| A |
sassa da dama na fadin kasar nan, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a farkon makon da ya gabata, wanda hakan ya sa aka samu saukin tsananin zafin da ake fama da shi.
Rashin wutar lantarki daga tashoshin samar da wutar lantarki ya sa lamarin ya yi matukar kamari.
Matsakaicin yanayin zafi na rana a cikin watan Maris ya tashi daga digiri 33 zuwa digiri 38 a Legas da Abuja.
Ya zama wajibi a sanya gidan wutar lantarkin Nijeriya cikin kasashe masu tasowa da ke fuskantar matsalar wutar lantarki. Babu wani abu mai tabbas da ya wuce sanarwar katsewar wutar lantarki, wanda ya bar kasuwanci da gidaje wajen neman hanyoyin da za su sama wa kansu wutar ta hanyar kashe makudan kudaden da bai kamata su kashe ba, babu gaira babu dalili.
Wane Alkawari Tinubu Ya Yi?
A lokacin yakin neman zabensa na 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, idan bai gyara matsalar wutar lantarki ba, bai kamata a sake zaben sa a karo na biyu ba. Don haka, dole ne ya yi nadama a yanzu.
Tun farkon gwamnatinsa a watan Mayu 2023, an samu katsewar wutar lantarki da dama, wanda adadin da aka bayyana a cikin shekarar 2024 ya kai sau kusan 12. Tun kafin katsewar ta yi yawa, aka ci gaba da fuskantar matsalar wuta. An danganta matsalar da raunin da ake da shi ta bangaren fasaha da kuma tsarin gudanarwa. Amma akwai abin da ake lura da shi na cewa: “Iya gwargwadon ganinka da abu, iya karancin fahimtarka da shi”.
Don haka, rashin dogaro da wutar lantarkin da fadar shugaban kasa ta ware kimanin naira biliyan 10 a shekarar 2025, da kuma karin naira biliyan 7 a shekarar 2026, don sanya sola mai amfani da hasken rana, wanda za ta taimaka wajen hana katsewar wutar lantarkin Nijeriya yadda ya kamata daga na’urar sadarwa ta kasa, wanda ke fama da matsalar tsufa ta layukan sadarwa da ke katsewa akai-akai, sakamakon zagon kasan da ake samu da rashin kulawa da kuma matsalar rashin daidaito daga mitoci.
Abin Dariyar A Kanmu Take
A shirye ’yan Nijeriya suke, su yi izgili da munanan cututtukan da suka jima suna fama da su, haka nan idan aka zo batun maganar rashin wutar lantarki, abubuwansu na da matukar daura kai. Idan da za su ga wayar wuta mafi hadari (High-tension cables) ta kasa-kasa, ba za su yi shakkar rataye kayan wankinsu a kai ba, saboda tabbacin da suke da shi na cewa, layukan wutar kawai a shimfide suke babu wutar lantarki a tare da su.
Na ga hoton bidiyo na wani maski da ake yi a kan sandar fitilun titina. Layukan babu wutar lantarki tsawon watanni, sannan kuma babu yiwuwar samun wutar.
Kyakkyawan fata da yakini dai, ya sake kunno kai tun a farkon gwamnatin Tinubu, a lokacin da labari ya kara tabbatar da cewa, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da ke fama da rikici a halin yanzu, ba wai kawai ya samar da wani tsari ba, har ma za a ba shi aikin tantance fitaccen bangaren wutar lantarki a Nijeriya. Na fahimci cewa, a cikin shirinsa, El-Rufai yana tattaunawa da Saudiyya kan yarjejeniyar zuba jarin dala biliyan 10, kafin ya samu kansa cikin mawuyacin hali.
Zuwan Adebayo
A haka Adebayo Adelabu ya dauki wannan aiki, aikin mai matukar wahala, yana mai cewa; ya gaza. Amma ba laifinsa ba ne, laifin shugaban kasa ne da ya nada shi da kuma majalisar dattawa ta wanke shi ko dai bisa la’akari da tarihinsa ko kuma bisa wani fata na fansa. Babu shakka, yana da hazaka, amma a bangaren wutar lantarki ya yi matukar gazawa, idan aka kwatanta shi ragowar hazikan mutane.
Mafi kyawun shekarunsa, shi ne lokacin da ya yi aiki a matsayin mai duba PWC. Ya kuma kasance Babban Darakta/CFO a bankin First Bank, sannan ya zama mataimakin gwamna a babban bankin kasar.
A al’ada, aikin banki da ya sani a wannan bangare ya kamata ya kasanc. Amma, kasancewar Nijeriya, an fi yin la’akari da tsari iri na rabo da kuma alakar siyasa, shi yasa abubuwan suka sha banban.
Sannan a shekarar 2023, Tinubu ya ba shi mukamin Ministan Wutar Lantarki, bayan yunkurin da ya yi na zama Gwamnan Jihar Oyo a Jam’iyyar Accord Party bai samu nasara ba.
Babu shakka, hakan ya kara dagula al’amura. Kazalika, za a fi tunawa da Adelabu, saboda raba rukunin biyan kudin wutar lantarki da ya yi, wanda ba lallai ba ne hakan ya nuna ingantattun ayyukansa.
Wannan ba shi ne yake nuna cewa, Adelabu ya gaza ko bai samu nasara a aikinsa ba, rashin shaidar da zai nuna ce matsalar. Mista Dan Kunle, wani masani kan harkokin makamashi, wanda ya san tarihin wannan fanni, ya shaida min cewa;
“Babu wanda ya dage cewa, sai ministan wutar lantarki ya samo kudin da za a gyara wutar lantarki, amma ya rage nasa ya samar da ingantaccen tsarin da zai taimaka wajen samar da yanayin da ya dace da kuma jawo hankalin masu ruwa da tsaki.”
Adelabu, kamar sauran magabatansa, yana gudanar da ma’aikatar wutar lantarki a 2026, ta hanyar amfani da littafin aiki na 1950 na Hukumar Lantarki ta Nijeriya (ECN). Duk da haka, ko da a lokacin, lokacin da kasar ke da mutane kusan miliyan 50, Birtaniya sun san cewa; wutar lantarki na da matukar amfani ga tattalin arziki. Domin samun ingantacciyar wutar lantarki mai dorewa, dole ne su ba da fifiko, ba kawai ga manyan cibiyoyin gudanarwa ba, har ma da wuraren da za su iya biya. Shi ya sa, alal misali, ana jigilar kwal daga Enugu zuwa tashar wutar lantarki ta Ijora a Legas.
Babu Taswirar Inda Aka Nufa
Adelabu ba shi da taswirar hanya, idan kuma yana da ita kashi hudu karkashin tsarin ECN take, taswirar hanya ce da babu inda za ta je. Matsalolin da tuntuni aka saba da su, su ne dai ke ci gaba da kasancewa: wadanda suka hada da karancin iskar gas, faduwar bishiyoyi, karancin kayan aiki, basussuka masu yawa da katsewar wutar lantarki akai-akai, wanda hakan ya sa ake iya samun mega wat 4,000 kacal, maimakon mega wat 13,000.
Yayin da Adelabu ke nade da hannuwansa tare da ‘yan Nijeriya, wutar lantarki kuma ta yi nata waje, bangaren ya nutse a karkashin kasa, inda aka biyo shi bashin kimanin naira tiriliyan 6 a karshen shekarar 2025, wanda hakan ya haifar da rashin biyan kudade ga kamfanonin rarrabawa da kuma samar da wutar lantarki. Wasu daga cikin matsalolin sun riga Adelabu, amma rashin iyawarsa ce ta dame su.
Duk da haka, har yanzu yana da babban buri, amma fa ba na ya gyara kuskuren da ya yi na tsawon shekara uku yana minista ba, sai don kawai ya zama Gwamnan Jihar Oyo.
Ko shakka babu, shi kansa ya san bai yi wani abin a zo a gani a wannan mukami da aka ba shi ba. Abin kunya a wajensa sosai, domin kuwa ba zai taba goge tarihin katsewar wutar lantarkin da aka yi ta samu a lokacinsa ba. Ma’ana, babu wani abu da zai nuna face yadda kasuwancin Nijeriya ya gudana da taimakon injinan wuta na Indiya da kuma sola mai amfani da hasken rana na Kasar Sin.
Misalai Daga Afirka
Masar, mai yawan al’umma miliyan 110, tana da damar samun wutar lantarki kashi 100 cikin 100 na duniya, wanda ke samun tallafi ta hanyar dogaro da iskar gas mai karfi (kashi 81) da habaka kananan hanyoyin ‘carbon’, kamar wutar lantarki.
Wannan yana tabbatar da cewa, al’umma na cikin wadata ta hanyar samun yadda suke so.
Afirka ta Kudu, tana samar da kashi 85 zuwa 90 a cikin 100 ga al’ummarta su kimanin miliyan 62, duk da tana fuskantar karancin wutar, sakamakon bashin Eskom da tsufan da kayan aikin suka yi da kuma rashin kula, duk da yawan jama’an da ake da su.
Ghana ta kai kashi 88 zuwa 89 cikin 100 da ke da mutane miliyan 34, birane suna samun kusan kashi 99 cikin dari, yayin da yankunan karkara kuma a kan dan samu matsala lokaci bayan lokaci.
Kasar Kenya na da kusan kashi 76 cikin 100, wadda ke da al’umma miliyan 56, inda ta yi fice a birane da kashi 97 na wutar lantarki. Wutar ba ta wadata a kauyuka ba, koda-yake ana sa ran samun wadatuwarta nan da 2030.
Idan aka kwatanta da kasashen da ke sama, kashi 57 cikin dari na ‘yan Nijeriya katsewar wutar lantarkin da ake samu yana shafar su kai tsaye, haka nan dauke wutar na shafar kashi 85 cikin dari ga matsalar mita da cin hanci da rashawa da sauran makamantansu.
Bayan kallon Adelabu a matsayin wanda ya kasa tsinana komai a shekaru biyu da suka gabata, ina yi masa fatan tafiya salin-alin, karkashin duhun da ya samu. Amma tun da ya dage cewa, ba zai tafi salin-alin ba, kuma ya kuduri aniyar ci gaba da zama, ina tunanin wani aiki ya nada da kansa domin ja shi Jihar Oyo, don ganin yadda zai mayar da darensu rana.















Discussion about this post