Lokutan mika mulki na shugaban kasa lokuta ne na farin ciki a tsakanin al’umma sannan kuma lokuta ne mafi damuwa ga masu mika madafun iko. Lokutan mika mulki suna da wata alaka da damuwa da dimauta mai cike da dimbin rikici da kalubale.
Shugaban kasa mai barin gado, ba wai kawai zai cigaba da jagorancin kasa ba ne, dole ne ya fara shirya mika ragamar shugabancin ga sabon shugaba mai jiran gado da tawagarsa.
A wannan lokaci, shugaba mai barin gado bai da wata cikakkiyar karfin guiwa sabida kusan duk al’amuran mulki da kwarjini a wurin Jama’a ya fara komawa wurin shugaba mai jiran gado.
Shugaban kasa da tawagarsa za su fara fuskantar halin da ake ji na rabuwa da mulki musamman na fara rasa abokai masu son alaka da makusanta kujerar shugaban kasa.
Ziyarar ban-girma da aka saba kaiwa shugaban kasa mai ci a sannu a hankali sai ta fara gushewa ta koma bangaren zababben shugaban kasa.
Wadannan halaye na siyasa – fara janyewa daga shugaba mai barin gado zuwa mai jiran gado, a karshe dai duk za su dusashe da zarar an mika mulki. Wannan rana ta bikin mika mulki ga shugaban kasa a Nijeriya, za a yi ta a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
A Nijeriya, daga 1999 zuwa yau, an yi bukukuwan mika mulki sau shida, amma sau uku daga shugaban kasa zuwa wani shugaba – Obasanjo zuwa ‘Yar’Adua/ Jonathan, Jonathan zuwa Buhari, yanzu kuma Buhari zuwa Tinubu.
Akwai nau’o’i biyu ne na mika mulki na shugaban kasa: akwai daga shugaban kasa zuwa shugaban kasa a karkashin jam’iyya daya sai kuma wanda ba a karkashin jam’iyya daya ba suka fito. Duka wadannan nau’ikan a Nijeriya mun dandanasu bisa tsarin dimokuradiyya, wannan alama ce na Nijeriya tana kan turbar Dimokuradiyya.
Kowane canji yana haifar da kalubale da firgici daban-daban da kiyayya. Amma kuma a wannan sauyin na halin yanzu akwai aminci sosai fiye da yadda aka saba ganin sabani tsakanin zababbe da mai barin gado – Shugaba Buhari na jam’iyyar APC zai mikawa zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC mulki.
Wannan shi ne bangare mafi sauki na wannan mika mulki na shugaban kasa da ke cike da cece-kuce kuma ya raba ra’ayoyin jama’a zuwa mabambantan ra’ayi – wasu suna kira da a dage rantsar da shugaban kasa sabida dalilai daban-daban na zato, wasu kuma suna nan kan cewa, babu wani dalili da zai hana rantsar da zababben shugaban kasa, bisa ga ka’ida da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin mu. Duk suna da hakkin ra’ayinsu amma dole ne dokar kasa ta yi rinjaje.