Idris Aliyu Daudawa" />

Mummunan Hatsari Ne A Jijjiga Jarirai

Jarirai

Bincike ya nuna cewa kuka na daya daga cikin abubuwan da ke sa a jijjiga jarirai

Sama da jarirai 220 ne suka muka mutu a Burtaniya dalilin jijjiga su da aka yi a shekara 10 da suka wuce, a cewar wani bincike da kungiyar  NSPCC ta yi.

An yi bitar lamarin da ya faru da jarirai 1,253, inda kusan daya cikin shida na jariran ya nuna cewar ya samu rauni ne a kwakwalwarsa.

Kungiyar ta ce a ganinta, wadannan  alkaluma “somin tabi” ne.

An gudanar da shi wannan binciken ne a matsayin wani kamfe a yankin Yorkshire don wayar da kan iyaye su daina jijjiga jariransu.

Dakta Suzanne Smith, wata tsohuwar malamar jinya ce  a Leeds ta kafa shirin kuma ta ce: “Na ga mummunan tasirin da jijjiga jarirai ke yi a asibitoci- inda jarirai suka rika mutuwa ko kuma su kamu da munanan cututtuka da kan iya haifar da nakasa, don haka dole ne mu tashi tsaye mu hana hakan na cigaba da faruwa.”

Joanne Peacock ta ce tana alhinin rashin samun rayuwar da ya kamata a ce danta na yi

Dan Joanne Peacock, mai suna Charlie ya zama galhanga kuma ya makance bayan da mahaifinsa ya jijjiga shi a gidansu da ke Huddersfield lokacin yana dan wata hudu.

“Na fito daga wanka na samu Charlie ya sauya launi, kamar ba shi da rai, ba ya numfashi a hannun mahaifinsa wanda kuma bai yi mani wani bayani ba.

“Ba mu yi tunanin za mu kai asibiti da ransa ba.

“Sun gaya mana cewar mu yi shirin samun labari mai wanda baya da dadi nan gaba, bayannan kuma raunin da ya samu daidai yake da a ce ya same shi a hatsarin mota ne, saboda an jijjiga shi da karfin gaske.”

An tsare tsohon mijin nata tsawon shekara 4 a  cikin shekarar 2009 bayan da  ya amsa cewar ya aikata  shi laifin da har ya yi ma  jaririn rauni.

Ta ce yanzu Charlie, mai shekara 12 ya girma kuma ya zama yaro mai kawo wa iyalinsu farin ciki amma ba komai yake iya yi ba kuma har zuwa karshen rayuwarsa, za a rika ba shi kulawa ta musamman.

An yi matukar jijjiga Charlie da har likitoci sun cire rai  zai rayu,  yanzu Joanne Peacock ta zama mai wayar da kan mutane ce akan illolin jijjiga jarirai.

“Abu mafi muhimmanci  ne a gare ni dangane da abin da ya samu Charlie shi ne rage yawan jariran da irin haka ke faruwa su,” a cewarta.

Kamfe din ICON na nufin wayar da kan iyaye kan illolin jijjiga jarirai kafin da kuma bayan haihuwarsu

John McMullan, wani kwararren likitan kwakwalwar yar ne  a asibitin yara na Sheffield ya ce jijjiga jariri na janyo raunuka a kwakwalwa iri daya da wanda akan samu a wasan dambe.

Elaine Hanzak ta ce iyaye mata na jin ba dadi da kunya wajen bayyana cewar suna bukatar a taimaka masu

Elaine Hanzak ta tuna yadda a ranar ta dimauce, cikin kankanin lokaci ta sauya daga kasancewa cikin farin ciki zuwa son ta yi wa jaririnta rauni.

“Lallai na ji a jikina cewa zan iya gwara kansa da bango, in jijjiga shi, in jefo shi daga saman bene. Kawai ji na yi ya lalata min rayuwa,” a cewarta. .

A daidai wannan lokaci, an gano cewar Elaine tana fama da cutar tsananin damuwa bayan haihuwa kuma duk da cewa tana shan magunguna, amma ba ta jin dadin jikinta kuma tana nuna babu matsala.

Ta bayyana cewar a lokaci guda sai tunanin mai kyau ya shigo mata sai ta ajiye jaririn a kan gadonsa bayyannan  ta nemi taimako.

Mai fafutukar Dakta Smith ya  bayyana cewar: “A Amurka da  kuma Canada suna da shirye-shirye dake rage yawan samun rauni a kai, amma mu a nan babu abin da muke yi kuma akwai bukatar samun canji.

“Sakonmu daya ne. Sai a ce kukan jariri ba wani abu bane, za su daina kuma ba wani abu bane don ka ajiye jaririn na dan lokaci muddin jaririn na wuri wanda yake da tsaro.”

Exit mobile version