Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Mahmood Yakubu ya bayyana cewa sun yi matukar daukar darasi a zaben 2023, sannan za su kara kwazo a zaben gwamnoni da zai gudanar a jihohin Kogi, Imo da kuma Bayelsa.
Ya kara da cewa hukumar ta gamsu da irin martanin da ta samu a yayin bitar bayan zaben 2023 da hukumar ta shirya.
- NSCDC Ta Lalata Haramtattun Matatun Mai 10, Ta Kafa ‘Yan Sintiri
- Yadda Amurka Ke Kwaton Albarkatun Kasa Da Kasa Da Sunan Yaki Da Ta’addanci
Shugaban INEC ya bayyana hakan ne a jim kadan bayan kammala bitar zaben 2023 na kwanaki uku da ya gudana a Jihar Legas, inda ya tabbatar da cewa za a magance matsalolin da suka faru a lokacin zaben da tare da yin amfani da shawarwarin da hukumar ta samu domin inganta zaben kasar nan, wanda hukumar za ta fara yin gwaji a zabukan gwamnoni da za su gudana a jihohin Kogi, Imo da kuma Bayelsa.
“Mun yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin cewa za mu gudanar da bitar zaben 2023 a cikin wata daya. Mun fara ne tun daga ranar 4 ga watan Yulin har zuwa 4 ga watan Agusta, mun samu korafe-korafe mai matukar yawan gaske. Mun fara gudanar da taron tattaunawa na shawarwari da kwamishinoninmu da ke jihohi, sannan muka zarce har zuwa wurin kungiyoyin sufuri, kafin muka shigo da jam’iyyu da sauran kungiyoyin fararen huda da dai sauransu. Gaba daya dai, muna samun kwarin gwiwa ta hanyar martanin masu ruwa da tsaki a fadin hukumar da irin gudunmawar da suka bayarwa.
“Mun samu matsaloli masu yawa tu daga wurin tantance masu kada kuri’a har zuwa saka sakamakon zabe a na’ura, sai dai mun samu shawarwari a kan haka.
“Akwai batun kalubalen kai kayayyakin zabe da yadda za a fara zabuka a kan lokaci da da samar da katin zabe da kuma amsa katin da sauransu. Muna samu korafe-korafe masu yawa kuma mun samu shawarwari a kan lamarin, inda wadanda hukumar za ta iya magancesu a ofis, za ta yi hakan, wadanda kuma ke bukatar gyara ga dokokin zabe ne ko kundin tsarin mulki za mu kai su zauren majalisar kasa domin duba lamarin. Don haka mun yi farin ciki da martanin da muka samu da kuma tattaunawa da muka yi a hukumar. Abu mafi muhimmanci ga hukumar shi ne, mun ji ta bakin ‘yan Nijeriya kuma hakan zai ba mu damar komawa kan turbar hukumar domin ci gaba da inganta zaben kasar nan.
“Bayan mun samu wadannan korafe-korafe, hakan zai ba mu damar yin gyare-gyare a zabukan gwamnoni da za su gudana a jihohin Bayelsa, Imo da kuma Kogi a watan Nuwamba, domin za mu kaddamar da wasu daga cikin shawarwarin da muka samu wadanda suka kunshi hukumar, amma wadanda suka kunshi majalisa, majalisar kasa za ta yi aiki ne bisa tanadin dokokin kasar nan.
“Haka kuma akwai wata damar da muka da ita, saboda a halin yanzu kwai zaben cike gurbi har guda hudu da suka hada da mazaba Surulere 1 a Jihar Legas da mazabar Jalingo da ke Jihar Taraba da mazabar Chibok da ke Jihar Borno State da kuma mazabar Chikun da ke Jihar Kaduna. Za mu ci gaba da kaddamar da wasu shawarwarin a zabukan cike gurbi da ke tafe.”