Wasu masu ruwa da tsakani a fannin noman Shinkafa don riba sun bayyana cewa, biyo bayan hasashen da hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi kwanan baya kan samun ambaliyar ruwan sama a wasu sassaa kasar nan, sun bayya cewa, a yanzu haka suna a cikin fargaba.
Manoman musamman wadada suka fito daga jihohin Taraba, Jigawa, Kano, Benue, Niger, Kogi, da Kebbi da sauran wasu jihohin, sun bayyana hajan ne a wata hura daaka yi da su da ban da ban.
- ‘Muhallin Mutum 43,000 Aka Cunkusa Alhazan Nijeriya 95,000 A Mina’
- Bukatar Dakatar Da Kara Kudin Wutar Lantarki A Nijeriya
Sun wara da cewa, a yanzu haka suna cike da tsaro samakamakon hasashen hukumar ta kuka da yanyi da ta I a kwanan baya, inda suka sanar da cewa, annobar da ta auka wa gonan su a kakar noma ta bara, ba su ji da dadi ba domin sun tabka asara mai dimbin yawan gaske.
Ambaliyar ruwan da ta auku a bara, rahotannin sun ce, ta kutsa a cikin gonakan sun a noman Shinkafar, inda hakan ya janyo masu tabka mummunar asara.
Rahotannin sun ce, iftila’in ya aukwa gonakan su na ne Shinkafar, a yayin da take kan girma.
Akasari dai, a wasu jihohin an fi samun yawan ruwan sama mai yawa daga watan Satumba.
Shinkafa dai ta kasance akasarin cimmar alumma Nijeriya, inda gwamnatin tarayya mai ci ke kokarin baiwa fannin kulawar da ta dace, tun a 2016.
Sai dai, abin takaici, Nijeriya a duk shekara na fuskanyar kalubalen ambaliyar ruwan sama, inda hakan musamman ke shafar gonakan manoman Shinkafa da kuma sauran amsu ruwa da tsaki a kasar.
Hakan ya janyo wasu manomanta sun yi asara mai yawa, inda wasu rahotanni daga jihar Taraba sun ce, dubban manoman Shinkafa a kananan hukumomi biyar, sun tabka asara saboda ambaliyar da ta ta so daga kogin da ke a jihar Biniwe.
An ruwaito cewa, kusan kashi 90 na gonakan Shinkafar, ambaliyar ta lalata, inda ake tunin, hakan zai janyo karancin samun Shonkfar da ake noma wa a wannan shekarar
Dubban kadadar da abin ya shinkfar sun kasance ne a Karim-Lamido, Lau, Ardo-Kola, Gassol da Ibbi.
A cewar wata namomiyar Shinkafar a yankin Mutumbiyu da ke a karamar hukumar Gassol Madam Rita John, ta ce, ta ciyo basgin naira 400,000 daga gun wanu dilolin Shinkafarm bisa burin za ta samu riba idan ta firbe ta, amma kuma ambailyar, ta lalata mata barna a gonarta.
Shi ma wani manominta Abubakar Dauda, ya sanar da cewa, ya ciwo bashin naira 350,000 ne daga gun wani dilan Shinkfar domin yin noman, amma ambaliyar ta lalata masa gonar sa.
Bugu da kari, manyan manoma sune abin ya fi shafa, ganin cewa, sun zuba miliyoyin naira domin yin nomanta
Shi ma wani dan majalisar dokokon jihar Taraba Suleiman Abbas, ya sanar da cewa, ya zuba dimbin kudade a nomanta, amma ambailyar ta lalata masa gonarsa, inda ya sanar da cewa, akwau bukatar gwamnati ta kawo masu dauki.
Haka shi ma Yakuku Adamu, wanda babban manominta ne ya bayyana cewa, a baya ya na girbe sama da buhunhuna 3,000 na Shinkafar cikin gida, amma ambailyar ta lalata masa gonarsa.