Jagororin da suka jagoranci kifar da gwamnatin demukuradiyya a Jamhuriyyar Nijar, sun yi barazanar hallaka shugaba Mohammed Bazoum muddin kasashen da ke makwafta da su ko kuma ECOWAS ta afka musu da karfin soja.
LEADERSHIP ta labarto cewa ECOWAS a ranar Alhamis ta umarci dakarunta na ko-ta-kwana da su kimtsa su ja damarar fara yaki domin dawo da mulkin demukuradiyya a jamhuriyyar Nijar.
- Nijar: Sojoji Sun Kame Manyan ‘Yan Siyasa Da Ministocin Bazoum
- ECOWAS Na Duba Yiwuwar Amfani Da Karfin Soja Wajen Mayar Da Bazoum Kujera
Rahoton AP ya labarto cewa wani jami’in sojan kasashen yamma, ya shaida bisa sharadin ba za a bayyana sunansa ba cewa, wakilan dakarun Junta sun tabbatar wa mataimakin sakataren wajen Amurka Victoria Nulanda irin barazanar da shugaba Bayou ke fuskanta a lokacin da ta ziyarci kasar a ciki makon nan.
Kazalika, wani jami’in Amurka shi ma ya tabbatar da wannan, yayin da ke magana bisa neman a sakaye sunansa saboda ba shi ne ke da ikon magana da ‘yan jarida ba.
Barazanar daga dukkanin bangarorin ya haifar da zaman dar-dar, sai dai an yi fatan dukkaninsu ba za su kai ga aiwatar da kalaman nasu ba, kamar yadda tsohon jami’in ofishin jakadancin Amurka, Aneliese Bernard ya shaida, wanda shi din masani ne kan harkokin Afrika.
LEADERSHIP ta labarto cewa ECOWAS ta gudanar da wani taro a ranar Alhamis a Abuja dangane da matakinta na gaba da za ta dauka kan halin da ake ciki a Nijar.
Da yake magana bayan kammala ganawar tasu, shugaban hukumar ECOWAS, Omar Alieu Touray, ya ce, sun bi matakan lalama da salama amma hakarsu bata cimma ruwa ba wajen maido da shugaba Bazoum kan mulkinsa, don haka ne suka cimma matsayar umartar sojojinsu na ko-ta-kwana da su shirya damarar yaki.
Ya kuma daura laifin dukkanin wani kunci da takunkumin da aka kakaba wa Nijar ya janyo wa jama’an kasar, ya kuma ce, matsayar da suka cimma zai zama hadin guiwa ne.