• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Waje Ke Da Kwarin Gwiwa Game Da Kasar Sin? Baje kolin Kayayyakin Masarufi Ya Ba Da Amsa…

by CMG Hausa
3 years ago
Yan Kasuwar Kasashen Waje

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

“Ina son kasar Sin, akwai babbar damar samun ci gaba a kasar.” Guido.M.Ognibeni, shugaban wani kamfanin sarrafa kayan kwalliya na kasar Italiya ne ya bayyana haka, a gun bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na 3 da aka gudanar daga ranar 10 zuwa 15 ga wata a birnin Haikou na kasar Sin. Akwai ‘yan kasuwan kasashen waje da dama da ke da kwarin gwiwa game da kasar Sin kamar wannan jami’in. Wannan bikin baje kolin kayayyakin masarufi shi ne karo na farko da kasar Sin ta gudanar da babban baje kolin kasa da kasa, tun bayan da aka yi nasarar gudanar da aikin rigakafi da shawo kan cutar COVID-19 yadda ya kamata, wanda ya jawo kayayyakin masarufi sama da 4,000 daga kasashe da yankuna sama da 60 na duniya.

Ga kamfanoni da yawa na kasashen waje, wannan bikin baje kolin ba kawai dandali ne na nuna samfurori ba, amma wata dama ce da za ta haifar a nan gaba. Tun bayan irin baje koli na farko da aka gudanar a shekarar 2021, kamfanonin kayan masarufi na kasa da kasa da dama, sun zauna a lardin Hainan, inda suka shiga cikin ayyukan raya cibiyar yawon bude ido da kayan masarufi ta kasa da kasa ta Hainan. A ganin wadannan kamfanoni, yanayin kasuwanci mai inganci da yadda Sin take bude kofofinta ga ketare, da matakai daban-daban na bude kofa da yarjejeniyar RCEP ta gabatar, musamman ma halin musamman na bude kofa da yankin ciniki cikin ‘yanci ta Hainan ke ciki, dukkansu sun ba su damammakin samun ci gaba a kasar ta Sin, har ma da bunkasa a duk duniya.

A yau Asabar 15 ga wata ne, aka rufe bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa karo na uku, sannan aka bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da fitarwa daga kasar Sin karo na 133. Bukukuwan baje kolin kasa da kasa da kasar Sin ke gudanarwa daya bayan daya, sun nuna yadda kasar ke ci gaba da cika alkawarin da ta dauka, wato kokarin mai da kasuwar kasar zama kasuwar duniya, kasuwar hada-hadar kudi, kasuwar kowa da kowa. Duk da yanayin da duniya ke ciki na rashin tabbas, tabbacin da kasar Sin ta samu ya kasance ginshikin kiyaye zaman lafiya da ci gaban duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
Daga Birnin Sin

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
Next Post
Kin Amincewa Da Kwangilar Dala Miliyan 22 Ta Yi Sanadiyyar Sauke Ni Daga Shugabancin NPA –Hajiya Hadiza Bala-Usman

Kin Amincewa Da Kwangilar Dala Miliyan 22 Ta Yi Sanadiyyar Sauke Ni Daga Shugabancin NPA –Hajiya Hadiza Bala-Usman

LABARAI MASU NASABA

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

November 8, 2025
Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

November 8, 2025
Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

November 8, 2025
An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

November 8, 2025
An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

November 8, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.