ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Su Wa Ke Fatattakar Obi Da Kwankwaso?

by Azu Ishiekwene and Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
Obi

Tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, na ganin shi ne dan siyasar da aka fi yi masa wata gurguwar fahimta a Nijeriya.

Ana sanya ayoyin tambaya kan dalilin suka sa mutane ke ganin sauya-sauyensa daga jam’iyya zuwa jam’iyya (wanda ya kai kusan sau biyar a zabe uku) a matsayin rashin tabbas ko neman dama, maimakon a dauke shi a matsayin dabara ta kare kai domin maslahar jama’a.

An kuma kwatanta shi da Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, dangane da yawan sauya jam’iyya, inda aka tambaya ko ya dace a dauke su iri daya a siyasa.

ADVERTISEMENT

Haka kuma, an yi tambaya kan ko wa ke kokari ganin bayan Obi da sabon abokin siyasarsa, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma dalilan hakan, inda aka ce akwai yiwuwar amsoshi uku kan wannan batu.

Hannun Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Wanda ake fara zargin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

An zarge shi sawa’un ko dai gaskiya ne ko akasin haka da cewa yana da hannu a wahalhalun da da Peter Obi ke sha a siyasa.

Banda ficewar Obi ta farko daga jam’iyyar APGA zuwa PDP a 2014, an ɗora laifin sauya shekarsa sau uku daga cikin hudu na baya-bayan nan kan Tinubu.

A lokacin da Obi ya fice daga PDP zuwa Labour Party a 2022, saura watanni kusan tara kafin babban zabe, ya sauya matsayinsa daga dan takara na yau da kullum zuwa wani mai fafutuka mai karfi a siyasa.

Ya yi nasarar kayar da Tinubu a Jihar Legas, wadda ake dauka a matsayin sansaninsa, sannan ya mayar da zaben da ake tsammanin zai kasance tsakanin mutum biyu zuwa fafatawa ta mutum uku, inda shi ya zo na uku da kuri’u kusan miliyan shida.

Tun daga lokacin, an ce Tinubu ya fahimci darasin da ke cikin wannan rikici na siyasa, wato kada a raina karfin Obi a fagen siyasar Nijeriya.

Sanya rudani a siyasar Obi

Don kawo karshen abin da ake kira “tashin hankalin siyasar Obi,” an yi zargin cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi amfani da tasiri wajen raunana jam’iyyar Labour Party.

An kuma ce ya yada irin wannan tasiri zuwa sauran jam’iyyu, ciki har da PDP, domin hana Peter Obi ko wasu abokan hamayya samun mafaka ta siyasa.

Bisa wannan ra’ayi, an yi ikirarin cewa irin wannan dabaru na siyasa an cim ma su ne ta hanyar amfani da wakilai a fagen siyasa da kuma tasiri a tsarin shari’a, wanda hakan ya sa aka rage wa Obi damar motsi a fagen siyasa, har ma aka kwatanta yanayinsa da na wanda ke neman mafaka a siyasa.

Siyasar Rabiu Musa Kwankwaso an bayyana cewa ba ta sha wahala a matakin kasa kamar yadda wasu ke fuskanta ba.

A wani lokaci ma, har an fara tunanin zai shiga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda aka ce hakan ba lallai ne ya taba kasancewa da sauki ga Peter Obi ba, ko da a mafarki.

Har ma ganawar da Obi ya yi da Tinubu a birnin Vatican daga baya ta zama abin ce-ce-ku-ce, inda wasu suka fara hasashen wata yarjejeniya ce da ka iya shafar wata matsalar banki da ake alakantawa da shi.

Duk yadda aka juya batun, wadanda ke ganin Tinubu a matsayin tushen kowace matsala ta siyasa tare da kalaman wasu jami’an jam’iyyarsa da ake ganin ba su dace ba sun yi imanin cewa shi ne ke da alhakin raunana jam’iyyun adawa a Nijeriya.

Abubuwan da ke haddasa masa wahala

Akwai ra’ayi na biyu game da rashin daidaiton siyasar Peter Obi.

Masu wannan ra’ayi suna cewa, duk da abin da wasu ke dangantawa da tasirin Bola Ahmed Tinubu, to a gaskiya Obi ne da kansa ya jawo wa kansa halin da yake ciki yanzu.

A cewarsu, tsananin neman mafita da gaggawa wajen siyasa shi ne babban abokin gabarsa.

Wannan hujja ta kara fitowa fili musamman a makon da ya gabata, bayan Obi ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC zuwa NDC, jam’iyyar da aka kafa shekaru tara da suka wuce amma aka yi rajistarta kawai watanni uku da suka gabata.

Ko da bayan kalaman Peter Obi cewa zai iya sauya jam’iyya har sau 20 idan ya zama dole, hakan bai kawar da zargin da ake yi ba cewa shi ne babban matsalarsa.

Wata majiya daga jam’iyyar ADC ta ce a daren Litinin ta bayyana cewa a cikin watanni shida da ta yi aiki da Obi a matsayin mamban jam’iyya guda, ba ta taba ganin dan siyasa mai tsananin neman nasara kamar sa ba.

Majiyar ta ce Obi ba shi da hakuri yana jiran jam’iyyar ta yanke shawarar wanda zai zama dan takara, kuma ba ya iya boye rashin natsuwarsa kan batun.

Domin kwantar masa da hankali, an ba shi mukamin Sakataren Tsare-tsaren Jam’iyya na Kasa, wanda aka kwace daga tsohon shugaban hukumar kiyaye zirga-zirga, Osita Chidoka, aka kuma ba wa wanda Obi ya zaba, Chinedu Idigo.

Duk da haka, ana cewa har yanzu damuwar rasa babbar kujerar takara ta ci gaba da damunsa sosai.

ADC. Me ya canja?

A cikin watanni shida da Peter Obi ya shafe a cikin ADC), ba a ce ya ga wani sabon abu ba da bai iya gani daga waje ba tun shekara guda kafin ya yanke shawarar shiga jam’iyyar.

Abin da ake cewa yana biye da Obi ba wai kawai Bola Ahmed Tinubu da kuma zargin gaggawar siyasa ba ne kawai, har ma da tsoron shiga gasa mai karfi.

A cewar wannan ra’ayi, Obi yana son samun tikitin takara ne a saukake ba tare da gasa ko hamayya ba.

Duk da cewa shi da masu taimaka masa sun sha musanta wannan zargi sau da dama, masu wannan ra’ayi suna ganin hujjojin da ke akwai ba su goyi bayan musantawarsu ba.

Shekaru hudu da suka gabata, lokacin da Peter Obi ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa Labour Party, ya yi hakan ne kwanaki uku kafin zaben fidda gwani na PDP.

A lokacin da ya shiga Labour Party, bai bukaci yin gasa ba aka ba shi tikitin takara kai tsaye a matsayin dan takara na jam’iyyar.Amma a wannan karon, an ce lamarin zai bambanta sosai.

Idan ya zauna a cikin ADC na tsawon lokaci, zai iya fuskantar gasa kai tsaye a zaben fidda gwani (wanda ake kira “direct primaries”), wanda ke da matukar hadari ga dan siyasa da ba shi da ginshikin jam’iyya mai karfi a kasa.

Ko kuma zai iya shiga tattaunawa da sauran ‘yan takara domin a nada shi “dan takara na hadin kai (consensus candidate),” wanda shi ma ana ganin yana da nasa hadarin da ba zai iya jurewa ba.

Sai ya janye. A cikin (NDC), sabuwar mafakarsa, shi ne kamar yadda yake a Labour Party, shi ne babban jigo.

Bayan shekaru yana alfahari cewa ba zai taba zama mataimaki ko na biyu ba, Rabiu Musa Kwankwaso zai yi hakuri ya rungumi kasa, ya kuma gamsu da zama mai tallafawa kawai ba tare da wani babban matsayi ba.

Siddabarun Da Ke Tattare Da Akidar Kwankwaso

Me ya sauya tun lokacin da Kwankwaso ya ce a Chatham House cewa ba zai iya janyewa wa Peter Obi ba, har ma ya kara da cewa Obi ba dan takara ne mai karfi ba, sannan kuma Arewa ba za ta bashi kuri’a ba?

Kamar yadda ya yi a 2023 lokacin da ya yi amfani da jam’iyyar NNPP wajen tattara kuri’un Kano ga gwamnan da ya ba goyon baya, ana cewa wannan karon ma yana amfani da Obi ne don jawo kuri’un Ibo a Kano domin karfafa tushensa.

A takaice, “gara a zama sarki a Kano fiye da zama na uku a Abuja.”

Amma har yanzu hakan ba zai kasance mai sauki ba.

Tuni an ga wani bidiyo na shugaban jam’iyyar NDC a Kano, Usaini Mai Riga, wanda ke da maciji a wuyansa, yana yi wa duk wanda zai yi tunanin takarar shugabancin jam’iyyar kalma ta la’ana.

Saboda haka tambayar ba ita ce wa ke son ganin bayan Obi da Kwankwaso.

A zargi tsarin

Akwai kuma ra’ayi na uku da ya sha bamban: cewa ba daidai ba ne a zargi Peter Obi ko Rabiu Musa Kwankwaso da yawan sauya jam’iyya, domin a Nijeriya, ba kamar wasu kasashe ba ce, jam’iyyun siyasa ba sa bambanta da akida ko manufofi na gaske.

A maimakon haka, ana kallon jam’iyyun a matsayin kawai hanyoyin da ake amfani da su wajen neman mulki.

Ko wadanda suka soki tarihin sauya jam’iyyar Atiku Abubakar suna yawan yi wa Obi da Kwankwaso rangwame a wannan batu.

A cewarsu, ba don kansu suke shiga takara ba ne kawai, sai don su samu wurin tsayawa domin kokarin sauya kasar zuwa abin da suka fi so.

Wannan hujjar ba ta tsaya a nan ba. Tana nacewa cewa babu wani dan siyasa a ‘yan shekarun nan da hukumomi suka bi shi da tsanani da zargi kamar Peter Obi, duk da haka ba a taba samun wani babban abin zargi a kansa ba.

Masu binsa suna ganin sa a matsayin dan siyasa mai tsafta fiye da yadda su kansu za su iya kasancewa.

An bayyana wannan ra’ayi sosai a tattaunawa da wani masoyin Obi wanda ya ce ya san shi sosai tsawon shekaru hudu.

Sai dai martanina shi ne cewa siyasa ba ta da sauki ko tsafta kamar yadda ake tsammani, kuma ba fafatawa ba ce tsakanin mutane tsarkaka.

A cikin irin wannan zargin na matsin lamba da ake cewa ana yi wa Peter Obi, an ce ‘yan siyasa kadan ne a cikin shekaru 27 da suka gabata da aka gwada su da irin wannan tsananin “bin diddigi” kamar Atiku Abubakar, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, Natasha Akpoti, Nyesom Wike, tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ko kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Duk da haka, an ce kowannensu ya tsaya ya yi gwagwarmaya ya kare kansa a siyasance.

Saboda haka, ana ganin akwai lokacin da dole dan siyasa ya tsaya ya yi fafatawa kai tsaye maimakon gujewa matsin lamba.

A wannan ra’ayi, ana cewa Peter Obi ya zabi siyasar sauki da rashin tsauri.

Ko kuma wata fassara ta daban ita ce kamar yadda aka taba tunanin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, watakila ana dora masa nauyin halin da ba shi da shi.

Idan haka ne, to laifin ba na sa ba ne, illa na wadanda ke tsammanin abin da bai dace da halayensa ba.

Ishiekwene shi ne Babban Edita na jaridar LEADERSHIP, kuma marubucin littafin “Writing for Media and Monetising It”.

Obi
Azu Ishiekwene
+ posts Bio
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Muhammadu Sa’ad Abubakar III: Sarkin Da Ya Dace Da Kowane Zamani
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya
  • Azu Ishiekwene
    https://hausa.leadership.ng/author/azu-ishiekwene/
    Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya
Obi
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
’Yansanda Sun Tabbatar da Sace Ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa

’Yansanda Sun Tabbatar da Sace Ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.