Abubuwan Bukata
Kubewa danya
Attaruhu
Albasa
Manja
Gishiri
Sinadaran dandano
Kifi Timatir na leda
Kanwa
Za ki wanke kubewarki, ki raba ta gida biyu, rabi za ki markada a blander da ruwa, rabi kuma za ki yanka ta kanana.
Ki jajjaga attaruhu da albasa ki zuba a tukunya, ki saka timatir na leda da manja, gishiri da sinadaran dandano ki soya.
Sai ki zuba ruwa dai-dai yadda yawan kubewarki take, za ki fara zuba kubewarki da kika yanka, ki jefa kanwa ‘yar kadan ki rage wutar dan kubewar ta tafaso, sai ki juye wadda kika markada ki saka kifinki, bayan kin soya shi.
Idan kubewarki ki ta dahu za ki ga mai ya tsatsafo kuma za ta hade jikinta.
Za ki ci wannan miyar da tuwo, semo ko sakwara.