Miyatti Allah Na Da Kyakkyawar Fahimta Da Gwamnatin Kebbi

A halin yanzu muna tare da shugaban Miyatti Allah na makiyaya a reshen jihar Kebbi, ALHAJI MUHAMMADU DAN’ALI don tattauna wa da shi kan dangantar kungiyar da gwamnatin jihar Kebbi, da sauran bayanai da suka shhafi kungiyar wakilinmu  IBRAHIM MUHAMMAD ne ya zanta da shugaban kungiyar ga kuma yadda tattaunawar ta su ta kasance

Ranka ya dade za mu so mu ji irin ci gaba da gwamnatin jihar Kebbi ta samar wa ‘yan’uwa Fulani makiyaya a jihar Kebbi wadda ka ke jagoranta.

A’uzubillahi minasshaidanir rajim, bismillahirrahmanir rahim, wasallalahu ala nabiyul karim, amma ba’ad, hakika mai girma gwamnan jihar Kebbi, sanata Abubakar Atiku Bagudu kuma Matawallen Gwandu, in aka duba duka bangarori ya yi wa al’ umma aiki, ba mu makiyaya kawai ba, duka sauran al’ummar jihar Kebbi, mun ga ci gaba daban-daban da aka samu a karkashin jagorancinsa na shekara uku, kuma muna yi wa Allah godiya da ya ba mu shi a matsayin gwamna wanda ke kula da tausayi na talakawansa da Allah ya ba shi, mun zama shekarun baya idan wani lamari ya taso na  makiyaya sai mu ga gwamnati ba ta nuna kulawa ko kuma bukata, amma shi da kansa yake kiranmu a lokaci zuwa lokaci yana tambayarmu shin ku kuwa menene matsalolinku? Ba ku da matsaloli ne da ba ku zuwa kuna fada min? Muna cewa Your Edcellency ai ka san matsalolinmu, matsalolin makiyaya ba su wuce wuraren zama ba, wuraren shan ruwa, hanyoyin da za su bi, kuma a hakikanin gaskiya, ya dukufa wajen yin wadannan abubuwan da muka ambata har ma da dadi, don yanzu yana kokarin ya kirkiro mana  kamfuna na sarrafa madara wanda za a kafa su yankuna daban-daban na jihar Kebbi, domin a rage yawon talla da matan Fulani suke yi, suna gararanba a cikin garuruwa da kasuwanni, a takaice wannan shimfidar ke nan.

 

To ranka ya dade, kana ganin me ya ba gwamnan jihar Kebbi sha’awa, har ya yi tunanin saukakawa al’ummar Fulanin jihar Kebbi da wannan shiri da ya dakko?

To hakika ya iske mu cikin matsaloli da ukuba daban-daban, to idan ya ce zai gyara mana wuraren zamanmu ya kawo mana ruwa da makarantun yin boko da masallatai da asibitoci kuma ya zama bai koyama matan mu sana’o’i da matasanmu ba, to kamar an yi tuya ne an manta da albasa, amma idan ga wurin zama mai kyau kamar kuma bisa ga tsari sannan kuma ga sana’ar yi, ko kuma sana’ar da aka gada kaka da kakanni ta harkar tatsar nono da madara ya zama an sawwaka abin an kawo  na’urorin zamani yadda za a kyautata wannan madara, na farko dai za a samar da ita mai tsafta kuma za a samar da ita mai lafiya, kuma mutane za su sha ta za su yi murnar shan ta, irin yadda za a sarrafata, za a sarrafata har ma za a iya yin madara irin wadda ake yin shayi da ita, duka dai ya kawo wannan kamfani yanzu haka suna nan suna kokari yadda za su yi su fara kafa masana’anta ta gwaji a nan dai Birnin Kebbi, kafin su kara gaba.

To a karshe ita ma matar gwamna, ita ma tana koyi da yadda mijinta yake, tana shiga ruga ba dare ba rana domin ta inganta tarbiyyar matan Fulani wato su daina zuwa tallace-tallace domin samun ingancin tarbiyyar ‘ya ‘yan Fulani domin samun tarbiyya mai kyau da kuma irin abin da ake gani cewa tarbiyyar Bafulatani bai kamata a ce matan Fulani suna yawo a layuka ba.

 

Ya ka kalli yadda matar gwamna ita ma ta rungumi yadda mijinta shi ma yake yi?

To a hakikanin gaskiya mu abin ya burge mu matuka, kamar kokarin sai mu ga da matar da shi waye ya fi kokari ga Fulani, saboda duk da dai shi ne sama, shi ne ke ba ta gudummawa, shi ke ba ta izini, shi ke ba ta dama, take mana wadannan abubuwa na amfani ta ziyarci makiyaya ta kai masu kayan masarufi ta ziyarcesu ta yi hulda da su ta tambaye su matsaloli a rubuto ta kawo ma shi mai girma gwamna kuma ya je a aiwatar, ta ta yi mana abubuwa, kusan yanzu ta yi cobering din jihar Kebbi gaba daya. Kowacce karamar hukuma takan je ta zabi kamar ruga uku ko hudu biyar ta ziyarce su har can a ruga ta zauna da su ta sauraresu musamman mata da yara da ya ke tana da wani shiri na wata kungiya ta ta da ake ce ma malfai, wato mai kula da harkar taimakon almajirai, marasa galihu da kuma ainihin mata, so wannan ta ba Miyatti Allah wani kaso daga ciki, ta ba mu wani babbar kulawa daga cikin wannan kungiya, kuma muna jin dadin haka Allah ya saka mata da alheri, Allah ya kara taimakonta.

 

Exit mobile version