Tambaya:
Assalamu alaikum Allah ya gafarta Mallam, don Allah ina Matsayar Malamai akan wadannan Mas’aloli, tare da ambaton dalilai daga Kur’ani/Hadisi: Mutane nawa ne Ya tabbata a Alkur’ani/Hadisi Sun yi Mutuwar Shahada? Domin wani Dalibi abokina ya ce: Albani ya Ambaci mutum 9 a cikin AHKAMIL JANA’IZ, kuma na duba ban gani ba, sannan idan Mace ta Mutu a yayin haihuwar Cikin Shege, shin ita ma ta yi Shahada?
Amsa:
Wa’alaikumus salam.To dan’uwa shahidai suna da yawa: sun haura guda tara : Ibnu- hajar yana cewa : “Mun tattara hadisan da suka yi bayani akan shahidai sai muka samu sama da nau’i ashirin na shahidai, Fathul-bary 6\43 hakanan Suyudi a littafinsa mai suna : Abwabissa’adah fi asbabi assa’adah, ya kawo sama da guda talatin Ka ga daga ciki, akwai wanda ya mutu a fagen daga, da wanda ya mutu da ciwon ciki, sai wanda ya mutu a lokacinn kwalara sai kuma wanda ya mutu ta hanyar rusowar gini, sai wanda ya nutse a ruwa, Hakanan wanda ya mutum wajan kare dukiyarsa, da wanda kunama ko mijiji ya harba, sai ya yi ajlinsa, haka matar da ta mutu wajan haihuwa, dama wanda namun daji suka cinye shi Haka wanda aka kashe shi saboda kare iyalansa, duk wadannan sun tabbata a cikin hadisai .
Sai dai wasu malaman suna ganin akwai sharuda kafin mutum ya samu shahada: Daga ciki kada ya zama: Ba ta hanyar gangaci ya mutu ba, kamar mutumin da bai iya ruwa ba, ya shiga kogi, sai ya mutu, sannan kar ya zama ta hanyar sabo ya isa zuwa shahadar, kamar matar da ta mutu wajan nakudar cikin shege, ko bawan da ya gujewa mai gidansa, sai ya mutu a hanya, wasu kuma suna ganinin hakan ba sharadi ba ne, tun da hadisan ba su kayyade ba.
Don neman Karin bayani duba: Fataawal-kubra na Ibnu-taimiyya 3\22 da Mugni A l-muhtaj 3/166
Allah ne mafi sani.
Shin Sunan Rumaisa’u Yana Da Asali A Musulunci?
Tambaya:
Assalamu alaykum. Malam menene asalin sunan Rumaisa ko Rumassa’u kuma a zamanin Annabi akwai mai sunan, in akwai a bani tarihin ta?
Amsa:
Wa’alaikum assalam, Rumaisa’u suna ne na daya daga cikin sahabbai mata, ita ce ta haifi Anas Dan Malik hadimin Annabi (SAW), ita ce ta kai shi wajan manzon Allah don ya dinga masa hidima, ta auri Abu-dalha, sahararren sahabi mutumin Madina, an fi saninta da sunan Ummu-sulaim. Tana daga cikin mataye masu hikima, akwai mahaddatan Alku’ani da yawa da suka fito daga tsatsonta.
Allah ne mafi sani.
Yadda Ake Warware Matsalolin Rayuwa A Saukake
Tambaya:
Assalamu alaikum da fatan mal ya tashi lafiya, wata ‘yar uwa ce take son karin bayani a kan wani lamari wato ya kasance tana da aminiya sai take gaya mata matsalolnta, sai ta hada ta da wani Dan’uwanta malami a kan zai bata addu’oi, sai ta ce tana so kuma ya mata istihara sai suka je sai ya yi istaharan, a lokacin ya mata bayani kamar yadda ta yi wa kawarta bayani har ya karbi kudin da za’a yanka kaza saboda za a karanta Suratul Yaasin. Malamin sai ya ba ta rubutu ya ce ta sayi tumbin shanu ta dafa da rubutun. Ta kuma yi amfani da kifiya tana ci, dai-dai lokacin ta roki Allah ya kare ta daga sharrin makiya, amma daga baya da ta yi tambaya, sai aka ce ta guji irin wadannan malaman, har dai daga bisani tazo ta karyata abin, to malam ya matsayinta yake?
Amsa:
Wa alaikum assalam, akwai alamun da suke nuna cewa wannan malamin ba mai ilimi ba ne, don haka Ina ba ta Shawarar da ta rabu da shi don kar ta fada cikin halaka.
Ana iya samun waraka daga matsaloli ta hanyar yawaita istigfari da tuba zuwa ga Allah da mayar da hakkokin da ba na ka ba, da yawaita sadaka, da nisantar cin mutuncin mutane, da yawaita addu’o’i, saboda addu’a tana tunkude bala’i, taimakawa mutane da yaye musu bakin ciki na daga cikin abubuwan da suke warware mushkiloli, Annabi s.a.w. idan abubuwa suka dame shi yana ta shi izuwa sallah kamar yadda Abu-dawud ya rawaito shi kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 4171>
Gano ainihin matsala da shawartar masana wadanda suka goge a rayuwa yana taimakawa wajan warware wasu matsalolin, mutukar shawarar da su ka bayar ba ta sabawa ka’idojin sharia ba, ana iya samun mafita ın aka bita.
Allah ne mafi Sani.
Babu Bambanci Tsakanin Wiwi Da Giya A Haramci
Tambaya:
Assalamu Alakum. Malam ina da tambaya kamar haka,shin tabar wiwi tana daukan dukkanin hukunce hukuncen da suka hau kan giya (barasa)ko kuwa akwai banbanci.Dafatan zanga amsan wannan tambaya a Zauren Fikhu, nagode.
Amsa:
Wa’alaikum assalam, mutukar ta amsa sunanta na WIWI kuma tana bugarwa, tabbas za dauki dukkan hukunce-hukuncen giya na haramci.
Annabi S.A.W yana cewa “Dukkan abin da yake sanya Maye giya NE, kuma dukkan giya haramun ce” kamar yadda Nasa’i ya rawaito a hadisi ingantacce, wannan sai ya nuna haramcin shan WIWI da duk abin da yake sanya maye.
Allah ne mafi Sani.
Mijina Ya Yi Min Kome, Bayan Na Shiga Jini Na Uku, Ya Halatta?
Tambaya:
Salaamun alaikum .malam inada tambaya danAllah.A fahimta ta idan aka saki mace saki daya iddarta tsarki uku ne dalili fadin Allah subhaanahu cikin suratul bakara aya 228. Sai nazo naji sharhin wani malami cewa”idan aka saki mace cikin tsarki zata kirga wannan tsarki a matsayin tsarki 1,idan tayi al’ada ya zama tsarki na 2 kenan idan ta sake al’ada tsarki uku kenan ma’ana ta gama iddarta. Ko kuma yace idan tana al’ada aka saketa to idan ta sake wata al’adar zata ce 1,ta kara wata tace 2,ta kara wata tace 3,ta gama iddarta kenan. Tambaya anan malam itace ,saboda fahimta ta ta tsarki uku,mun sami sabani da miki na har saki ya auku kuma ina cikin tsarki,nayi tsarki na daya,nayi na biyu ina cikin al’ada ta uku ya ce ya maidani kuma na koma. duba da sharhin malamin da na fada maka ina matsayin kome na a shari’a ?danAllah malam ina cikin fargabar ko mun sa6ama shari’a .idan ko mun sa6a malam mecece mafita? Allah ya karawa malam lafia da basira Amin.
Amsa:
‘Yar’uwa in har kin shiga jini na uku, a iddarki, ta bayan saki sannan mijinki ya miki kome, to komen ya inganta a bisa mazhabar Abu Hanifa, amma a fatawar Imamu Malik kin kammala idda, tun da kın shiga cikin jini na uku, saidai duk mazhabar da kika dauka kika yi aiki da ita a nan wurin, ta yi, tun da lafazin Kur’i da ya zo a aya ta : 228 a suratul Bakara yana daukar ma’anar haila, yana kuma daukar ma’anar tsarki, Don haka in har kin tabbata kafin kammala jini na uku ya miki kome, to cigaba da mu’amalar auranku babu matsala. Allah ne mafi Sani.
Don neman Karin bayani duba: Tafsirin Ibnu Kathir 1\542.
Allah ne mafi sani.
Wane Lokaci Ne Ya Fi Dacewa A Yaye Yaro A Musulunci?
Tambaya:
Asslam ya shaikh: Allah yakara wa Doctur lafia amin. Don Allah mallam wane lokaci ne mafi inganchi da ya dace a yaye yaro daga barin shan nono a shariance? Nagode Allah yasaka da alkhairi amin.
Amsa:
To dan’uwa ina rokon Allah ya amsa addu’arka, Lokaci Mafi çıka na yaye yaro shı ne: idan ya kai shekaru biyu, kamar yadda aya ta: 233 a suratul Bakara ta tabbatar da hakan, saidai ya halatta a yaye yaro kafin ya cika shekaru biyu, mutukar ba zai cutu ba, kuma iyaye guda biyu sun cimma daidaito akan hakan.
Don neman karın bayani duba: Tafsirin Kurdubi 3/162.
Allah ne mafi Sani.
Wace Irin Tsintuwa Ce Ake Yi Wa Cigiya?
Tambaya:
Assalamu alaikum malam wani bawan Allah ne ya tsinci Naira: #500#, a wurin kuma bai ga wadanda zai yi wa cikiya ba… Ya ya kamata yayi da kudin tsintuwar ?, suna ajiye yanzu haka kusan wata daya .
Amsa:
Wa alaikum assalam. To dan’uwa idan mutum ya yi tsintuwa ya wajaba a gare shi ya yi cigiya har tsawon shekara guda, idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da ita, amma in mai ita ya zo daga baya zai biya shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 5761. Amma idan abin da ya tsinta dan kadan ne ba shi da yawa, to ya halatta ya yi amfani da shi ko da bai yi cigiya ba, saboda abin da aka rawaito cewa : Annabi s.a.w. ya ga wani dabino akan hanya, sai ya ce : In ban da ına tsoron na sadaka ne da na ci. Muslim ya rawaito a lamba ta:2527, sai hadişin ya nuna dan karamin abu ba ya bukatar cigiya.
Malamai şun yi sabani wajan iyakance tsintuwar da ba ta bukatar cigiya, wasu sun ce za’a koma al’adar mutane, duk abin da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to in an tsince shi ba ya bukatar cigiya, Ibnu Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa: bai wajaba mutum ya yi cigiyar abin da bai Kai a yanke hannu saboda shi ba, wato daya bisa hudun dinari, haka nan sayyadina Aliyu ya tsinci dinare daya ya yi amfani da ita ba tare da yayi cigiya ba. Abin da ya gabata yana nuna cewa: mutukar ba ka samu mai Naira (5,00) din da ka tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta ka yi amfani da ita ba tare da cigiya ba, tun ba kudi ne mai yawa ba, kuma mai ita ba zai kwallafa rai Akanta ba. Don neman karin bayani duba : Al-mugni 6/351.
Allah ne mafi Sani.