Ministan ma’aikatar bunkasar harkokin ma’adanaiwta tarayya (ministry of Solid Minerals Development), Dele Alake ya yi kira na musamman ga dukkan hukumomi masu harkokin haka da sarrafa ma’adanai musamman a karamar hukumar Nasarawa da jihar baki daya su zauna lafiya da juna ayayin da suke gudanar da harkokinsu.
Alake ya yi kiran ne jim kadan bayan wani zama na musamman da ya yi da Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule da wasu mukarraban gwamnatinsa a gidan gwamnati da ke birnin Lafiya, fadar jihar ranar Litinin.
Dele Alake wanda darakta janar na sashin ma’aikatar da ake kira “Cadastry” a turance ya wakilce shi ya ce ba shakka kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da mahimmancin zaman lafiya a tsakanin masu harkokin ma’adanan don ta haka ne kawai za su samu ci gaba da bunkasar harkokin nasu a dukkan matakai.
A cewarsa, dole ne hukumomin daban-daban a jihar su hada kai su koma teburin sasantawa don warware duka rigingimu da ke tsakanin su kasancewar sai da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin su kadai hukumomi masu zuba jari daga gida Nijeriya da ƙasashen waje za su samu damar ci gaba da zuba jari a harkokin ma’adanan karamar hukumar ta Nasarawa da jihar baki daya.
Ministan Dele Alake ya kuma yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da abin da ya bayyana a matsayin gagarumin gudunmawa da gwamnatin sa ke bayarwa a kai-a kai wajen bunkasar harkokin ma’adanan da safarar su a dukkam matakai inda ya ce tabbas hakan ne ma ya aza jihar a mataki na gaba-gaba a ƙasar nan a fannin ci gaba da bunkasar ma’adanan a yanzu haka.
Daganan sai ministan ya kuma yi amfani da wannan damar inda ya sanar cewa tuni ma’aikatarsa ta yanke shawarar gudanar da wani gagarumin taro a watan Nuwambar shekarar 2024 kuma ma’aikatar ta zabi jihar Nasarawa a matsayin wajen da za a gudanar da taron bisa la’akari da gagarumin gudunmawa da take bayarwa wajen bunkasar harkokin ma’adananta da ta ƙasa baki daya.
Da yake jawabi, Gwamna Abdullahi Sule, bayan ya gode wa bakin nasa dangane da ziyarar da kuma zabar jihar tasa a matsayin inda za a gudanar da babban taron ma’adanan ya kuma tabbatar masu da cewa a shirye gwamnatinsa take ta ci gaba da bai wa fannin fifiko kasancewar Allah ya albarkaci jihar da dinbin ma’adanai iri daban-daban.
Sauran manyan baki da suka yi jawabi a yayin ziyarar har da kwamishinan ma’aikatar ma’adanai da albarkatun kasa na jihar ta Nasarawa, Honorabu Kwanta Yakubu inda suka yi fatan alheri da samun nasarorin da ake fatan gani a fannin na ma’adanai.