Bala Kukuru" />

“Mijina Marigayi Shehu Yar’Adua Ne Ya Tabbatar Wa Hausawa Kasuwar Alabar Rago”

Uwargidan Marigaya tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya na mulkin soja, Janar Shehu Musa Yar’Adua, Dakta Hajiya Asabe Yar’Adua kuma uwar kungiyar Katsinawa mazauna Legas ta bayyana cewar, mijinta ne ya tabbatar wa al’ummar Hausawa kasuwar Alabar Rago a Legas. Don haka ba ta ga dalilin da zai sanya gwamnatin jihar Legas ta tashi wannan kasuwar ba.

Dakta Hajiya Asabe ta yi wannan tsokaci ne a Legas a filin tashi da saukar jiragen sama da ke Murtala Muhammad jim kadan bayan saukarta daga jirgin sama a lokacin da ta dawo daga Kasa Mai Tsarki, domin gudanar da addu’o’i na musamman ga Nijeriya, don samun karin cigaba da kuma zaman lafiya bakidaya.

Ta cigaba da cewar a kan haka ne ta ke ba gwamnatin jihar Legas shawara da ta gaggauta kawar da wannan furuci na tayar da kasuwar ta Alabar Rago idan a ka yi la’akari da irin gudunmawar da kasuwar ke bayarwa a Legas da Nijeriya bakidaya ta fannin shanu da sauran dabbobi da kayan  abinci bakidaya.

Ta kara da cewar, gwamnatin jihar ta Legas ta yi adalci bisa ga la’akari da dimbin jama’ar daban-daban da su ke gudanar da harkikin kasuwanci kuma su ke cin abinci a kasuwar Hausawa, Ibo, Yarabawa da sauran kabilu a ka tashe su rana tsaka ba tare da an sama mun su wani wuri mai kyau ba.

Ta ce, akwai matsala ta cewa za ta tada kasuwar ta alaba tunda mijinta ya ba wa Hausawa wannan kasuwa ne, domin su cigaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu na yau da kullum kuma zama na dundundun ba tare da an tashe su an kai su wani wurin cutarwa ba.

A cewarta, ta na mamakin irin wannan furuci da gwamnatin jihar Legas ta ke yi wa wadansu kasuwanni  na al’ummar Hausawan arewacin Nijeriya mazauna jihar Legas haka nan kawai a ce kasuwa ta tashi babu laifin zaune balle na tsaye.

Ta ce, a kan haka ta ke kara shawartar gwamnatin jihar ta Legas da ta guji furta irin wadannan kalamai ga kasuwannin jihar ta Legas, domin jihar ta kara samun cigaba a maimakon tada hankulan al’umma bakidaya.

Sannan ta cigaba da umartar shuwagaban kasuwannin al’ummar Hausawa mazauna jihar ta Legas da su cigaba da tsaftace kasuwanninsu, domin kiwon lafiyarsu da ta al’umma bakidaya a kokarin gwamnatin jihar ta Legas na kare lafiya jama’ar bakidaya.

Da ta koma a kan kungiyar Katsinawa mazauna jihar ta Legas kuwa cewa ta yi ta na mai yaba wa shuwagabanin kungiyar a kokarinsu na hada kawunan al’ummar jihar Katsina a Legas, domin zama tsintsiya madaurinki daya gare su.

 

 

 

Exit mobile version