Abba Ibrahim Wada" />

Muna Ci Gaba Ta Tattaunawa A Kan Makomar Ozil – Arteta

Arteta

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya tabbatar da cewa shugabannin kungiyar suna ci gaba da Magana akan makomar dan wasa Mesut Ozil wanda yake shirin barin Arsenal a wannan watan na Janairu.

Arteta ya bayyana haka ne bayan tashi daga wasa da Arsenal ta buga 0-0 da kungyar kwallon kafa ta Crystal Palace a wani kwantan wasa da suka fafata a ranar Alhamis sai dai bai fayyace kungiyar da dan wasan zai koma ba.

Rabon Ozil da buga wa Arsenal wasa tun a cikin watan Maris na shekarar 2019 duk da cewa ya sha nanata cewa yana jin lafiya kamar ingarman doki, kuma a shirye yake ya yi wasa amma Arteta baya amfani dashi.

Tsohon dan wasan na Real Madrid ya fito sosai a dandalin sada zumunta tun lokacin da aka daina ganinsa a filin kwallo, inda har a rana Litinin da ta gabata ya dinga amsa tambayoyin masu bibiyansa a Twitter.

Ya amsa tambayoyi da dama da suka hada da wadda akayi masa mai cewa ko yana da na sanin zuwa Arsenal sai dai dan wasan ya bayyana cewa bai taba danasanin komawa kungiyar ta Arsenal ba a rayuwarsa.

Sai dai yayin da har yanzu ake dakon fayyace makomarsa a Arsenal, Mesut Ozil ya ce baya nadamar kulla yarjejeniya da kungiyar da kawo yanzu ya shafe akalla shekaru 7 tare da ita duk da a yanzu baya buga wasa

A shekarar 2013 Ozil ya sauya sheka daga Real Madrid zuwa Arsenal kan kudi fam miliyan 42 da rabi, inda kuma a tsawon lokacin da suke tare ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofunan FA guda uku, da na Community Shield guda daya, haka zalika ya lashe kyautar dan wasa mafi kwazo a kakar wasa ta 2015 zuwa 2016.

Exit mobile version