Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Mike Pompeo Mai Fuskoki Da Dama Yana Matukar Son Zama Shugaban Kasar Amurka

by
2 years ago
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Mike Pompeo Mai Fuskoki Da Dama Yana Matukar Son Zama Shugaban Kasar Amurka
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Cinikin Wajen Kasar Sin Ya Samu Ci Gaba Cikin Sauri

Masanin Najeriya: Yadda Amurka Da Kasashen Yamma Ke Furta Kalaman Tsokana Zai Kara Rashin Zaman Lafiyar Duniya

ADVERTISEMENT

Kwanan baya, Mark Brzezinski, dan shahararren ma’aikacin huldar jakadancin Amurka, ya shaidawa manema labarai na CMG cewa, kudi da neman kuri’u, sun zama tushen siyasar Amurka, kuma wasu ’yan siyasa masu neman riba sun kutsa kai cikin gwamnati yadda suka ga dama, cikin su hadda Mike Pompeo wanda ya yi kaurin suna a wannan bangare.
A matsayi wani ma’aikacin diplomasiyya maras ci gaba, a tsawo shekaru biyu da ya yi yana aiki, Mike Pompeo na da fuskoki da dama, inda ya dage wajen dora laifi kan sauran kasashe, game da gaza daukar matakan da suka dace don yakar COVID-19 a Amurka, da kuma illata hadin kan da aka samu a wannan fanni, lamarin da ya jefe jama’ar kasar Amurka cikin wani hali mai hadari.
Game da zanga-zanga da aka yi dake da alaka da adawa da nuna bambancin launin fata, ya yi kamar ba ya ji ko ba shi da masaniya, ya ci gaba da goyon bayan tsarin daukar matsayi biyu salon Amurka, bisa ra’ayin rashin lura. Ban da wannan kuma, ya dauki matakin matsawa kasar Sin lamba, don dora laifi kan ta, yayin da yake fuskantar rikicin al’umma cikin kasarsa. Ta wannan hanyar ne kuma yake yunkurin neman kuri’u ga bangaren da yake goyon baya.
Mike Pompeo mai fuskoki da dama, ya yi biris da nauyin dake wuyansa, a matsayin wani ma’aikacin diplomasiyya, ya kuma bar mutunci da muradun kasarsa, da na jama’a a baya, don cimma bukatar zama shugaban koli a kasar a nan gaba.
Gaza sauke nauyin dake wuyansa, da kuma neman moriya ta hanyoyi marasa kyau, da dai sauransu laifuffuka, dukkansu alamu ne na Mike Pompeo, amma abun tambaya a nan shi ne, me ya ba shi da karfin gwiwar yin hakan? Dalili shi ne, gaggauta yiwa shugabannin kasar kanzagi. Jaridar Washington Post ta fadi gaskiya da ta ce, sharudda mafi muhimmanci don shiga jikin shugabannin gwamnati a wannan karo su ne nuna rashin kunya. A wannan fanni kuwa, babu wanda zai zarce Mike Pompeo.
A wani bangare na daban kuma, Mike Pompeo ya dauki kwararan matakai kan batun dangantakar dake tsakaninsa da yankin gabas ta tsakiya, da Korea ta arewa. Har ma ya tilastawa gwamnatin kasar biyan bukatunsa ta hanyar nuna rashin imani. Kafar CNN ta taba ba da labarin cewa, Mike Pompeo shi ne mutum daya tilo da ya kitsa shirin kashe babban hafsan sojin kasar Iran, wanda hakan mataki ne da ya sabawa babbar manufar diplomasiyya da gwamnatin Amurka ke dauka.
Idan masu neman riba kamar Mike Pompeo sun jagoranci manufofi dake da alaka da kasar Sin, zuwa wata hanya ta kuskure, to lallai Amurkawa ne za su ji a jikin su. Yayin da shi kuma Mike Pompeo zai kafa mummunan tarihi. (Amina Xu)

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Babban Burin Kasar Sin Shi Ne Neman Hanyoyin Ci Gaba Tare Da Sauran Kasashe Masu Tasowa

Next Post

Kalaman Harzuka Jama’a: NBC Ta Ci Wani Gidan Rediyo Tarar Naira Miliyan Biyar

Labarai Masu Nasaba

Cinikin Wajen Kasar Sin Ya Samu Ci Gaba Cikin Sauri

Cinikin Wajen Kasar Sin Ya Samu Ci Gaba Cikin Sauri

by CMG Hausa
2 hours ago
0

...

Masanin Najeriya: Yadda Amurka Da Kasashen Yamma Ke Furta Kalaman Tsokana Zai Kara Rashin Zaman Lafiyar Duniya

Masanin Najeriya: Yadda Amurka Da Kasashen Yamma Ke Furta Kalaman Tsokana Zai Kara Rashin Zaman Lafiyar Duniya

by CMG Hausa
5 hours ago
0

...

Wang Yi: Manufar Amurka Ta Hadin Gwiwar Tekun Indiya Da Pacific Ba Za Ta Yi Nasara Ba

Wang Yi: Manufar Amurka Ta Hadin Gwiwar Tekun Indiya Da Pacific Ba Za Ta Yi Nasara Ba

by CMG Hausa
5 hours ago
0

...

Gwamnatin Sin Za Ta Baiwa Manoman Hatsi Rangwamen Yuan Biliyan 10

Gwamnatin Sin Za Ta Baiwa Manoman Hatsi Rangwamen Yuan Biliyan 10

by CMG Hausa
6 hours ago
0

...

Next Post
Kalaman Harzuka Jama’a: NBC Ta Ci Wani Gidan Rediyo Tarar Naira Miliyan Biyar

Kalaman Harzuka Jama'a: NBC Ta Ci Wani Gidan Rediyo Tarar Naira Miliyan Biyar

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: