Shugabannin kungiyar masu sayar da takin zamani a kasuwar P/Z da ke Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna sun bayyana cewa sun dauki matakan fito-na-fito ga duk wanda aka samu yana sayar da gurbataccen takin zamani da ke cutar da manoma.
Shugaban kungiyar Alhaji Sani Ibrahim da aka fi sani da Alhaji Sani Danmarke ya shaida wa wakilinmu haka jim kadan bayan sun kammala taron wannan kungiya ta masu sayar da takin zamani a wannan kasuwa ta P/Z.
Alhaji Sani Danmarke ya ci gaba da cewar shugabancin wannan kungiya ba zai yi sak -sako ba ga duk wanda aka samu yana da masaniya ko kuma an hada baki da shi aka shiga da gurbataccen takin zamani cikin wannan kasuwa zai gamu da fushin kungiyar duk matsayin da yake da shi.
A cewar Alhaji Danmarke, duk wadanda ke da hali na shiga da kuma sayar da gurbataccen takin zamani a cikin wannan kasuwa da su ji tsoron Allah, domin yin haka ne kawai dukiyar da aka mallaka zai zama mai alhaira ba ga cuta ba.
A karshe, Alhaji Danmarke ya yi kira ga duk wani mai sayar da takin zamani a kasuwar P/Z da yan makomar rayuwarsa ta gobe, domin tunanin tara dukiya ta hanyar cutar da al’umma ba da za ta iya zama babbar matsala a rayuwa.