Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home ADABI

Mene Ne Adabin Kasuwa? (III)

by Tayo Adelaja
October 1, 2017
in ADABI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Dr. Bashir Abusabe

Cigaba daga makon jiya

samndaads

 

Adabin Kasuwar Kitsch a Jamus

Shi wannan adabin na Kitsch ba wai na talakawa ba ne kadai, na sababbin matsakaitan tajirai ne da suke da kudin sayen irin wadannan ayyuka, amma karfinsu bai kai na sayen adabin masu gari ba, sun yi haka ne domin a tunaninsu sayen wannan aikin adabin zai sa su tafi kafada-kafada da sarakuna da tajiran Jamus, masu sayen ayyukan adabi na kwarai. Duk da cewa Kitsch ya samu karbuwa a tsakanin jama’a, duk da haka bai wuce adabin kasuwa ko yayi ba ga sauran jama’a, musamman masu sarauta da tajirai, domin kuwa ba a yi aikin da kyau ba ko kuma takardun da aka zayyana hoton ko buga aikin adabin sun kasance na banza, ba su da aminci. Ke nan adabin Kitsch bai wuce adabin Jamus da bai da mazaunin kwarai ba a tsakanin masu mulki da tajirai ko kuma yana magana kan abubuwan da ba su ne aka sa gaba ba a tsakanin al’ummar, ko kuma dai gwanjon adabi ne ko adabi ne da ke kwaikwayon wani adabi, ba tunani ko kirkirar wanda ya samar da shi ba ne ko da kuwa ya samu karbuwa tsakanin wasu gungun mutane, (Cuddon, 1999).

Saboda haka kamar yadda muka gani a baya, Kitsch wani nau`in adabi ne da wanzu a kasar Jamus wanda yake nufin duk wani aiki na zane ko aikin adabi wanda masu mulki ko masu kudi ba su yi na`am da shi ba. An samar da wannan adabi ne mai suna Kitsch domin a mai da martani ko ya yi jayayya da ayyukan adabi da aka samar a karni na 18 da na 19 wanda yake ana masa kallo na masu mulkin kasaita da fitattun masu kudi ne. Shi dai wannan salon adabin yana da matukar alaka da adabin da ke tashe ko kuma na yayi, ba wani abu ya sa aka kira shi da haka ba kuwa sai ganin cewa aikin da aka yi na zanen ko aikin adabin ba a yi shi yadda za a iya cewa ya ginu ko tsaru ba.

Ke nan adabin Kitsch an samar da shi ne domin matsakaitan masu kudi ko masu mulkin da ba su kai su yi gogayya da wadanda suka yi fice ba, duk da haka su ma wadanda suka yi ficen, ganin karko ko kuma yanayin da wannan adabi ya fita da yadda mutane ke rububinsa ya sanya suka fara saye da karanta shi.

Za mu iya cewa adabin Kitsch ya kasance na kasuwa ne kawai domin ganin fasalin yadda aka samar da shi ba mai aminci ba ne, ma`ana kayan da aka yi aiki da su wurin samar da wadannan zane ko ayyukan adabin ba su da inganci, kuma an samar da su ne ganin cewa wadanda suke sayen shi ba su iya sayen manyan ayyukan adabi, wato wannan yana da saukin kudi ga masu sayen shi, kusan kowa zai iya sa kudi ya saye shi Wannan ya sa ake danganta adabin Kitsch, (Wikipedia.org ) da duk wani aikin adabi ko zane da aka samar maras kyau, wanda zai iya biya wa mai saye da bukatarsa, ma`ana zai kashe masa kishirwa daga abin da yake so ya gani ko ya karanta, musamman cikin wata sabuwar kama ko siffa, a ayyukan adabin wanda aka kwaikwaya daga wanda ya gabace shi ko suke rayuwa tare. Wannan ne ya sa irin wannan tsari ko fasali ya sha suka daga masana, fitattun daga cikin su kuwa su ne; Gabriel Thuller da wanda ya goyi bayan cewa wannan adabi na Kitsch bai dace da zamanin ba, domin ba gwanaye ke yin sa ba. Haka kuma wani fitaccen masani a fannin zane Georg Wilhelm Friedrich Hegel ya jaddada cewa zane-zanen wannan zamani yana da alaka da wani yanayi na lokacin da aka samar da shi, ba abin damuwa ba ne, in dai ya samu karbuwa daga masu karatu.

 

Adabin Kasuwa Na Larabawa

Shi ma adabin Larabci kamar sauran ya sha kwaramniya har zuwa lokacin da aka samar da na zamani wanda yake da alaka da na Yammacin Dauri, (Neo-Classical), wanda ya nemi ya canza fasalin adabin Larabci gaba daya, wato wanda za a ce ya samo kayan aikinsa daga wanda ya gabata, kamar su Makamatul Hariri da Alfu Laylah, saboda haka su wadannan na zamanin sai ya kasance sun koma ko dai suna samo kayan gininsu daga wadannan ko kuma suna juyar aikin marubuta adabin yammacin dauri ne kai tsaye, suna mai da su na Larabci.

An dai fara buga labarin Ziedan a farkon karni na 18 a cikin jaridar kasar Misira, wato Al-Hilal. Ba wani abu ya sa aka kira ayyukan wadannan mutane da na ya yi ko na kasuwa ba sai ganin cewa su ne ayyukan da mutane suka fi sha`awa, saboda irin yadda aka samar da su da harshen da kalmomin da aka yi amfani da su da kuma yadda aka tsara su, sai kuma ficen da marubutan suka yi. Sauran wadanda suka kasance a cikin wannan tsarin sun hada da Khalil Gibran da Mikha`il Na`ima.

Amma dai masana da dama na adabin Larabci sun bayyana cewa, an fi ganin littafin Zaynab na Muhammad Husayn Haykal da Adraa Denshawi na Muhammad Tahir Hakki da kasancewa ayyukan adabi na farko a wannan karni masu kama da ayyukan adabin jama’a ko kasuwa, fiye da wadancan da muka ambata a baya. (dubi karin bayani a Arabic Literature The free encyclopedia). Daga nazarin da aka gudanar an fahimci cewa litattafan adabin yayi ko na jama’a na Larabci sun fi bayyana rayuwar iyali, misali ayyukan Naguib Mahfuz na Cairo Trilogy, inda ya siffanta rayuwar iyali.

 Za mu cigaba insha Allahu

SendShareTweetShare
Previous Post

Ni Na Hana Kaina Fim Ba Mijina Ba — Fati Ladan Ashe Ta Haihu Babu Rai H

Next Post

Gidan Dabino: Gwarzonmu Na Wannan Mako

RelatedPosts

Fitattun Littattafan Hausa A 2020

Fitattun Littattafan Hausa A 2020

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

Masu iya magana suka ce 'komai ya yi farko zai...

Rayuwan Aurena

Sharhin Littafin: A Rayuwar Aurena: Abin Da Ba Zan Manta Da Shi Ba

by Muhammad
2 weeks ago
0

Na Adamun Adamawa Bauchi Daga Yusuf Kabir 09063281016 Sunan wannan...

Zama Farfesa

Ina Son Zama Farfesa, Cewar ’Yar Shekara 18 Da Ta Wallafa Littafi A Kebbi

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

MAIMUNA GARBA HAMMANI wata matsashiyyar yarinya ce ’yar Shekaru 18...

Next Post

Gidan Dabino: Gwarzonmu Na Wannan Mako

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version