Yusuf Shuaibu">

Ministan Sufuri Ya Mika Daftarin Kasafin Manyan Ayyuka Na Naira Biliyan 205

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya mika daftarin kasafin kudin manyan ayyuka na shekarar 2021 na naira biliyan 205, kafin ma’aikatan ta samu damar kammala dukkan mahimman ayyukan da ta fara. Amaechi ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala jawabinsa ga hadaka na kwamitin majalisar dattijai da majalisar wakilai a Abuja. Ya bayyana cewa, a cikin naira biliyan 205 da za a kashe, sufuri ta kasa zai lakume naira miliyan 204, yayin da sufuri ta ruwa zai ci naira miliyan 845 tare da wasu naira miliyan 358 a shekarar 2021.

“Yawan kudaden da manyan ayyukan shuka ci a shekarar 2020 ya kai na naira biliyan 70, ida sufuri ta kasa ya ci naira biliyan 69.6, yayin da sufuri ta ruwa ya ci naira miliyan 698.

“A cikin wadannan kudade, naira biliyan 36 wanda ya kai na kashi 51.49 an zuda su ne a sufuri ta kasa, yayin da naira miliyan 90 suka tafi a sufuri ta ruwa a ranar 2 ga watan Nuwambar shekarar 2020.

“Bugu da kari, akwai naira miliyan 245 na ayyukan na musamma, a cikin kudin,  an kashe naira miliyan 177 ga ayyukan yau da kullum, inda a ranar 28 ga watan Oktobar shekarar 2020, aka kashe naira miliyan 158.

“Ma’aikata ta gabatar da daftarin kudin na manyan ayyuka da ya kai na naira biliyan 205, inda sufurin ta kasa zai lakume kudade wanda yawan su ya kai na naira biliyan 204, yayin da sufurin ta ruwa zai ci naira miliyna 845 da naira miliyan 359 na ayyukan yau da kullum a kasafin kudin shekarar 2021 wanda muke bukatar amincewar majalisa.

“Mahimmancin wannan daftarin kudade dai shi ne, yin amfani da su wajen kammala ayyukan da aka fara.

“Idan aka samu nasarar kammala titin jiragen kasa na zamani, za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasan kasar nan,” in ji Amaechi.

A cewarsa, cibiyan sufuri ta kimiyya da ke Nijeriya da hukumar da ke kula da harkokin jiragen kasa sun hada kai wajen samar wa kasar nan kudade. Minista ya kara da cewa, hukumar da ke kula da tashoshin jiragwn ruwa da makarantun koyar da sufuri ta ruwa da hukumar kula da sufurin kaya ta kasa da kasa za su samar wa kasar nan kudaden shiga a nan cikin gida da kuma kasashen ketare. Haka kuma ya bayyana cewa, hukumomi guda uku wadanda suka hada da hukumar da ke kula da tashoshin jiragen ruwa da hukumar da ke sufurin kayayyaki ta ruwa da ta kasa da kuma ta sama suma suna cikin wadanda za su samar wa kasar nan kudaden shiga masu yawan gaske.

Ya kuma ce, ma’aikatarsa tana taka mahimmiyar rawar a bangaren sufuri ta ruwa wajen aiwatar da manufofin gwamnati wanda hukumomin suke gudanarwa. Amaechi ya ce, daftarin kasafin kudin shi zai bayar da damar aiwatar da kammala dukka ayyukan da ma’aikatar da fara a shekarar 2021, yayin da za ta kammala sauran a cikin shekarar 2020. Ya ce, ma’aikatarsa ta mayar da hankali wajen kammala manyan ayyukan da ta fara kamar a Illela da Jibiya da Idiroko da kuma sauran ayyukan sufuri ta kasa a shekarar 2021.

Exit mobile version