Gwamna Dauda Lawal ba wai ya tunkari shekarar 2027 ne kawai a matsayin dan siyasa da ke neman wata dama ta sake neman mulki ba. Yana tunkararta ne a matsayin gwamna mai ci, wanda zai iya gabatar da tarihin ayyukansa, kwarewarsa, hangen nesansa da ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa ga al’ummar jihar, domin su tantance shi.
Yayin da sannu a hankali Jihar Zamfara ta doshi kakar siyasar 2027, babu shakka batutuwan shugabanci, ci gaba, ci gaba da mulki da kuma makomar jihar za su kara daukar hankali.
Gwamna Dauda Lawal, tafiyarsa a siyasa da tarihin ayyukansa a ofis ne suka ba shi wani matsayi na musamman a idon al’ummar Zamfara.
Daya daga cikin manyan abubuwan da ke bai wa gwamna mai ci damar neman sake zabe su ne damar nuna wa jama’a abin da aka cimma a zahiri. Saboda haka, tattaunawar siyasar Gwamna Lawal ta 2027 na iya ta’allaka ne kan wata muhimmiyar tambaya: Shin me ya sauya a Zamfara, kuma me kuma za a iya cimmawa idan aka ci gaba da wannan gwamnati?
Jagoranci a karshe dai ya ta’allaka ne kan tasirin da ake samarwa. Hanyoyi, ilimi, kiwon lafiya, tsaro, noma, ababen more rayuwa, gyare-gyaren hukumomi, bunkasa jarin dan’Adam da samar da damar tattalin arziki ba wai kalaman siyasa ne kawai ba; su ne abubuwan da ke shafar rayuwar talakawa kai tsaye.
Saboda haka, hujjar da ta fi karfi da gwamnan zai iya gabatarwa ita ce tarihin ayyukan da ya yi, ta yadda jama’a za su iya kwatanta yadda Zamfara ta kasance a baya, yadda take a yau, da kuma yadda za ta iya kasancewa a gobe.
Ci Gaba Da Mulki A Matsayin Dabarun Samar Da Ci Gaba
Zamfara ba ta bukatar ta ci gaba da komawa daga tushe a duk lokacin da aka samu sabon yanayi. Ci gaba mai dorewa yana bukatar ci gaba da manufofi, daidaito da kuma isasshen lokaci domin kyawawan tsare-tsaren da aka shirya su samu damar habaka.
Wa’adi na biyu zai ba da damar karfafa gyare-gyaren da aka fara, kammala ayyukan da aka riga aka kaddamar, inganta hukumomi da kuma aiwatar da sabbin shirye-shirye bisa darussan da aka koya a wa’adin farko.
Sakon a bayyane yake, idan an riga an kafa ginshiki, to alhakin gaba shi ne a kara gina sama, ba wai a rushe abin da aka yi a sake farawa daga farko ba.
Kwarewar Da Ake Samu A Fannin Gudanar Da Mulki
Akwai bambanci tsakanin kamfen domin samun mulki da kuma ainihin gudanar da mulki. Wa’adin farko ya bai wa Gwamna Lawal damar fuskantar hakikanin yanayin mulki, rikicewar gudanar da harkokin gwamnati, bukatun jama’a, kalubalen da kananan hukumomi ke fuskanta, matsalolin tsaro, yadda ake tafiyar da karancin albarkatu, da kuma muhimmancin yanke shawarwari masu wahala.
Wannan kwarewa na iya zama wata babbar fa’ida gare shi yayin da ake tunkarar shekarar 2027. Ba zai bukaci ya roki al’ummar Zamfara da su damka makomar jihar ga wanda ba a gwada shi ba. Abin da zai nema shi ne su sake ba shi damar amfani da kwarewar da ya samu a wa’adin farko wajen gudanar da mulki yadda ya fi inganci.
Hangen Nesa Fiye Da 2027
Shugabannin siyasa mafiya jan hankali su ne wadanda ba sa mayar da hankali kan kamfen don zabe mai zuwa kawai, sai dai su gabatar da hangen nesa da ya wuce zaben.
Zamfara na bukatar wani tsari na dogon lokaci na ci gaba wanda zai magance manyan kalubalen da jihar ke fuskanta, tare da samar da damammaki ga matasanta.
Saboda haka, ya kamata a gabatar da zaben 2027 ba kawai a matsayin fafatawa don neman mukamin siyasa ba, amma a matsayin zabin alkiblar makomar Zamfara.
Zamfara wadda matasa za su iya gina sana’o’insu da ayyukansu. Ita ce wadda manoma za su iya noma su samu wadata. Kazalika Zamfara ita ce ’yan kasuwa za su iya bunkasa harkokinsu.
Sannan Zamfara ita ce jihar da yara za su samu damar samun ingantaccen ilimi. Bugu da kari Zamfara ita ce jihar da kowa zai iya samun ingantacciyar kiwon lafiya cikin sauki.
Zamfara ce ke biyan albashi, fansho da alawus-alawus a kan lokaci. Zamfara wadda hukumominta suka fi karfi, kuma ake amfani da dukiyar jama’a cikin gaskiya da rikon amana.
Sannan Zamfara ce zaman lafiya da tsaro suka zama tubalin samun ci gaba.
Yadda Aka Bunkasa Rayuwar Matasa
Watakila daya daga cikin manyan damammakin da ke gaban Gwamna Lawal a shekarar 2027 shi ne yawan matasan Jihar Zamfara.
Bai kamata a dauki matasa kawai a matsayin magoya bayan siyasa, taron kamfen ko kuma adadin masu jefa kuri’a ba. Ya kamata a dauke su a matsayin abokan tafiya wajen gudanar da mulki kuma masu gina makomar jihar.
Saboda haka, huldar gwamnati da matasa bai kamata ta tsaya kawai kan tattara magoya bayan siyasa ba. Ya kamata ta mayar da hankali kan ilimi, koyon sana’o’i, kasuwanci, samar da ayyukan yi, fasaha, noma, bunkasa shugabanci da kuma ba matasa damar taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da mulki.
Kungiyar siyasa da ta bai wa matasa damar taka rawa wajen tsara makomarsu, a dabi’ance za ta karfafa musu jin cewa su ma suna da hannu kuma suna da muhimmiyar rawa wajen makomar jihar.
Shugabanci Cikin Tawali’u Da Kula Da Hakkin Al’umma
Hanyar zuwa shekarar 2027 ba zai yiwu a ce babu suka, adawa ko tattaunawa masu wahala ba. Wannan shi ne yanayin dimokuradiyya. Sai dai, amsar da ta fi karfi ga suka ba haushi ba ce abin da ya fi muhimmanci shi ne aiki da kyakkyawan sakamako.
Kamfen da ya fi gamsarwa ba lallai ne ya kasance wanda ya fi daga murya ba. Shi ne kamfen da zai iya nuna nasarorin da aka samu a zahiri, amincewa da wuraren da har yanzu suke bukatar gyara, da kuma gabatar da ingantaccen tsari sahihi na makomar gaba.
Saboda haka, babban abin da zai fi karfafa damar Gwamna Dauda Lawal shi ne ayyukan da ya yi tare da hujjoji, hangen nesa da ya ginu kan kwarewa, da kuma buri da aka hada shi da bin hakki.
A Karshe Dai, Zabe Na Al’umma Ne
Al’ummar Zamfara ne za su yanke shawarar wanda suka yi imanin zai iya jagorantar jihar yadda ya kamata zuwa mataki na gaba. Amma yayin da tattaunawar siyasa ke fara samun karfi, Gwamna Dauda Lawal ya shiga wannan fafatawa da wasu muhimman abubuwa da duk wani gwamna mai ci zai so ya kasance da su:
Saboda haka, tambayar da ya kamata a yi yayin da ake tunkarar 2027 ba wai kawai a ce: “Wane ne yake son mulkin Zamfara ba. Ya kamata tambayar ta kasance: “Wane ne ya nuna kwarewa, nagarta, gogewa da hangen nesa da za su iya kai Zamfara zuwa mataki na gaba?”
Ga Gwamna Dauda Lawal da magoya bayansa kuwa, wannan ita ce damar da ke gabansu. Tunkarar 2027 bai kamata ta tsaya a burin lashe zabe kadai ba. Ya kamata ta kasance bayar da gamsasshiyar hujja ta ci gaba da mulki, karfafa abubuwan da aka fara, da shugabanci mai ma’ana, sannan a bar al’ummar Zamfara su yanke hukunci kan suke so.
Makomar Zamfara ta fi kowane mutum girma. Shugabanci amana ce. Kuma ma’aunin wannan amana shi ne abin da muka gina, abin da muka canza, da kuma abin da muka bari a baya domin al’ummomin da ba su zo duniya ba tukuna.














