Wasu masu yawon shakatawa 20 na kasar Japan sun yi yawo a sassan jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin cikin tsawon kwanaki 9, inda suka gane ma idanunsu yanayin rayuwar al’ummar jihar da ma al’adunsu.
Kafin wannan, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Japan ta shirya wani aiki na tara masu yawon shakatawa da suke son zuwa jihar Xinjiang, kuma dimbin mutanen kasar ta Japan sun yi na’am da kiran, wadanda kuma suka biya kudin yawon da kansu. Sai dai kafin su fara wannan ziyara, sun nuna shakku game da yanayin da ake ciki a jihar, sakamakon rahotannin da kafofin yada labarai na kasarsu suka bayar game da jihar.
Da suka isa Xinjiang, sun ziyarci gonakin auduga na zamani, inda suka samu fahimtar yadda ake amfani da na’urorin zamani wajen noman auduga, wato cikin kwanaki biyu kadai za a iya kammala shuka auduga a gonaki masu fadin eka 20, tare da kammala aikin fesa maganin noma cikin sa’o’i biyar. A game da wannan, Akihiko Inoue ya ce abin ya burge shi matuka, wanda ke nuni da cewa babu wani batu na “aikin tilas” da kafofin yada labarai na kasarsu Japan ke watsawa, saboda tuni aka fara yin amfani da na’urorin zamani wajen ayyukan gona a jihar ta Xinjiang. A wata masaka kuma, da suka ga yadda ma’aikata masu kwarin gwiwa ke amfani da injunan saka na zamani, malama Watanabe Yumi ta ce, tabbas za ta bayyana abubuwan da ta gani da idanunta ta shafinta na sada zumunta, don fahimtar da karin mutane a kan hakikanin yanayin da ake ciki a Xinjiang, saboda ya sha bamban da ikirarin keta hakkin dan Adam da kafofin yada labarai na kasarsu ke yadawa.
A cikin ’yan shekarun baya, jami’an diplomasiyya da ’yan jarida sama da 1000 da suka fito daga kasashe da yankuna fiye da 100 sun ziyarci Xinjiang, inda suka gane ma idanunsu kyakkyawan yanayin jihar Xinjiang da bunkasuwarta.
Sai kuma a tarukan da majalisar hakkin dan Adam ta MDD ta shirya a shekarun baya, kusan kasashe dari suka yi ta bayyana goyon bayansu ga matsayi mai adalci na kasar Sin, tare da yin Allah wadai da kasashen yammacin duniya bisa manufar siyasa da suke neman cimmawa.
A gaba, muna maraba da karin baki da su ziyarci jihar Xinjiang. Don Gani Ya Kori Ji. (Lubabatu)