Wata mata mai niyyar zuwa aikin Hajjin bana daga Jihar Nasarawa, Hajiya Aisha Yahya Sule, ta rasu a shirye-shiryen da take yi na sauke farali a bana.
Bayan da ta kammala gwajin lafiya da allurar rigakafin da ake yi ga maniyyatan, ne wata mota ta buge ta a lokacin da take kokarin tsallaka titi.
- Matashi Ya Shiga Hannu Kan Yi Wa ‘Yar Shekara 4 Fyade A Nasarawa
- Tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa Ya Kubuta Bayan Biyan 4m
Hukumar Alhazai ta Jihar Nassarawa, karkashin shugabancin Malam Idris Ahmad Almakura, ta bayyana kaÉ—uwa da alhini bisa rasuwar maniyyaciyar.
Almakura ya ce rasuwar Aisha wani rashi ne mai ban tsoro da bakin ciki.
A sanarwar da ya fitar ga manema labarai a garin Lafiya, Almakura, ya yi wa iyali da ‘yan uwan marigayiyar ta’aziyya tare da addu’ar Allah ya yi mata rahama.
Tuni dai aka yi jana’izar marigayiyar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.