• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Yaɗa Labarai Ya Kafa Kwamitin Tsara Cusa Ɗa’a Da Kishin Ƙasa

by Sulaiman
2 years ago
Ministan Yaɗa Labarai

A ƙoƙarin da ma’aikatar sa ke yi na fara shirin wayar da kan jama’a, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya kafa kwamitin da zai tsara daftarin cusa wa ‘yan Nijeriya ɗa’a, kishin ƙasa da kuma kyawawan ɗabi’u.

Daftarin Ɗa’a, Kishin Ƙasa da Kyawawan Ɗabi’u dai ya ƙunshi wasu tsare-tsare ne da ɗan Nijeriya zai ƙudurta amfani da su a zuciya da kuma aikace, waɗanda suka ƙunshi halaye nagari.

  • Shettima Ya Ziyarci Wadanda Sojoji Suka Jefawa Bam A Kaduna
  • An Kaddamar Da Cibiyar Buga Muhimman Takardu Ta AU Da Sin Ta Ba Da Taimakon Ginawa

Shugaba Bola Tinubu ne zai ƙaddamar da shirin a farko-farkon 2024.

Shirin Zai ƙunshi Ƙudirorin Alƙawarin Zama Ɗan Ƙasa Nagari, wanda ke ɗauke da shikashikai bakwai kowane.

Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar cusa wannan shirin ɗabbaƙa kishin ƙasa da kyawawan ɗabi’u a cikin manhajar karatu da kuma mu’amalar yau da kullum.

LABARAI MASU NASABA

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

Gwamnatin Tinubu na so ta ƙarfafa kyakkyawan tsarin zamantakewar ‘yan Nijeriya, a matsayin su na ‘yan ƙasa ɗaya amma kuma mabambantan ƙabilu da al’adu.

Kan haka ne ake ƙoƙarin shata tsarin wanda zai ƙara ƙarfafa ƙasar ta zama mai al’umma ɗaya, kuma mai dunƙulalliyar kyakkyawar mu’amala, ɗa’a da kishin ƙasa.

Cikin sanarwar da Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Suleiman Haruna ya sa wa hannu kuma ya fitar a ranar Laraba, ya ce Daraktar Wayar da Kai da Cusa Kyawawan Ɗabi’u (OBM) a Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) ce, Theresa Nnalue za ta tafiyar da ayyukan kwamitin.

Wannan kwamiti dai ya ƙunshi mutum 9, ƙarƙashin Dakta Muhammad Auwal Haruna, a matsayin shugaba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
Manyan Labarai

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Manyan Labarai

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu
Manyan Labarai

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
Next Post
kaduna

Matsalar Da Ta Haddasa Harin Bom Na Kaduna

LABARAI MASU NASABA

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025
Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

October 31, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.