Wannan hoto ne mai taken “Yaron Kasar Sin”. A ranar 28 ga watan Agustan shekarar 1937, sojojin kasar Japan suka kai harin bom wata tashar jiragen kasa da ke birnin Shanghai, wanda ya halaka fararen hula na kasar Sin da dama. An dai dauki hoton ne bayan harin, inda wani yaron da bai kai shekara daya da haihuwa ba yake kuka a burbushin gini.
A kwanakin baya, na kalli wani fim mai taken “Dead to Rights”, wanda yanzu haka ke samun matukar farin jini a gidajen sinima na kasar Sin. Fim din ya bayyana duhun da al’ummar Sinawa suka shiga sakamakon wannan yakin da maharan Japan suka tayar, da ma yadda suka tashi tsaye don yakar maharan. A watan Disamban shekarar 1937, sojojin Japan suka mamaye birnin Nanjing na kasar Sin, inda suka shafe tsawon makwanni shida suna yi wa fararen hula sama da dubu 300 na birnin kisan kiyashi. Fim din wanda aka yi amfani da ingantattun shaidun hotuna na ta’asar yakin da Japanawa suka aikata a lokacin kisan kiyashin Nanjing, ya ba da labarin wani rukunin fararen hula na kasar Sin da suka nemi mafaka a wani dakin daukar hoto a birnin Nanjing, a wani yunkuri na neman tsira da rayukansu hajaran-majaran. Sai dai sojojin Japan sun tilasta musu taimaka wa wani mai daukar hoto na sojan Japan wanke hotuna, amma kwatsam suka gano yadda hotunan ke dauke da shaidun munanan ta’asar da sojojin Japan suka tafka a sassan birnin. Bisa kudirinsu na tona asirin abin da ya faru, sai suka boye hotunan tare da jefa rayuwarsu cikin hadari wajen bayyana su ga duniya.
- Ba Gaskiya Ba Ne Rahoton Da Ke Cewa An Yi Sulhu Da Bello Turji – Guyawa Isa
- Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas
A yayin da muke kallon fim din a gidan sinima, masu kallo da yawa sun yi kuka, labarin da fim ya nuna yana da matukar ban tausayi da bata rai, sai dai aihinin abin da ya faru a tarihi har ya fi shi muni.
Fim din ya bakanta ran ‘yan siyasa da masu ziyartar shafukan yanar gizo da dama na kasar Japan, har ma sun musanta tarihinsu na kisan kiyashin, suna zargin cewa, wai “kasar Sin na amfani da fim don yayata ra’ayoyin kin jinin kasar Japan.” Lallai akwai tarin shaidu game da miyagun laifukan da sojojin kasar Japan suka aikata a yakin da suka tayar a kan kasar Sin, amma duk da haka, gwamnatin kasar Japan ba ta taba yarda da laifuffukan da ta aikata ba, kuma masu tsattsauran ra’ayi na kasar sun yi iyakar kokarinsu wajen jirkitawa da boye tarihin kutsen da suka yi wa Sin, don neman gurgunta fahimtar kasashen duniya game da tarihin.
Akwai dimbin fina-finai masu alaka da yakin duniya na biyu, to, amma me ya sa Jamusawa ba su damu da fina-finai irinsu Schindler’s List ba? Sa’an nan me ya sa masu kallon fina-finan ba su ji haushin kasar Jamus ba? Amsa ita ce sabo da gwamnatin kasar Jamus da al’ummar kasar sun yi matukar tuba game da laifukan da kasar ta aikata a lokacin yakin duniya na biyu, tare da neman gafara wurin wadanda suka yi musu laifukan, don haka ma kasa da kasa suka yi musu afuwa. Amma yadda Japan ke kin yarda da laifukanta tare da neman gurbata gaskiyar abubuwan da suka faru, ya kara wa al’ummar kasashen da ta aikata wa laifukan radadin abun da ya faru, kuma hakan ya kasance gargadi ga kasa da kasa.
A cikin fim din “Dead to Rights”, an ce, “Mu tuna da jinin da aka zubar a yakin, don mu kiyaye hasken da muke da shi yanzu.” Abin haka yake, yau mun waiwayi abubuwan da suka faru a tarihi, ba don neman ci gaba da kiyaya da juna ba, a maimakon hakan, muna son kira ga al’ummomin duniya da su tsaya tsayin daka a kan kiyaye zaman lafiya da magance yaki a tsakaninsu.
Yakin duniya na biyu babbar masifa ce ga dan Adam, kuma irin ra’ayi da ake rike da shi game da tarihin yakin, ya zama wata jarrabawa ga dan Adam. A bana ake cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka samu nasarar yaki da mahara Japanawa, da ma kasashen duniya suka samu nasarar yaki da ‘yan Fascist, kuma rike ra’ayi madaidaici game da tarihin yakin duniya na biyu a daidai wannan lokaci, yana da ma’ana ta musamman ga kasashen duniya, musamman a yayin da ake fuskantar rikice-rikice da zaman dar dar a duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp