Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa su na nazarin dokoki guda 69 da kuma buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙudirin ƙirƙirar ƙananan hukumomi 278 bisa ga tsarin kundin mulkin 1999.
Barau, wanda shi ne shugaban Kwamitin Bita na Tsarin Mulki a majalisar dattawa, ya bayyana hakan ne a taron haɗin gwuiwa da kwamitocin majalisar dattawa da kwamitocin majalisar wakilai kan gyare-gyaren dokokin tsarin mulki da suka gudanar a Lagos.
- Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu
- Firimiyar Nijeriya: Barau FC Ta Samu Nasarar Farko A Tarihinta
Ya jaddada cewa an dauki lokaci mai tsawo wajen tattaunawa da al’umma da masu ruwa-da-tsaki da ƙungiyoyi daban-daban, domin kawo waɗannan ƙuduri a gaban majalisar.
Ya kuma bayyana burin majalisar cewa za ta miƙa kashi na farko na gyare-gyaren tsarin mulki ga majalisun jihohi kafin ƙarshen shekarar.














