An ceto wata mata mai matsakaicin shekaru, Sadiya bayan da mijinta ya tsare ta a gidansa har tsawon shekara daya ba tare da abinci ba a garin Nguru da ke Jihar Yobe.
Matar wadda uwa ce ga ‘ya’ya hudu ‘yar asalin Jihar Kano.
- ‘Yar Nijeriya Amusan Ta Shiga Sahun ‘Yan Wasa Mata Na Duniya Da Za A Karrama A 2022
- An Jinjinawa Matakan Sin Na Shawo Kan Kalubalen Sauyin Yanayi
Leadership Hausa ta gano cewar mahaifiyar Sadiya ce, Hadiza, ta ceto ‘yarta daga mawuyacin halin a makon jiya.
Wata majiya mai tushe wacce ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa manema labarai cewa, “Mahaifiyar ta bayyana cewa ta je Nguru daga Kano domin ganin diyarta a lokacin da ta ji muryarta a waya ba dadi, amma sai ta hadu da ita a wani yanayi wanda rai yana hannun Allah.
“Matar tana fama da yunwa, mijinta dan da ‘yan uwansa suna kokarin cutar da ita ta hanyar hana ta abinci.
“Kunu ne kawai yake ba ta a duk lokacin da ta bukaci abinci kuma ya hana mutane shiga dakinta”.
A cewar majiyar, mijin mai suna Ibrahim Yunusa Bature kuma an ce kani ne ga tsohon Darakta Janar na hukumar NEMA, Mustapha Yusuf Maihaja da Jakadan Nijeriya a Kenya, Yusuf Yunusa.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa an garzaya da Sadiya zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano, inda a halin yanzu take jinya tare da mahaifiyarta.
Mahaifiyar matar ta yi kira ga Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni da ya shiga lamarin.