allah da ake bautar da su da zalunci. Ya nuna wa duniya hukuncehukuncen yaki mafi dacewa da tausayin Dan Adam da kyautata masa.
A ranar Badar Yahudawa sun yi imani tare da tabbatar da cewa lallai wannan Annabi shi ne Annabin Karshe kamar yadda suka karanta a Attaura, duk kuwa da cewa tun kafin yakin sun ga alamomin hakan.
Amma su cewa suke mutum ba zai zama na Allah ba sai in yana samun nasara a kan abokan gaba, wannan kuma daga garesu ne kawai.
Saboda misali, duk idan wani ya ce mutum ba zai zama na Allah ba sai ya zama mai kudi, ko sai ya zama talaka, ko sai ya zama malami, ko sai ya zama jahili to bashi da ma’aunin gane haka. Shi Allah Tabaraka wa Ta’ala ta shi ake gane shi, amma ba ta wani abu ba.
Duk wani abu da za ka gani kyauta ce kawai ta Allah. To, Yahudawa sun yi imani da Annabi (SAW) a ranar Badar, sai dai daga baya suka warware.
Yusufun Nabahani (RA) ya fada a cikin Littafinsa na Anwarul Muhammadiyya cewa tun da aka yi Yakin Badar Allah ya ajiye wasu Mala’iku da dunfufofi suna ta bugawa domin murnar nasarar Badar kuma ba za su bari ba har tashin duniya, duk wanda Allah ya yi masa gamo da katari idan ya je Badar zai ji.
Allah kuma mai iko ne ya shigar da wani Bawansa cikin ‘Yan Badar duk kuwa da cewa bai yi yakin ba.
Idan mutum ya yi wani kokari Allah ya duba sai ya yi masa hakan, bare kuma Khalifan Manzon Allah (SAW) ya ce ma Allah zai tasheka a cikin ‘Yan Badar.
Domin da yawa akwai wadanda ba a yi Yakin Badar da su ba sun tambayi Manzon Allah (SAW) cewa a raba Ganimar Badar da su, Manzon Allah ya amince, wani ma ya tambayi ladan fa, Manzon Allah ya ce har da ladan.
To yanzu dai ganima ta kare, amma mutum zai iya yin wani kokari Allah ya duba ya sa shi a cikin ‘Yan Badar ba dole sai yaki ba.
Misali, idan mutum ya yi wata kasaitacciyar gona ya ciyar da al’ummar Annabi (SAW) Allah zai iya sa shi a ciki, haka in ka yada zaman lafiya a cikin al’ummar Annabi ko yada sanin Allah, duk dai Allah mai iko ne ya shigar da mutum cikinsu.
Sahabban da suka yi Yakin Badar suna da wata falala ta musamman ta yadda idan aka yi wani taro ana ba da labarin wadanda suka halarta akan ce Sahabban Manzon Allah sun je wurin har da ‘Yan Badar.
Haka nan ko Hadisi ne wani ya ruwaito a cikinsu za ka ji bayan an ambaci kasancewarsa Sahabin Annabi akan kara da fadin falalarsa cewa Dan Badar ne.
Daraja ce babba, ‘Yan Badar Alheri ne. Kuma har ila yau, yana daga falalar Badar a ranar Sahabbai Muhajirai da Ansaru suka hadu a abu guda daya, wato ana kiransu da sunan ‘Yan Badar dukansu. Daga ‘Yan Badar sai ‘Yan Ukhudu, sai ‘Yan Bai’atur Ridwani, sannan ‘Yan Fatahu Makkata kuma dukkansu masu girma ne a wurin Allah.
Masu karatu kun ga dai duk da abubuwan da Ranar Badar ta tara, Sahabbai ba su fara kirgen shekara da ita ba sai a ta Hijirah domin hikima.
Kamar yadda bayani ya gabata, wata rana mai girma da kuma ba a fara kirgen farkon shekarar da ita ba ita ce ranar da Wahayi ya cika.
Shekara 23 da aiko da Manzon Allah (SAW), a sannan kuma shekarar giwa tana da 63. Shekara 634 kuma da haihuwar Annabi Isah (AS).
A wannan lokacin Allah ya cika mana addini a Dutsen Arfa, bayan Manzon Allah (SAW) ya isar da amana, ya yi wa al’umma nasiha, ya gama duk abin da aka aiko shi da shi na kira, ya yi wa mutane bishara da wannan addini, sai Allah ya cika addinin da tun daga Annabi Adamu (AS) Ya faro har zuwa kan Annabi Muhammadu (SAW).
Allah ya cika Islam, Iman da Ihsan. Shekara wajen goma da aka yi a Makka ana ta fama ne da mutanen Makka a kan La’ila ha illallal da kuma kyawawan dabi’u.
Har zuwa lokacin da Manzon Allah ya yi Isra’i da Mi’iraji aka kawo Sallah, daga nan sai Zakkah, sai kuma Azumin Ramadan.
Sallah ce kawai aka saukar a Makkah, amma Zakkah da Azumin Ramadan da Hajji duk bayan Hijira ne aka saukar da su. A shekara ta goma Manzon Allah ya zo Hajji.
A Hajjin bankwana da Manzon Allah ya yi, ya ce wa al’umma ku riki Hajji daga wuirna ba na zaton zan sake kaiwa wani Hajjin.
Bayan ayar da ta yi magana a kan cika addini ta sauka a ranar Arfa, kashegari kuma sai surar Izha ja’a nasrullahi ta sauka. A cikinta ga batun Istigfari da Tasbihi a ciki.
Bayan an dawo gida da ko awa biyu ko kwana biyu (babu dai wata ruwaya da ta ce an yi sati guda) sai ayar Wattaku yauman ta cikin Suratul Bakara ta sauka, ita ce rufe Kur’ani.
Ita kuma a cikinta ga batun Takawa nan (tsoron Allah) a cikinta.
Duk dai komai na Shari’a ya sauka. Lokacin da Mala’ika Jibrilu ya zo ya tambayi Annabi (SAW) mene ne Musulunci, mene ne Imani kuma mene ne Ihsani? Bayan Annabi ya ba shi amsa ya tafi, Manzon Allah ya ce wa Sahabbai Jibrilu ne ya zo don ya sanar da ku addininku. Ina kara jaddadawa cewa “Addini” Manzon Allah ya ce.
Ka ga masu cewa ai addini ya cika don haka ina aka samo Darikun Sufaye ba su san mene ne addini ba.
Za mu dora a mako mai zuwa in sha Allahu.