ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Muhammadu Sa’ad Abubakar III: Sarkin Da Ya Dace Da Kowane Zamani

by Azu Ishiekwene
2 months ago

A ranar Talata shekaru biyar da na rubuta wa Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, yabo wanda a lokacin yana da shekaru 65.

Mu’amalarmu ta faro ne bayan naɗa shi Sarkin Musulmi, biyo bayan rasuwar ɗan uwansa, Muhammadu Maccido, a hatsarin jirgin sama a shekarar 2006, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 93.

Baya ɗan uwansa, Birgediya Abubakar (yadda ake kiransa a lokacin) ya kuma rasa ɗan uwansa, Sanata Badamasi Maccido, a lokacin wannan hatsarin.

ADVERTISEMENT

Wannan al’amari ya zo ba zato ba zo tsammani. A ranar Litinin, 24 ga watan Agusta, Sarkin Musulmi Abubakar III ya cika shekaru 70 a duniya.

Har ila yau zai cika shekara 20 a kan karagar mulki a ranar 2 ga watan Nuwamba. Sai dai ba abun mamaki ne ba yadda shekaru biyar da suka gabata na mulkinsa suka bayyana abubuwa da dama game da shi da kuma Masarautar Sakkwato.

LABARAI MASU NASABA

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

Misali, kwanaki biyu bayan cikarsa shekaru 65 a shekarar 2021, Sarkin Musulmi ya bayyana a bainar jama’a inda ya bayyana cewa abubuwa ba su inganta ba, kuma shugabannin addinai suna da alhakin faɗa wa gwamnati gaskiya kan yadda za a ingata rayuwar al’umma.

Yana Yin Al’amuransa Kai-tsaye

Bai tsaya a nan ba. Ya ce duk wanda ya tunzura mutane suka haifar da tashin hankali, ko shugabannin addini ne, ko sarakunan gargajiya ko ‘yan siyasa, ya kamata doka ta hukunta su.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da Jihar Filato ke fama da rikicin ƙabilanci, yayin da rikice-rikicen ɗaukar fansa suka yi ƙamari a jihar.

Ba mutum ba ne mai ɓoye kalamansa ba. Lokacin da mayaƙan Boko Haram ko ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ita suke kai wa jama’a hare-hare, kisa, fyaɗe da lalata dukiya da sunan ɗaukaka kalmar Allah, suna iƙirarin cewa idan suka mutu, ‘yan mata na jiran su a Aljanna, da yawan shugabannin addini sun kame bakinsu tare da yin shiru. Amma Sarkin Musulmi Abubakar III bai yi shiru da bakinsa ba.

Yana jan hankalin irin waɗannan ‘yan ta’adda cikin harshe da kalamai masu sauƙin fahimta, kalaman da ya taɓa maimaitawa a gabana cewa: “Kai-tsaye za su tafi Jahannama!”

“Babu wanda zai kashe mutum da sunan Allah sannan ya yi tsammanin samun mafaka a Aljanna. Fassarar Suratul Ma’idah 5:78-79,

“Lā yatanāhawna ‘an munkarin fa‘alūhu,” ta nuna ƙarara waɗanda ba sa hana juna, ko dakatar da juna, ko yi wa juna gargaɗi kan laifin da suka aikata.

Gwarzo Wajen Haɗa Kan Addinai

Shekara guda bayan cikarsa shekaru 65 a duniya, ya fuskanci ƙalubale a matsayinsa na jagoran haɗa kan addinai lokacin da aka kashe Deborah Samuel, ɗalibai a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, bisa zargin ɓatanci ga Fiyayyen Hallita Annabi Muhammad (S.A.W).

Majalisar Masarautar Sakkwato ta yi Allah-wadai da kisan ɗalibar tare da buƙatar a gurfanar da waɗanda ake zargi da hannu a lamarin a gaban doka.

Wannan mataki ya kasance abin ban mamaki, ko da yake hukumomi a ƙarƙashin Gwamnatin Waziri Tambuwal sun yi biris da shawarar, sannan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, bayan ya yi Allah-wadai da lamarin a wani sakon Twitter, ba a ɗauki lokaci ba ya goge saƙon.

Abubakar III ya yi ƙoƙarin haɗa kan addinai tare da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai sama da duk wani jagoran addinin Musulunci da na sani tsawon lokaci.

A matsayinsa na mataimakin shugaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Addinai ta Nijeriya, ya yi aiki ba dare ba rana, yana amfani da alaƙar da yake da ita da majalisun addinai a faɗin duniya, wajen gyara alaƙar da ta lalace da kuma daƙile tasirin rashin haƙuri a tsakanin addinai da tsattsauran ra’ayi.

Mai Rajin Gyara Halayyar Al’umma

Sarkin Musulmi Abubakar III, mutum ne mai matsakaicin ra’ayi kuma mai fafutukar gyara al’umma, lamarin da ke bai wa ɗimbin jama’a mamaki, ganin cewa ya fito daga Sakkwato.

Ya sha yin magana kan muhimmancin ilimi ga yara; namiji ko mace – yana tunatar da wawaye da masu goyon bayansu waɗanda suke raina ilimi da sunan Musulunci cewa an kafa Daular Khalifanci ne bisa ilimi da wayewa.

Kuma mutum ne mai gaskiya. Yawancin tarihin da aka rubuta game da Daular Khalifanci suna kallon wani ɓangare ne na Nana Asma’u, ƙanwar mahaifin Sultan Mohammed Bello, a littafin Fola Fagbule da Feyi Fawehinmi mai suna Formations: The Making of Nigeria from Jihad to Amalgamation, tana magana da harsuna huɗu.

Sarkin Musulmi Abubakar ya yi magana kan alaƙar da ke tsakanin ƙaruwar rashin tsaro, talauci, yunwa da kuma ware wasu daga cikin al’umma, inda a wani lokaci ya ce: “Yunwa ba ta san addini ba,” inda ya ƙalubalanci gwamnati da ta magance hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa, tare da daina kawo uzuri.

A lokacin da gwamnatin Buhari ta dinga yin kunnen uwar shegu da umarnin kotuna, ciki har da umarnin sakin ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore da aka tsare, Sarkin Musulmi ya bayyana a bainar jama’a cewa rashin bin umarnin kotu “hanya ce ta haifar da ruɗani da tashin hankali.”

Ya faɗi hakan ne a taron majalisar haɗin kan addinai da aka gudanar a Abuja, wajen da Buhari yake da tasiri a wancan lokacin.

Sauye-sauyen Diflomasiyya

Juyin mulkin da aka yi a Nijar a shekarar 2023 ya kasance yanayi mai sarƙaƙiya ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda a lokacin ba ta daɗe da rantsar da ita ba.

Bayan tsauraran matakan da Nijeriya da ECOWAS suka ɗauka sun gaza haifar da sakamako da ake so, gwamnatin Nijeriya ta tura wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar, wadda Sarkin Musulmi ke cikinta, domin nemo hanyoyin da shugabanni da jami’an diflomasiyya suka kasa samu.

Wannan ya nuna irin ƙarfi da tsarin shawo kan al’amura ta hanyar diflomasiyya da lallashi na iya warware matsala a wasu lokuta inda amfani da ƙarfi ya gaza.

Ko da yake Nijar, Mali da Burkina Faso sun ci gaba da kafa ƙungiyar da za ta ke jagorantar al’amuransu, wato (AES), ta zauna da kwamitin da Janar Abubakar ya jagoranta wanda hakan ya hana rikicin yin ƙamari a yankin Sahel.

Za A Ƙetare Koguna Da Yawa

Ɗaya daga cikin abubuwan da Sarkin Musulmi zai iya yin nadama a kansu yayin da yake cika shekaru 70 shi ne yadda tashe-tashen hankulan ‘yan tada ƙayar baya suka ƙafu matuƙa a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Borno, da ke Arewa maso Gabas, har yanzu ita ce yankin da lamarin ya fi ƙamari, amma ayyukan Lakurawa a Kebbi da Sakkwato suna nuna su a matsayin sabbin wuraren da masu iƙirarin jihadi ke amfani da su a Arewa maso Yamma.

Abin da Sarkin Musulmi yake kallo daga nesa yake kuma gargaɗi a kansa lokacin da yake da shekaru 65, yanzu ya iso har ƙofar Daular Khalifanci, a matsayin barazana daga yankin Sahel wanda ya tsallake iyakokin ƙasa.

Ayyukansa sun zama ma’auni da kuma muryar kawo daidaito. Duniya ba wai kawai tana sauraro ba ne, tana mayar da hankali kan yadda abubuwa ke tafiya

An taɓa gabatar da sunan Sarkin Musulmi da ɗan uwansa da Cardinal John Onaiyekan, a matsayin waɗanda ke ƙoƙarin haɗa kan addinai domin ba su lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel.

Gabatar da sunayensu kaɗai ya kasance tamkar samun nasara ne, domin ya aike da saƙo ƙarara cewa irin gagarumin aikin da waɗannan mutane biyu suke yi bai tsaya wajen gani da ido ba kuma ba a bar shi a iya yabo ba.

Dukkaninsu sun taɓa samun lambar yabo ta LEADERSHIP Persons of the Year 2012, lamarin da ya tabbatar da cewa waɗannan jagororin sun cancanci girmamawa, a gida da kuma ƙasashen waje.

Ƙalubale

Sai dai, ta fuskanci ƙalubale cikin ‘yan shekarun da suka gabata. Shekaru biyu da suka wuce, makomar Masarautar Sakkwato ta faɗa wani hali. Gwamna Ahmed Aliyu ya yi wasu sauye-sauye a dokar ƙananan hukumomi da masarautun gargajiya ta Sakkwato, waɗanda suka rage ikon Majalisar Masarautar Sakkwato na naɗa hakimai da dagatai.

A ƙarƙashin waɗannan sauye-sauyen da aka yi, waɗanda aka dakatar yanzu, majalisar za ta iya ba da shawarar sunaye waɗanda za a naɗa kawai, amma ba ta ikon naɗa su ba.

Duk da irin tanade-tanade da dokar ta yi, wannan na zuwa ne shekaru biyar bayan gwamnatin Jihar Kano ta rage ƙarfin ikon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi, lamarin da ya zama cin mutunci a idon wasu game da ikon masarautar da ke da ƙarfi a Arewa.

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta so ta durƙusar da Masarautar Sakkwato, lamarin da ya haifar da saɓani a cikin tsarin masarautun gargajiya na Nijeriya, mutum zai iya zama jagoran miliyoyin mutane, ya samu karɓuwa a duniya kuma shugabannin ƙasashe su riƙa neman ganinsa, amma kujerarsa ta kasance ƙarƙashin dokokin jiha, bisa yadda gwamna ya ga dama.

Soja Kuma Mutumin Kirki

Yayin da Sarkin Musulmi ke cika shekaru 70, na yi ta ƙoƙarin fahimtar abin da ka iya kasancewa a bayan wannan tafiya tasa mai cike da sirri.

Ya kasance ɗaya daga cikin mambobin 18th Regular Combatant Course na Kwalejin Tsaro ta Nijeriya, NDA, (ajisu ɗaya da tsohon Shugaban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Azubuike Ihejirika), kuma shi ne soja na farko da ya taɓa yin sauratar Sarkin Musulmi.

Yawan ayyukan da ya gudanar a aikin soji na faɗa da waɗanda ba na faɗa ba, musamman yadda aka tura shi Pakistan a matsayin mai ba da shawara kan harkokin tsaro, tare da kasancewarsa jakada mai kula da Iran, Iraƙi, Afghanistan, Saudiyya da kuma ƙasashen Gulf, wataƙila waɗannan abubuwa sun taimaka wajen tsara yadda yake kallon duniya.

Idan za a daidaita kalaman Kipling, a lokacin da yake da shekaru 70 kuma ya kusa cika shekaru 20 a kan karagar mulki, Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya samu nasarori da kuma koma-baya, kuma ya ɗauki dukkaninsu tamkar abubuwa masu rikitarwa da bai kamata su ruɗe shi ba.

Allah Ya tsawaita rayuwarka, Ya kuma tsawaita mulkinka cikin ƙoshin lafiya!

Ishiekwene shi ne Babban Editan LEADERSHIP, kuma marubucin littafin Writing for Media and Monetising it

Azu Ishiekwene
+ postsBio
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Su Wa Ke Fatattakar Obi Da Kwankwaso?
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya

MASU ALAKA

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya
Rahotonni

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

October 20, 2026
Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya
Rahotonni

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

October 13, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC
Rahotonni

Jam’iyyu Da Ƴan Takara Sun Yi Wa INEC Bore Kan Cire Sunayensu Daga Takara

October 12, 2026
Next Post
Zamfara 2027:Yadda Dauda Lawal Ya Baza Ayyukan Raya Kasa A Sassan Jihar

Zamfara 2027:Yadda Dauda Lawal Ya Baza Ayyukan Raya Kasa A Sassan Jihar

LABARAI MASU NASABA

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

Sin: Dole Ne Gyaran Kwamitin Sulhu Ya Kunshi Canza Karfin Wakilcin Kasashe Masu Wadata Fiye Da Kima

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.