Abba Ibrahim Wada" />

Messi Ya Yi Kuskure A Matsayinsa Na Babba – Kociyan Bilbao

Kociyan Bilbao

FILE PHOTO: Soccer Football - Europa League - Valencia Press Conference - Sports City of Paterna, Valencia, Spain - May 8, 2019 Valencia coach Marcelino Garcia Toral during a press conference REUTERS/Heino Kalis

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Athletico Bilbao, Marcelino Garcia, ya bayyana cewa dan wasa kuma kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi, yayi kuskure na dukan dan wasan kungiyar da hannu dalilin da yasa aka bashi jan kati.

Mai shekara 33 ya fara karbar jan kati a wasan da tawagarsa ta Argentina ta yi da Hungary a 2005 sannan ya kuma karbi na biyu a Copa America wasan neman mataki na uku a 2019 a wasa tsakanin Argentina da Chile.

Watakila a dakatar da Messi buga a kalla wasa hudu da zai iya shafar La Liga da sauran kofunan gaba da ake buga wa a Spaniya kuma kawo yanzu Messi shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Spaniya domin yana da kwallaye 11 a raga, kuma Barcelona tana ta uku a teburin gasar bana ta La Liga.

Yanzu dai kofin da kungiyoyin Spaniya ke hari shi ne Copa del Rey da ya kamata Barcelona da Real Madrid za su buga ranar Laraba da Alhamis wanda ake fatan daya daga cikinsu zata iya lashewa tunda sun rasa Spanish Super Cup.

 

Gasar Copa del Rey Laraba 20 ga watan Janairu

Cordoba bs Real Sociedad

Alcoyano bs Real Madrid

 

Gasar Copa del Rey Alhamis 21 ga watan Janairu

UD Ibiza bs Athletic Bilbao

Cornella bs Barcelona

Kungiyar Balencia ce ke rike da Copa del Rey na shekarar 2018 zuwa 2019, bayan da ba a buga wasan karshe a kofin bara ba tsakanin Real Sociedad da Athletic Bilbao, saboda koma baya da cutar da korona ta haddasa kuma Barcelona ce kan gaba wajen yawan lashe Copa del Rey mai guda 29, sai Athletic Bilbao da guda 22 da kuma Real Madrid mai 19 jumulla.

 

Kofin gasar La Liga

Sai a ranar Laraba 23 Real Madrid za ta ziyarci Deportibo Alabes a wasan mako na 20 a gasar La Liga ita kuwa Barcelona za ta ziyarci Elche ranar Alhamis 24 a wasan na mako na 20 a gasar ta kasar Spaniya.

Real Madrid tana mataki na biyu a teburi da maki 37, Barcelona mai maki 34 tana biye da Real sai Atletico Madrid mai kwantan wasa biyu ce kan gaba a teburin La Liga mai maki 41 kuma  Real Madrid ce mai rike da kofin La Liga, yayin da Barcelona ba ta ci kofi ko daya ba a kakar bara.

 

Gasar Champions League

Haka kuma kungiyoyin biyu na Spaniya sun kai karawar zagaye na biyu a Champions League na bana sannan ranar 16 ga watan Fabrairu, Barcelona za ta karbi bakuncin Paris St Germain, yayin da Real Madrid za ta ziyarci Atalanta ranar 24 ga watan na Fabrairu.

Exit mobile version