Minista Ya Bude Ayyuka A Hukumar Shige Da Fice

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta shimfida wasu muhimman ayyuka a shalkwatarta da ke Sauka, hanyar babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe domin inganta ababen more rayuwa da kyautata yanayin aiki ga jami’anta.

Ayyukan da hukumar ta aiwatar wanda Ministan kula da harkokin cikin, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Damzau ya kaddamar a jiya Litini, sun hada da katafaren dakin taro, titin da aka gina shi da siminti mai karko da kuma shuke-shuken itatuwa don inganta muhallin hukumar ya zama kore shar.

Har ila yau, Ministan ya makala wa wata jami’ar hukumar da ta samu karin girma daga mukamin karamar mataimakiyar shugaban hukumar (ACG) zuwa babbar mataimakiya (DCG), Juliet Fariku.

Minista Dambazau ya yi wa LEADERSHIP A Yau karin haske kan dalilin zuwan sa shalkwatar hukumar ta NIS.

“Muna gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya sa muka ga wannan rana. Na zo don in kaddamar da abubuwa guda uku. Farko shi ne babban dakin taro wanda aka gina saboda ka san yanayin yanzu, a da can a kan je hotel ne a yi haya a biya kudi don a yi taro, amma yanzu da irin wannan babban daki da aka bude, ma’aikata sun samu wurin da za su yi taro. Kuma ka ga yadda aka kawata dakin ya kai matsayin na ko ina a fadin duniya.

“Na biyu kuma akwai wacce ta samu karin girma na Deputy Controller General (Mataimakiyar Shugaban Hukumar Shige da Fice), kuma tun da dai ina nan suka gayyace ni in saka ma ta sabon mukaminta da ta samu. Na uku shi ne bude wannan hanya da aka yi sabuwa wadda a maimakon yadda aka saba amfani da kwalta sai aka yi sabon salo aka gina da siminta domin hanyar ta ginu sosai ta yi karko don a samu a more ta shekara da shekaru”.

Abdulrahman Dambazau ya nunar da cewa muhimmancin ayyukan Hukumar ta Shige da Fice yana da daman gaske, inda ya cigaba da cewa,“Ita wannan ma’aikata ta kula da shige da fice ma’aikata ce mai muhimmanci. Na daya, su ke kula da sha’anin tsaron kan iyaka a tsakaninmu da kasa da kasa. Don haka dole mu yi kokarin ganin mun sa su kan hanya tare da goya musu baya don su yi aikin da zai sa kasa ta bunkasa. Saboda haka ma’aikata ce mai muhimmanci ga kasa baki daya ba ga ma’aikatar harkokin cikin gida ba kawai”.

Ministan ya ce suna alfahari da hukumar kuma ga dalilin hakan: “Abin da ya sa muke alfahari da wannan hukumar shi ne, duk wani al’amari da ya shafi shige da ficen kasa a hannunsu yake. Su ne ke ba da izinin shiga kasa wato biza, sannan duk wani Dan Nijeriya mai sha’awar fita waje sai sun ba shi fasfo. Saboda haka ko ta fuskar kasuwanci ma kawai ba karamin taimakawa hukumar take yi ba. Na biyu, idan ba su tantance su waye ke shiga mana kasa ba, za a samu mutane masu mugun hali su rika shigo mana. Shi ya sa muka tashi tsaye tare da ba su horon da ya kamata don tabbatar da cewa wajen da suke aiki waje ne da zai ba da dama su yi aiki cikin sauki”.

Da yake jawabi bayan bude babban dakin taron, Shugaban Hukumar Shige da Ficen ta Kasa, Muhammad Babandede ya bayyana cewa samar da dakin taron cika umurni ne na Gwamnatin Tarayya a kan cewa hukumomi da ma’aikatu su daina hayar otel don gudanar da taro, su samar da nasu na kansu.

Ya kara da cewa, “Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta dukufa wurin ganin ana kashe kudaden gamnati ta hanyoyin da suka fi dacewa. Shi ya muka samar da wannan dakin taro”.

Shugaban hukumar ya ce bayan samun amincewa daga Ministan, sun sake fasalin tsarin gudanarwa na hukumar inda aka raba sassa daban-daban kowa da aikinsa.

“Misali akwai sabon sashe na musamman domin kula da kan iyakokin kasa, da sashen da aka kebe domin aikin da ya shafi ba da takardar izinin shigowa kasa, akwai sashen shige da fice wanda a shekarar da ta gabata Ministan ya rattaba hannu kan tsararrun dokokin shige da fice, muna da sashen da yake kula da kudi da na ma’aikata. Duk wadannan suna da takamaimen ayyukan da suka sa gaba”, ya bayyana.

Da ya juya ga batun burin da hukumar ta sa a gaba kan inganta muhallin ofisoshinta ta hanyar shuke-shuken bishiyoyi, Muhammad Babandede ya ce, “Idan aka duba shalkatar hukumar za a ga bishiyoyin da ke ciki kalilan ne. Mun yi amanna da samun muhalli kore shar. Minista da manyan mataimakan Kwanturola Janar ko wanne zai suka bishiya daya kuma abin zai cigaba da gudana. Wannan za a rika yi har a sauran ofisoshinmu na yankuna”.

Daga bisani dai Ministan ya shuka bishiyarsa, shugaban hukumar ya shuka tasa, haka nan sauran manyan mataimakansa, kana ya yi umurni ga sauran kananan mataimakansa cewa kowa ya tabbatar ya shuka tasa.

Wacce aka kara wa girman daga ACG zuwa DCG, Juliet Fariku ta yi godiya ga Allah a kan matsayin da ta samu, kana ta gode wa Shugaba Buhari da Ministan cikin gida da Shugaban hukumar ta NIS bisa damar da aka ba ta ta yi aiki, inda ta yi alkawarin yin aiki tukuru.

 

Exit mobile version