Yusuf Shuaibu" />

Mun Gano Kudaden NHIS Naira Biliyan Biyar Da Suka Bace – Sambo

Kudaden NHIS

Sakataren hukumar inshoran lafiya ta kasa, Farfesa Nasir Sambo, ya bayyana cewa, hukumarsa ta gano kudaden da suka bace na naira biliyan biyar da suka wabe. Haka kuma ya bayyana cewa, hukumar NHIS ta samu damar dawo da wasu kudade da suka bace. Sambo ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabi wajen taro matsalolin tattalin arziki a bangarorin lafiya da kulawa da wasu dubaru karo na 16, wanda ya gudana a Jihar Legas ranar Talata.

Ya ce, “Sauran abubuwan da muka yi dai sun hada da samun damar farfado da hanyoyin kudade a kan inshoran lafiya a hukumar NHIS.

“Lokacin da na zama sakataren shirin insharan lafiya, biliyoyin kudade sun bace ba tare da wani dalili ba.

“Mun samu nasarar fitowa daga wannan matsala ta hanyar bin ofishin akawun gwamnatin tarayya da hukumar yaki da cin hanci da rashawa wanda muka hada hannu da karfe, inda muka sami nasarar dawo da kudade har na naira biliyan biyar wanda suka bace a hukumar NHIS.

“Muna tsammanin samun daftarin biliyoyin kudade a kasafin kudin shekara da kuma shekara mai zuwa

“A lokacin da muka sami wadannan kudade, ina mai tabbacin za a samu gagarumin canji a hukumar NHIS,” in ji shi.

Ya ci gaba da bayyana cewa, kididdiga ya  nuna cewa sama da mutane miliyan 82.9 ke fama da matsanancin talauci, kamar  yadda hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana a shekarar 2019.

Haka kuma, Bankin Duniya ya kimanta cewa, ‘yan Nijeriya miliyan 92.6 za su kasance cikin mummunan talaauci a shekarar 2022.

Ya ce, “talauci yana karuwa ne idan ya kasance an samu karancin samun lafiya ga talakawa.

“Hukumar kula da cutattuka ta kasa ta bayyana cewa, ana samun karuwar cutattuka a Nijeriya wadanda suka hada da zazzabin cizon sauro da kuma  cutar Korona wanda ake fama da ita a halin yanzu.”

Ya kara da cewa, duk da wadannan abubuwan, Nijeriya tana iya bakin kokarin wajen bunkasa harkokin lafiya a karkashin shirin nan na cimma muradu na shekarar 2030. Ya ce, gwamnatin Nijeriya tana daukan matakan da suka dace wajen farfado da harkokin lafiya a cikin kasar nan musamman ma a yankunan karkara wanda ake samar da magunguna da cibiyoyin  lafiya da samar da kayayyakin lafiya na zamani.

Exit mobile version