Tauraron dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Lionel Messi, ya kafa makamancin tarihin da Davi Hernandez ya bari na bugawa kungiyar wasanni 505 a gasar La Liga tun bayan daya fara bugawa kungiyar wasa..
Messi ya kafa tarihin ne yayin fafatawar da suka yi da kungiyar kwallon kafa ta Alabes a ranar Asabar, wadda suka lallasa ta da 5-1 wasan da yabawa magoya baya mamaki ganin yadda kungiyar ta samu koma baya a wannan kakar.
A wasa na gaba da za su fafata da kungiyar kwallon kafa ta Cadiz ake sa ran Messi ya bugawa Barcelona wasa na 506 a La liga, abinda zai bashi damar goge tarihin tsohon tauraron kungiyar Dabi.
Har yanzu dai Dabi Hernendez ke rike da tarihin zama dan wasan Barcelona da ke kan gaba wajen buga mata wasanni a jumlace, bayan haskawa a dukkanin fafatawar da tayi sau 767, sai dai wasanni 8 kawai suka rage Messi ya buga kafin goge tarihin.
A watan Oktoban shekarar 2004, Messi ya bugawa Barcelona wasa na farko, kawo yanzu kuma ya ci mata kwallaye 651, tare da taimaka mata wajen lashe kofin gasar La Liga 10, da kofin gasar Zakarun Turai guda 4.
A wata hira da akayi da Messi a kwanakin baya ya bayyana cewa bai damu da tarihin da yake kafawa ba a Barcelona idan har kungiyar bata kokari inda kuma yayi kira ga ragowar ‘yan wasan kungiyar akan su dage domin fitar da magoya baya kunya.