Ministan kwadago da samar da ayyuka, Dakta Chris Ngige, ya ce ma’aikatarsa ta warware rikicin ma’aikata kusan 4,000 cikin shekaru takwas.
Ya bayyana hakan ne ga manema labarai na fadar shugaban kasa a lokacin da ya bayyana a taron tattaunawa na mako-mako da kungiyar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya a fadar shugaban kasa.
Ministan wanda ya kare yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da rikice-rikicen ma’aikata, ya ce, “Muna da himma. Mun sasanta rikicin aiki kusan 4,000. Muna samun sanarwar takaddamar ciniki (TDN) kuma muna kiran su don yin taro musamman a masana’antar mai da iskar gas.
“Ofisoshinmu na jihohin suna yin sulhu akai-akai”, in ji shi.
Ngige ya kuma bayyana cewa a sakamakon koma- bayan tattalin arzikin kasa ya fuskanta, rashin aikin yi a Nijeriya ya rubanya sama da hudu tun daga shekarar 2015.
Sai dai kuma ya jaddada bukatar yin kokari domin dakile illolin da ke tattare da tattalin arziki da yawan al’ummar kasar.
“Batutuwa guda uku na rashin aikin yi, talauci da tabarbarewar tattalin arziki sun kasance wani abin damuwa a rayuwar Nijeriya. Adadin rashin aikin yi a kasar ya ninka fiye da sau hudu tun bayan da tattalin arzikin kasar ya fada cikin koma-bayan, na farko a shekarar 2015, sannan kuma a shekarar 2020.
“Yawan rashin aikin yi a Nijeriya ya karu zuwa kashi 9.9 a shekarar 2015 a lokacin da gwamnati mai ci ta zo.
“A cikin ma’anar ILO na rashin aikin yi, akwai bukatar a yi kokari tare dakile illar rashin aikin yi ga tattalin arziki da kuma yawan al’ummar kasar nan.
“A bisa abubuwan da aka ambata kwanan nan ne ya sa gwamnatin tarayya ta kaddamar da wata kungiya mai suna ‘Technical Working Group’ (TWG) a kan samar da ayyukan yi da bunkasa sana’o’in matasa domin tunkarar matsalar rashin aikin yi da bunkasar matasa a kasar nan,” in ji shi.
Dangane da kokarin magance rashin aikin yi, Ngige ya ce kamata ya yi gwamnatin APC mai jiran gado ta yi la’akari da tsarin ofishin samar da ayyukan yi da ke karkashin ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi.
Ya ce ma’aikatarsa na da cibiyoyin bunkasa fasaha guda 125 a shiyyoyin guda shida na kasar nan, baya ga cibiyoyi 19 na ayyukan yi da ke Bauchi, Kaduna, Legas, Abuja, Edo, da Inugu, da dai sauransu, inda mutane suka samu horo kan aikin samar da bulo.
Ngige ya kuma bayyana cewa ma’aikatarsa na hada kai da ma’aikatar kwadago ta Amurka domin dakile bautar da yara, inda ya kara da cewa sun samar da dala miliyan 75 domin yaki da talauci a yankunan da ake noman koko da ma’adanai a Nijeriya.
Ngige ya ce ana maganar karin albashin ma’aikatan Nijeriya, kuma abin da ke faruwa a yanzu shi ne adadin kudaden da ake samu ya yi karanci ballantana a karin albashi.
Ya kuma ce adadin kudin da za a biya zai dogara ne a kan yadda ake samun kudade da kuma yadda za a iya biya.