Mukalar Talata: Shin Buhari Ya Gaza?

Aliyu Dahiru Aliyu dahiraliyualiyu@gmail.com                    +2349039128220 (Tes Kawai)

 

Abu Hamidil Gazzhali a cikin littafinsa “Ihya’u Ulumiddin” ya fadi mana cewa kada mu kuskure mu amincewa dan adam dari bisa dari. A mafi yawan lokaci, wanda muke dauka shi ne Musan da zai kubutar damu sai ya koma Fir’aunan da zai bautar damu.  Ba a amincewa zuciya, kamar yadda John Paul Sartre yake fada. Tun kafinsa kuwa, Alkur’ani ya gayamana cewa zuciya mai umarni ce da mummuna. Kana amincewa abinda take gayamaka to ka gama yawo. Kada ka taba yarda da zuciyarka don ka samu nasarar rayuwarka. Marcus Aurelius a cikin littafinsa “Meditation” yana umartarmu da mu tursasa zuciyarmu akan kada ta yarda mu ne akan gaba. Daga cikin nasara shi ne kada mu yarda da zugar magoya baya su kaimu inda bamu je ba. Daga manyan hijaban da suke katange mutum daga cimma hakikar ci gaba shi ne yarda da cewa ka kai wani matsayin da baka gwada ka gani zaka iya ba.

Tsari ne na dan adam cewa duk lokacin da aka nuna shi kadai ne mai gaskiya kuma ya aminta shi mai gaskiyar ne, to daga nan zai lalace ya zama mai karfa-karfa. Ta irin wannan masu burin adalci suke komawa azzalumai idan suka samu masu tsarkakesu. Saboda imanin da akai Buhari shi ne mai gaskiya kuma shi kadai zai iya gyara Nijeriya kuma ya yarda shi kadai ne mai gaskiyar, shi yasa gwamnatinsa ta lalace ba tare da an yi komai ba. Hatta cin hanci da rashawar da aka ce ana yaka shima ya tashi a banza tunda masu sa ido sun ce mulkin Buhari bai canjawa yaki da cin hanci zani ba.

Babu wani abin a yaba da zaka kalla ka gani a gwamnatin Buhari. Hatta tsaron da ake magana, duk da an samu sauki ta wata fuskar, amma masana lamarin sun nuna rigimar Shekau da Albarnawy ce ta janyo aka iya samun nasara akan Boko Haram ba wai karfin sojan Nijeriya a karkashin Buhari ba. A yanzu kam makiyaya masu kisa sun kashe sun kashe har mun gaji da lissafawa. Sace-sacen mutane da neman fansa ya zama ruwan dare. Maimakon kwato yan matan Chibok da akai alkawarin yi, yanzu sun sake hadawa da yan matan Dapchi.

Yunwa kam ba a magana. Talaka har ya saba da ci sau daya ko sau biyu a rana a Nijeriya. Maimakon neman suttura da tunanin ci gaba, wannan gwamnati ta sanyawa talaka tunanin abinci kawai da tsadar kayan masarufi. Tashin dala, tsadar man fetur da wahalarsa da rikicewar tattalin arziki duk sun hadu a mulkin “mai gaskiyar” da aka dauka duk tarin Nijeriya babu kamarsa. Kai sai ka dauka aikoshi Allah yayi da za a ce babu kamarsa! Ina karyar da aka yi mana cewa an kawo shinkafa ton dubu goma kuma ta zo bakin teku? Ko dai a bayan kunkuru aka daukota ai ya isa ta zo yanzu. Ina maganar cewa za a mai da man fetur naira 45 duk lita? Yanzu sama da 200 ake siyarwa kuma gwamnati na gani. Ina dalar da aka ce zata dawo tamkar naira daya? To a 180 aka karbeta kuma yanzu 360 ce.

Karin wata masifar kuma shi ne yadda masoyan Buhari idonsu ya rufe saboda borin kunya da nade tabarmar kunya da hauka. Da ka nuna kuskuren Buhari to shikenan za a fara zaginka. Kai sai ka dauka kundin kasa bai baka damar ka fadi ra’ayinka a mulkin dimokradiyya ba! Mu dukanmu mun so Buhari tamkar wani babanmu. Mun yi kwanan sallah da addu’o’i don samun nasararsa, amma mun gaji da wahalar da ake sha bayan gwamnatin ta kasa komai.

Ba burinmu ace Buhari ya kasa shugabancin kasar nan ba. Mu muka zabeshi a matakin farko. Ya kamata mu fadi masa gaskiyar abinda yake wakana domin babu lallai na kusa dashi su fadi masa halin da talaka yake ciki na kunci. Yanzu talakawa sun fara gajiya. Kamar yadda Buhari ya ce talakan Nijeriya bashi da hakuri, ba rashin hakurin bane, hakurin ne ya kare kawai. Mun gaji da gafara sa amma har yanzu bamu ga kaho ba. Yaushe talaka zai ga ribar gwamnatin da ta ce zata yayemasa damuwa cikin kankanin lokaci? Yaushe zai fara karbar tallafin da aka yi masa alkawari? Yaushe zai fara shan man fetur akan naira 45 din da aka yi masa alkawari?

 

Akan Yan Matan Dapchi

Abin da ya fara zuwar min bayan an sace ‘yan matan makarantar kwana ta Dapchi shi ne iyayensu. Ya iyayensu za su kasance? Ya suke iya kwana su yi bacci rabin idanu a bude? Ya su yaran suke ciki? Wani irin kukan bakin ciki iyayen zasu yi? Idan ya kasance Annabi Yakub idonsa zai yi fari saboda kukan bakin cikin batan dansa Annabi Yusuf, to ya zata kasance ga raunana irin iyayen yaran da aka sace? Lallai akwai damuwa! Akwai bakin ciki da hawaye. Wallahi gwara a ce sun mutu tun fari maimakon a ce sacesu akai. Mutuwa tafi saukin a yimata dangana fiye da bacewa ko sacewa. Akwai abokina da ya bata tun muna yara. Wallahi har yanzu abin yana damuna kuma naji kamar zai dawo mu ci gaba da wasan gare-gare ko busa balan-balan.

Lissafi ya fita daga bakin gwamnatin tarayya cewa an sace mata 110 da a yanzu ba a da tabbas din ina suka shiga. Kuma har lokacin da nake wannan rubutu babu wata kungiya da ta dauki alhakin sace ‘yan matan, duk da an fi zargin kungiyar Boko haram ce ta bangare Abu Mus’ab Albarnawy. Wannan yana zuwa bayan an gama rainawa iyayen yaran hankali wajen musa sacesu a matakin farko, cewa an gano su a mataki na biyu da kuma cewa ana tunanin tarwatsewa sukai ko kuma an shige dasu kan hanyar Jamhuriyyar Nijar. Yaushe za a dena yi mana wasa ko siyasa da rayuka? Rai ba abin wasa bane da har za a dinga yin wasarere ko siyasa dashi.

A wani gefen kuma, can aka gano tarayyar gwamnonin jam’iyyar APC suna kokarin tabbatar da cewa Buhari sai ya yi takara ko don sa samu shiga danshinsa. Wannan shima yana zuwa ne dai-dai lokacin da aka sace yan matan Dapchi! Abin kunyar a cikin gwamnonin akwai wanda a lokacin da aka sace yan matan Chibok har da shi ake balokokon sai tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya dawo da yan matan da Boko haram suka sace. Yanzu har ya manta! Duniya mai yayi. Yanzu ko a gabansa yan matan Dapchi basa nan tunda jam’iyyarsu ke mulki. A wancan lokacin mu muka bi shi a baya muna kabbarar kiran a dawo da yan matan Chibok, amma yanzu sai dai kuma wasu ba shi ba. Haka siyasa take canja mutane. Daga neman hakki zuwa danne hakki.

A yanzu dai duk wata siyasa a ajiye gefe guda. Buhari shi zai nemo mana yan matan nan kamar yadda muka kira Jonathan ya nemo mana wadancan. Babu wani lankwashe-lankwashe da za ai da zai hana mu kira gwamnatin tarayya ta nemo mana yan matan nan. Yadda jam’iyyar APC ta nemi waccan gwamnatin ta nemo yan matan Chibok, to haka zamu nemeta ta nemo mana yan matan Dapchi. Fatanmu Allah yasa su hada fuskokinsu da na iyayensu cikin gaggawa. Mu ci gaba da addu’o’i a guraren ibada domin nasarar samo yan matan nan. Kada mu siyasantar da lamarin nan. Gwamnati tayi aikinta kamar yadda muke tsammaninta.

Exit mobile version