Daga Abubakar Abba,
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Lionel Messi ya kafa tarihin zama dan wasa na farko a kudancin Amurka da ya zazzaga kwallo 80 a raga a kudancin Amurka.
Ranar Lahadi Argentina ta doke Uruguay 3-0 a wasan neman gurbin buga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a shekarar 2022 kuma kyafti Messi ne ya fara cin kwallo daga baya Rodrigo de Paul ya kara ta biyu, sannan Lautaro Martinez ya zura ta uku a raga.
Kawo yanzu tawagar Argentina ta yi wasanni 24 ba a doke ta ba, kuma wannan nasarar ta kara sa matsi ga Brazil a wasannin Kudancin Amurka a neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Kuma nasarar da Argentina ta yi, wadda take ta biyu a teburi ta rage tazarar maki tsakaninta da Brazil ta daya ya koma shida, bayan Colombia da Brazil suka tashi 0-0 ranar Lahadin daga gabata.
Karon farko da Brazil ba ta ci wasa ba a wasanni 10 kenan, bayan da ta yi nasara a wasanni tara a bana a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a katar a badi wato shekara ta 2021.
dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Lionel Messi ya kafa tarihin zama dan wasa na farko a kudancin Amurka da ya zazzaga kwalle 80 a raga a kudancin Amurka.
Ranar Lahadi Argentina ta doke Uruguay 3-0 a wasan neman gurbin buga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a shekarar 2022 kuma kyafti Messi ne ya fara cin kwallo daga baya Rodrigo de Paul ya kara ta biyu, sannan Lautaro Martinez ya zura ta uku a raga.
Kawo yanzu tawagar Argentina ta yi wasanni 24 ba a doke ta ba, kuma wannan nasarar ta kara sa matsi ga Brazil a wasannin Kudancin Amurka a neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Kuma nasarar da Argentina ta yi, wadda take ta biyu a teburi ta rage tazarar maki tsakaninta da Brazil ta daya ya koma shida, bayan Colombia da Brazil suka tashi 0-0 ranar Lahadin daga gabata.
Karon farko da Brazil ba ta ci wasa ba a wasanni 10 kenan, bayan da ta yi nasara a wasanni tara a bana a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a badi wato shekara ta 2022.